'Ana zuzuta wahalar da ake fuskanta a Nigeria"

Shugaban kamfanin dillancin labarai na Nigeria NAN, Bayo Onanuga ya ce, bisa ga dukkan alamu akwai wasu da suke ƙara gishiri dangane da batun wahalar da ake cewa, 'yan Nigeria suna sha a lokacin mulkin Buhari.

Bayo Onanuga ya zargi wasu kafofin yada labaran Nigeria da yin farfaganda domin muzanta gwamnatin Muhammadu Buhari.

A shafinsa na Facebook Bayo Onanuga ya ce, bisa binciken da ya gudanar a Bauchi da Jos har yanzu kayan abinci suna araha, ba kamar yadda ake ta yaɗawa ba.

Bayo Onanuga wanda fitaccen ɗan jarida ne ya ce, wadanda suka sha kaye a zaben 2015 ne suke kara gishiri, suna zuguguta irin wahalar da ake fama da ita a lokacin mulkin Buhari.

"Ina Bauchi, sannan na je Jos a karshen mako, amma na yi bincike sai na ga abinci yana araha. A otel din da muka sauƙa mun sayi tuwon Semovita da kifi, ko kaza, a kan naira 700. Na yi mamaki da aka sayar min lemon zaki guda hamsin akan naira dubu daya."

Image caption Wasu suna korafin cewa, abinci yana tsada

Bayo Onanuga ya ce, duk da cewa, akwai tashin farashin kaya, amma shi ya yi imanin ana zuguguta lamarin da nufin bata sunan gwamnatin Buhari.

Ya kuma ce, wadanda suka sha kaye a zaben 2015 har yanzu ba su yarda sun sha kaye ba, dan haka suke ta farfaganda kamar dai har yanzu yaƙin neman zabe ake yi.

Bayo Onanuga wanda da shi ne babban editan mujallar The News ya zargi wasu kafofin yada labaru da bari ana amfani da su wajen kara gishiri a kan halin da Nigeria take ciki da nufin muzanta gwamnatin Buhari.

Wannan matsayi na Bayo Onanuga ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda wasu suka zarge shi da kaucewa gaskiya.

Amma ya ce shi, ko a jikinsa.

Labarai masu alaka