Tim Cook: Kamfanin Apple bai yi laifi ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tim Cook ya musanta cewa Apple ya yi laifi

Shugaban kamfanin Apple, Tim Cook ya ce hukuncin da Tarayyar Turai ta yanke na cewa kamfanin Apple ya biya biliyoyin euro a matsayin kudin haraji ga jamhuriyyar Ireland "abin takaici ne" kuma abin ya zo da "ba zata ba"

A lokacin da ya ke jawabi a gidan rediyon Jamhuriyyar Ireland, ya ce bai yarda cewa Apple yayi wani laifi ba.

Hukuncin da Tarayyar Turai ta yanke ya ce an bai wa Apple din kudin haraji ba bisa ka'ida ba na Euro 13bn.

Mista Cook ya ce yana da "kwarin gwiwa sosai" cewar za a sauya hukunci idan ya bukaci hakan.

Labarai masu alaka