Uzbekistan: An fara makokin kwana uku

Hakkin mallakar hoto AP

Dubun-dubatar jama'a sun cika tituna a Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan domin jana'izar shugaban kasar marigayi Islam Karimov, wanda ya shafe sama da shekara 25 yana mulkin kasar.

Mutane sun yi ta jefa furanni, lokacin da ayarin motocin da ke dauke da gawar mamacin ya wuce zuwa filin saukar jiragen saman birnin.

Marigayin dai ya rasu ne yana da shekara 78 a duniya, kuma ya shafe sama da shekara 25 yana mulkin kasar.

Ya yi jinya ta kwana shida a asibiti a kasar.

A yau Asabar ne za a yi jana'izarsa, kuma Firayim Ministan kasar, Shavkat Mirziyoyev ne zai jagoranci jana'izar, wadda za a yi Samarkanda, inda aka goya marigayin, a wani gidan marayu.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai suna sukar gwamnatin marigayi Karimov da cewa tana daga cikin gwamnatoci mafi zalunci da kama-karya da aka taba yi a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce cin zarafi da take hakkil bil adama a lokacin mulkin Shugaba Islam ya zama ruwan dare.

Anna Neistat, jami'a a kungiyar Human Rights Watch, ta ce Karimov ya shafe shekara da shekaru yana murkushe 'yan adawa, yana kama mutanen da ya ga za su kalubalanci gwamnatinsa, yana garkame su a gidan-yari.

To sai dai shugaban Rasha Vladimir Putin jininawa Mr. Karimov yayi, yana cewa cikakken mai kishin kasa ne, da ya bada gudunmuwa wajen daidaita al'amura a nahiyar Asiya.

Shima tsohon shugaban ya taba bayyana cewa yana daukar tsattsauran matakai ne ta yadda zai yi maganin masu zafin kishin addini a kasar, wacce mafi yawan jama'arta musulmai ne.

Kasar dai na makotaka da Afghanistan.

Ana sa ran shugabannin duniya da dama za su halarci birnin Samarkanda domin zana'izar ta sa.

Labarai masu alaka