An bude taron kasashen G-20 a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firayiministar Burtaniya Theresa May da shugaba Xi Jingping na China

Shugaban China, Xi Jingping ya bude taron shekara na kasashen G-20, tare da yin gargadin cewa tattalin arzikin duniya yana wani mawuyacin yanayi.

Da yake magana a birnin Hangzhou, Mista Xi ya shaidawa taron shugabannin kashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya cewa, duniya yanzu na fama da rashin tabbas na kasuwanni, da raunin zuba jari, da rashin babbar alama ta samun sabon ci gaban fasaha.

Mista Xi ya kuma yi wata tattaunawar da wasu shugabanni da suka hada da Obama na Amurka, inda suka tattauna batun mamayen da China ke yi a Tekun Kudancin China.

A wata tattaunawar ta daban, shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce ta hanyar siyasa ne kadai za a iya magance rikicin Syria.

Labarai masu alaka