Syria: An kai hari kan yankunan gwamnati da Kurdawa

Akalla mutum 20 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu abubuwa a yankunan Kurdawa da wadanda ke karkashin ikon gwamnati.

Wani abu ya fashe a birnin Tartous da ke bakin ruwa da birnin Homs da ke tsakiyar gari da Damascus da kuma garin Hassakeh da ke arewa maso gabashin kasar, wanda ke karkashin ikon Kurdawa.

Mutane da dama sun rasa rayukansu a harin Tartous wanda sansani ne na sojin sama na Rasha da ke Syria.

A watan Mayu ne dai kungiyar IS ta kai hari na karshe a birnin.

Labarai masu alaka