'Za mu tabbatar an hukunta masu juyin mulki a Turkiyya'

Shugaban Obama ya ce Amurka za ta tabbatar da ganin an hukunta wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba a kasar Turkiyya.

Yana magana ne a yayin wata ganawa da shugaba Recep Tayyip Ergogan, a daidai lokacin da ake taron kungiyar kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a birnin Hangzhou.

Kasar Turkiyya na zargin limamin addinin musuluncin nan na kasar dake zaune a Amurka Fethullah da hannu a yunkurin juyin mulkin, ta kuma bukaci a taso keyarsa gida.

Amma kuma Mr Obama bai yi komai a kai ba wajen mika Mr Gullen din ga hukumomin Turkiyyar.

Mr Gulen dai ya sha musanta zargin da ake yi masa.

Labarai masu alaka