An kaddamar da jigilar shanu ta jirgin kasa a Najeriya

Image caption Kimanin shanu 500 ne ne cikin taragai 23 suka tashi daga Gusau zuwa Legas bayan kaddamarwar

A Najeriya, an kaddamar da wani shiri na jigilar shanu ta jirgin kasa daga yankin arewaci zuwa kudancin kasar.

An gudanar da bukin kaddamarwar ne a birnin Gusau na Jihar Zamfara da ke arewa-maso yammacin kasar.

Kimanin shanu 500 ne cikin taragai 23 suka bar garin Gusau zuwa birnin kasuwanci na Legas bayan kaddamarwar.

Wannan wani bangaren ne na shirin da babban bankin kasar ya bullo da shi mai suna NIRSAL.

Manufar shirin shi ne kara yawan kudaden da ake sarrafawa wajen aikin gona da kuma ragewa manoma yawan asarar da suke tafkawa wajen sayar da amfanin gonar su.

Gwamnatin Najeriyar dai ta kiyasta cewa cinikin shanu da sauran dabobbi da ake yi tsakanin arewaci da kudancin kasar ya kai Naira biliyan 850 zuwa 950 a duk shekara.

Labarai masu alaka