'Yan Iran ba Musulmai ba ne—Saudiyya

Image caption Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana Iraniyawa a matsayin wadanda ke da alaka da addinin Zorosta

Babban Muftin kasar Sa'udiyya, ya yi kakkausar suka a kan kasar Iran, yana cewa 'yan kasar ba Musulmi ba ne.

Babban Muftin, Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana Iraniyawan a matsayin wadanda ke da alaka da addinin Zorosta, wanda ke da karfi a kasar gabanin Musulunci.

Kalaman Muftin sun biyo bayan kakkausar da Ayatullahi Ali Khamenei ya yi wa Sa'udiyyar a kan yadda take gudanar da sha'anin aikin hajji.

Ayatullahi Khamenei din ya zargi hukumomin Sa'udiyya da kisan masu ibadar da turmutsutsin da aka yi a bara ya halaka.

Labarai masu alaka