Satar mutane: 'Yan sanda sun cafke mutum 22 a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar 'yan sanda ta kuma an samu bidigogi hudu daga hannu mutanen tare da shanu da tumakai sama da 120.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gabatar da mutune 22 da ta kama bisa zargin su da satar mutane don neman kudin fansa a yankin kudancin Kano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Rabi'u Yusuf shi ne ya gabatar da mutanen a wani taron manema labarai a Kano.

Daga cikin wadanda aka kama har da wani da ake zargi cewa ya yi kaurin suna wajen satar mutane mai suna Nasiru Alhaji Na Bakin Daji daga karamar hukumar Sumaila.

Rundunar ta kuma gabatar da wani mutum da ta ke zargin sa da hada baki da wani dansa wajen yiwa makwabcinsa barazanar sace shi matukar ya gaza biyan su Naira miliyan biyu.

Rundunar ta kuma ce ta samu bidigogi hudu daga hannu mutanen tare da shanu da tumakai sama da 120.

A cewar rundunar, an samu nasarar cafke mutanen ne sakamakon daukar sabbin matakai a kananan hukumomin yankin wadanda ke fama da ayyukan 'yan fashin shanu da suka rikide zuwa satar mutane ciki har da tsofaffi da matan aure.

Labarai masu alaka