An hana fitar da jakai daga Nijar

Image caption Kasashen nahiyar Asiya na sayen jakai da yawa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta hana fitar da jakai kasashen waje, musamman kasashen Asia, da kuma yanka su domin cin namansu.

Hukumomin sun ce sun dauki wannan matakin ne domin kare jakai daga karewa a Nijar din, inda adadin jakai da ake fitarwa ke ci gaba da karuwa.

An samu kari daga jakai dubu 27 da aka fitar a shekarar 2015 zuwa dubu 80 a wannan shekara.

Galibin jakan da ake ci a kudu maso gabashin Najeriya suna fitowa ne daga Jamhuriyar Nijar.

Haka kuma kasar China ce ta fi sayen fatar jakai, inda take amfani da sinadarin gelatin wajen hada magunguna na kara karfin mazakuta da kuma man shafawa mai-da-tsohuwa-yarinya.

Miliyoyin 'yan Nijar ne dai ke amfani da jakai musamman domin yin sufuri.

Labarai masu alaka