'Za mu mayar wa Najeriya kuɗaɗen sata'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin 'yan siyasar Najeria da suka gabata da sace kudaden kasar zuwa kasashen waje.

Gwamnatin Birtaniya ta amince za ta mayar wa Najeriya kudi kimanin Fam miliyan 700 daga cikin kudaden da aka sace aka boye a kasar.

A makon nan ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu a kan wata yarjeniyar tsare-tsaren yadda za a maida kudin a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ministan shari'a Abubakar Malami ne ya wakilci gwamnatin Najeriya, yayin da Ministan kula da shige-da-ficen Burtaniya, kuma dan majalisar dokoki, Robert Goodwill ya saka hannun a madadin Kasarsa.

Ministan shari'ar na Najeriya Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa wannan adadin kudin shi ne kashi na farko da Birtaniya ta amince za ta mayar wa Najeriya.

Ya ce ana ci gaba da bincike kan gidaje da kadarori da wasu kudaden da ake zargin an karkatar da su zuwa Birtaniya daga Nijeriya ba bisa ka'ida ba.

Abubakar Malami ya ce a makon gobe ne za a mika wa Birtaniya bayanai kan asusun da ake zargi an ajiye kudaden, inda daga nan kuma za a fara shirye-shiryen mayar wa Najeriyar kudaden.

Labarai masu alaka