A hukunta sojojin Sudan ta kudu-Power

Hakkin mallakar hoto EPA

Jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Samantha Power ta bukaci gwamnatin Sudan ta kudu da ta hukunta maharan da suka lakada wa wasu 'yan kasashen waje duka, kana suka yi musu fyade a wani Otel, har ma suka kashe wani dan jarida dan Sudan ta kudun a watan Yulin da ya wuce.

Ta ce matukar jami'an tsaro za su aikata fyade, su kwashi ganima, su yi kisan-gilla ba tare da an hukunta su ba, to zai yi wuya a wanzar da zaman lafiya a wannan wuri.

Samantha Power ta yi wannan furucin ne lokacin wata ziyarar da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar ya kai Sudan ta kudu, inda kwamitin ya bukaci gwamnatin kasar da ta daina adawar da take yi da yunkurin majalisar dinkin duniya na karfafa rundunarta a Sudan ta kudun, sakamakon fadan da ya kaure tsakanin sojojin gwamnati da magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ana dai zargin sojojin gwamnatin Sudan ta kudu da aikata galibin aika-aikar da aka yi a Juba, babban birnin kasar.

Labarai masu alaka