Maudu'in da ya fi shahara a Twittter

Maudu'in #30DaysofGratitude, wanda ke nufin #kwanakin30naGodiya ga Allah ne ya fi shahara a Twittter.

A kowace rana, a kwanakin talatin da za a shafe ana bibiyar maudu'in, akwai maudu'i na musamman da aka ware domin jin ra'ayoyin mutane.

Ranar Juma'a ce 2 ga watan Satumba kuma ta kasance ranar #technology wanda ke nufin # RanarFasaha inda muntane zasu bayyana ra'ayoyinsu, a shafikansu na Twitter a kan fasahar zamani da suke alfahari da ita.

A ranar Alhamis ne kuma aka duba maudu'in #smell wanda ke nufin #kamshi, inda mutane da dama su ka bayyana ra'ayoyinsu a kan kamshin da suke alfahari da shi.

Labarai masu alaka