Za a yi taro kan tura sojoji Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption MDD za ta yi taro kan tura karin dakaru 4000 Sudan ta Kudu

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gana da jami'an kungiyar tarayyar Afirka yau Litinin a Addis Ababa, bayan amincewar shugaban Sudan ta Kudu da aniyar MDD ta karfafa dakarunta a kasar.

Da farko dai shugaba Salva Kiir ya yi turjiya, yana cewa wannan matakin hawan-kawara ne ga kasarsa, a matsayinta na mai cikakken 'yanci.

Kwamitin sulhu na MDD ya ba da umurnin tura karin dakaru 4000 Sudan ta kudun ne bayan barkewar rikici a Juba, babban birnin kasar, a tsakanin sojojin gwamnati da masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Sabuwar rundunar dai mai dakaru 4000 za ta samu karfin iko fiye da dakaru dubu 13 da yanzu haka ke kasar ta Sudan ta Kudu