Obama 'ɗan karuwa' ne — Duterte

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Duterte ya kashe daruruwan masu safarar miyagun kwayoyi

Shugaban Amurka Barack Obama ya soke ganawarsa da shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte, mai jawo ce-ce-ku-ce bayan Mr Rodrigo ya kira shi "dan karuwa".

Mista Duterte yana mayar da martani ne ga alwashin da Shugaba Obama ya sha na tayar da batun kisan gillar da ake yi wa masu safarar miyagun kwayoyi a ganawar da za su yi.

Shugaban na Philippine ya yi kaurin suna wajen sukar manyan mutane, kodayake a wannan karon batun na da matukar tasiri a fannin diflomasiyya.

Mista Duterte ya ce ya yi nadamar miyagun kalaman da ya gaya wa Mista Obama.

Labarai masu alaka