Sabbin shawarwari a kan cutar Zika

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da sabbin shawarwari na kare kai ga wadanda suka ziyarci sassan duniya da ake fama da zutar Zika.

Sabbin shawarwarin sun ce, maza da mata da basu jima da dawowa daga yankunan da suke fama da cutar Zika ba su sanya kariya yayin jima'i, ko kuma su ƙauracewa jima'i na tsawon watanni shida koda kuwa babu alamun cutar tare da su.

Cutar Zika dai tana sawa a haifi jariri da lahani a kwakwalwa, kuma sauro ne yake yaɗa ta, amma kuma yanzu akwai hujjoji da suke nuna cewa, cutar tafi yaduwa ta hanyar jima'i.

Labarai masu alaka