Shugaban kasar Uzbekistan Islam Karimov ya rasu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Islam Karimov ya yi mulkin Uzbekistan ne fiye da shekaru 25

Shugaban kasar Uzbekistan, Islam Karimov ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Marigayi Islam Karimov ya yi mulkin Uzbekistan ne fiye da shekaru 25 kuma a halin yanzu ba a san wanda zai gaje kujerar tasa ba.

Tun da farko Firai Ministan Turkiyya, ya sanar da rasuwar Islam Karimov a lokacin wani taron majalisar zartarwa na kasar wanda aka nuno a talabijan.

Ya ce, "Shugaban Uzbekistan ya rasu. Allah kuma ya masa rahama. Mu 'yan Turkiyya muna taya al'ummar Uzbekistan jimamin wannan rashi."

An dai yi ta rade-radi game da batun, inda aka ce za a rufe filin saukar jirgin saman da ke birnin Samarkand ranar Asabar, garin da shi ne mahaifar Shugaba Karimov, kazalika wasu rahotannin sun ce an soma tsara mutanen da za su yi jana'izarsa.