Mahaukaciyar guguwa ta afka wa jihar Florida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guguwar ta tumbuke turakun wuta

Mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa da aka yi wa lakabi 'hermine', ta sauka a arewacin jihar Florida da ke Amurka, irinta ta farko a jihar a tsawon shekara 11.

Guguwar dai ta sauka a gabar ruwan jihar ta Florida da safiyar Juma'a.

Gwamnan jihar, Rick Scott ya ayyana dokar-ta-baci ga garuruwa 51 domin zama cikin ko-ta-kwana dangane da guguwar.

Jami'ai a babban birnin jihar, Tallahassee wanda ta nan ne guguwar ta wuce, sun ce akalla gidaje 70,000 ba su da wutar lantarki.