India: Ana bincika abinci dan gano naman shanu

Hakkin mallakar hoto AFP

Jihar Haryana dake arewacin India ta baiwa 'yan sanda umarnin su je wani yanki da musulmi suka fi yawa domin su duba irin dafa-dukka mai suna Biryani domin su tabbatar da cewa babu naman shanu a ciki.

Shanu dai suna da tsarki ga mabiya addinin Hindu, kuma a jihar Haryana akwai doka mai tsauri da ta haram yanka shanu.

Shugaban hukumar dake sa ido akan tabbatar da ana girmama shanu da kare tsarkinsu ya ce, malaman kiwon lafiyar dabbobi da 'yan sanda za su yi aiki tare domin duba dafa-dukka da ake sayarwa a yankin Mewat dan tabbatar da ba naman shanu a ciki.

Idan har aka gano naman shanu a cikin abinci to lamarin zai kai ga gaban alkali.

Amma wani lauya musulmi a yankin na Mewat yace, ba a yin dafa-dukka ta Biryani da naman shanu.

Lauyan ya kuma zargi mabiya Hindu masu tsananin kishin kasa da kokarin haifar da tsoro a yankin.

Labarai masu alaka