China: Kowa ya kora ruwa a shadda zai biya

Wata makaranta a China tana kokarin hana dalibai yawan kora ruwa a duk lokacin da su ka yi amfani da shaddar zamani.

Makarantar ta samar da na'urar da ta ke bai wa dalibai damar yin amfani da ban-dakunan da ke makarantar.

An tanadar wa ko wanne dalibi a Makarantar Horar da Ma'aikatan Kiwon Lafiya ta Kunming da ke lardin Yunnan litar ruwa 3,000 a ko wanne wata a kan na'urar da ke bayar da dama a yi amfani da shaddar, a cewar jaridar Chuncheng.

Idan har suka kora ruwa fiye da yadda ya kamata bayan sun yi bayan-gida, kuma suka haura yawan ruwan da aka ba su damar yin amfani da shi, sai su biya karin kudi duk da dai ba a kayyade kudin ba.

Lardin Yunnan dai ya sha fama da fari a shekarun baya-bayan nan.

Labarai masu alaka