Cutar Zika ka iya ɓulla Nigeria — Rahoto

Image caption Cutar Zika na sanya kan yara ya kankance

Wani binciken masana kimiyya ya nuna cewa fiye da mutane biliyan biyu na fuskantar hadarin kamuwa da cutar Zika, a wasu sassan Afrika da Asiya.

Nazarin dai wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ya ce, akwai miliyoyin jama'a dake zaune a wuraren da saboda yanayinsu yana da wahalar gaske a kauce, ko a gano alamun cutar ta Zika.

Wadanda suka yi nazarin sun ce, jama'a a kasashe kamar India, da Pakistan da Nigeria, su ne suka fi kasancewa cikin hadarin yiwuwar kamuwa da cutar.

Cutar Zika dai wadda Sauro ke yadawa, tana yin lahani ne ga kwakwalwar jariri tun yana ciki, a inda take tsumburar da ita.

Sannan kuma bayan an haifi jaririn zai kasance mai karamin kai.

Fiye da kasashe 65 ne a duniya suke fama da kwayar cutar ta Zika kuma a baya-bayan nan ne Zikar ta shiga nahiyar Afirka.

Ga dai yadda cutar ta fara a fadin duniya
  • A 1947 ne masu bincike kan zazzabin shawara a dajin Zika da ke kasar Uganda, suka fara gano kwayar cutar ta Zika a jikin biri.
  • 1952 ne aka fara samun cutar a jikin dan adam a Uganda da Tanzania.
  • 1954 an samu kwayar cutar a Najeriya.
  • 1960 aka samu cutar a kasashen Asiya kamar India da Indonesia da Malaysia da Pakistan.
  • 2007 kwayar cutar Zika ta fara bazuwa zuwa sauran sassan duniya daga Afirka.
  • 2015 Brazil ta fitar da rahoton bullar cutar a kasar, bayan yawaitar haihuwar jarirai masu kananan kai.

Sai dai kuma masana sun ce har yanzu ba a iya gano ko wane irin sauro ne yake dauke da kwayar cutar ba.

Labarai masu alaka