An bai wa Jackie Chan Lambar Yabo

Hakkin mallakar hoto

Cibiyar Nazarin Fina-finai ta Academy of Motion Pictures and Sciences dake da hedikwata a kasar Amurka, ta bayyana cewa zata bai wa Jakie Chan Lambar yabo.

Za a bai wa hahararren dan wasan fim din na kasar China, lambar yabo ta Oscar, saboda abin da ta kira gagaruman nasarorinsa a fagen fina-finai.

Za a ba shi lambar ce tare da wasu masu harkar fina-finan da suka yi fice a duniya.

Jackie Chan ya yi suna har ma a kasashen Afirka irinsu Nijeriya.