INDIA: An cafke tsohon minista kan zargin fyade

An cafke tsohon ministan ma'aikatar mata da kananan yara a Delhi babban birnin kasar India, bayan da aka zarge shi da aikata fyade.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan da aka sauke ministan Sandeep Kumar daga mukaminsa , bayan bullar wani faifen bidiyon da ya nuna shi yana yin lalata da wata mata.

Matar wacce aka nuna a faifen bidiyon ta ce lamarin ya faru ne shekarar da ta gabata, kuma an dauki bidiyon ne ba da saninta ba.

Tana kuma zarginsa da yi mata fyade .

Mr Kumar ya ce an hada faifen bidiyon ne, don haka ya musanta aikata ba daidai ba.

Yana cikin jam'iyar Aam Admi Party da ta lashi takobin kawo karshen cin hanci da rashawa a harkokin siyasar kasar.

Labarai masu alaka