Rikicin Syria: Mutane da dama sun hallaka

Akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu a fashewar bama bamai hudu a yakunan da ke karkashin ikon Gwamnati a Syria da kuma daya a wani birni da dakarun kurdawa suka mamaye.

An kai harin ne dai tsakanin karfe 08:00 da karfe 9:00 a kewayen Damascus da Homs d Tartous da kuma Hassakeh.

Ba a dai tabbatar ko hare-haren suna daa alaka ba.

Hari mafi muni ya faru ne a wajen garin Tartous da ke gabar tekun Bahar-rum.

Labarai masu alaka