Mali: matsalar tsaro ta ci rawanin minista

Hakkin mallakar hoto AP

Fargabar tabarbarewar tsaro a Mali ta ci rawanin Ministan tsaron kasar, Tieman Hubert Coulibaly.

An dai tube wa Ministan mukaminsa ne kwana guda, bayan wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai garin Boni, inda suka kwace iko da garin na wani lokaci.

Sojojin Malin dai sun ce sun sake kwace garin daga hannun 'yan bindigar, da taimakon rundunar majalisar dinkin duniya.

A ranar Juama'ar data gabata ne sojojin suka fice daga garin Boni, bayan harin da 'yan bindigar suka kai, inda suka bude-wuta a kan wasu gine-gine, tare da banka wa wasu daga ciki wuta.

Wata ruwayar ta ce 'yan bindigar sun sace wani jami'in gwamnati lokacin da za su fice daga garin.

Labarai masu alaka