'Yan adawar Venezuela sun yi zanga-zanga a Caracas

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shuagaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, ya ce gwamnatinsa ta dakatar da wani yunkurin 'yan adawar kasar na haddasa tashin hankali da kuma yin barna.

Gwamantin ta yi kokarin hana zanga-zangar da dubban jama'a daga bangaren adawa suka gudanar a Caracas babban birnin kasa.

Shugabannin bangaren adawar kasar ta Venezuela, sun furta cewa, sun tara mutanen da yawansu ya kai sama da milyan daya a babban birnin kasar domin gudanar gangami mafi girma cikin shekaru biyu.

'Yan adawar dai na kira ne a gudanar da kuri'a raba gardama game da matsayin shugaban kasar wanda 'yan adawar ke aza wa laifin tsunduna tattalin arzikin kasar a cikin wani mawuyacin hali.

To sai dai daga na shi bangaren shugaban kasar ta Venezuela Nicolas Maduro cewa ya yi zanga-zangar da 'yan adawar suka tsara ta kasance daga cikin wasu dubarun su na yin juyin mulki.

A kasar Venezuela an shafe dogon lokaci ana ta fito na fito tsakanin gwamnatin kasar da kuma 'yan bangaren adawa.