Bam ya tashi a kotu a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pakistan dai na fama da hare-haren kungiyoyi masu tsattsauran addini

Wani dan kunar-bakin-wake ya kai harin bam a wata kotu a arewacin birnin Mardan da ke Pakistan, a inda akalla mutane 11 suka mutu sannan kimanin 30 suka jikkata.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa, maharin dai sai da ya fara jefa gurneti a cikin kotun, kafin daga bisani ya kutsa kai ciki sannan ya tayar da bam.

Har wa yau dai, a ranar Juma'ar wasu maharan guda hudu sun kai hari a wata coci da ke makwabtaka da birnin Peshawar, kafin a harbe su.

Duka hare-haren dai sun faru ne a lardin Khyber Pakhtunkhwa kuma kungiyar Jamaat-ul-Ahrar ce wadda ta bangare daga kungiyar Taliban, ta dauki alhakin hare-haren.

A baya dai mayaka masu tsaurin addini sun kaddamar da hare-hare a kan lauyoyi da suka hada da harin bam din ya yi sanadiyyar mutuwar lauyoyi 18.

Shi ma wannan din Jamaat-ul-Ahrar ce ta dauki alhakin kai wa.

Labarai masu alaka