Rana ta yi husufi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto SAATCHI AND SAATCHI
Image caption Sai mutum ya sanya bakin gilashi zai iya ganin ranar

Wasu jihohi a Najeriya sun fuskanci haɗuwar rana da wata da misalin karfe bakwai na safiyar Alhamis.

Daman dai Hukuma mai hasashen yanayi ta kasar wato NIMET, ta sanar da cewa Rana da Wata za su yi taho-mu-gama a wasu sassan kasar.

Wasu mutane da dama sun shaida wa BBC cewa sun shaida yadda zazzabin na rana ya kasance a garuruwansu.

Umar Farouk, jihar Kano ne kuma ya yiwa wakilinmu, Usman Minjibir karin bayani.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka