G20: Za a magance matsalar tattalir arziki

Hakkin mallakar hoto AFP

An shiga kwana na biyu na babban taron kungiyar kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki a kasar China.

Ana taron ne a garin Hangzhou, kuma shugaba Xi Jinping ne mai saukin baki.

Mista Xi ya ce an riga an samu ci-gaba wajen shirya wani kuduri don daukar mataki a kan tafiyar hawainiyar da bunkasar tattalin arziki ke yi, da kuma bukatar tabbatar da cewa kowa ya ci moriyar dunkulewar kasashen duniya.

Ana kuma tattauna wasu batutuwa da suka hada da matakan da za a dauka domin magance matsalar samar da kayayyakin sarrafawa irin us farin karfe fiye fiye da yadda ake bukata, da kuma hanyar da kasashen duniya za su bi domin shawo kan matsalar 'yan gudun hijira.

Labarai masu alaka