Iran ta la'anci sarakunan Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ayatullahi Khamenei ya ce sakacin hukumomin Sa'udiyya ne sanadiyar mutuwar alhazai a turmutsutsin hajjin bara

Iran ta ƙara kausasa sukar da take yi wa sarakunan Sa'udiyya.

Jagoran addinin Iran din, Ayatullahi Khamenei ya bayyana gidan sarautar Sa'udiyyar a matsayin mugaye kuma la'anannu.

Ya kara da cewa ce gidan sarautar Sa'udiyyar ba su cancanci su zama wadanda wurare masu tsarki na Makkah da Madina ke karkashin kulawarsu ba.

Jagoran addinin Iran din ya shaida wa wadanda 'yan'uwansu suka rasu a turmutsutsin hajjin bara cewa sakacin hukumomin Sa'udiyyar ne sanadiyar mutuwarsu.

Shi ma shugaban Iran din Hasan Rauhani ya yi tir da Sa'udiyyar a taron majalisarsa ta zartarwa, inda ya ce wajibi ne a dora alhakin lamarin a kan gwamnatin Sa'udiyyar.

Koda ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya ce, hakika akwai bambanci tsakanin musulunci da wahabiyanci da irin tsaurin ra'ayin da Saudiyya take yadawa a duniya.

Tuni dai Amurka ta tsoma baki cikin wannan lamari inda ta ce, musayar kalaman masu zafi tsakanin Saudiyya da Iran zai kara ruruta rikici ne a yankin gabas ta tsakiya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, ba ta ji dadin yadda kasashen biyu suke musayar kalamai masu zafi ba a tsakaninsu.

Cacar bakin dai ta samo asali ne yayin da Iran ta zargi sarakunan Saudiyya da gazawa wajen gudanar da aikin Hajji.

Iran ta fadi hakan ne dangane da turmutsutsun da ya kai ga mutuwar alhazai fiye da 2000 bara, kuma 400 daga cikinsu 'yan kasar Iran ne.

Image caption Babban malamin Saudiyya ya ce, 'yan Iran ba musulmi ba ne

Ranar Laraba ce babban Muftin kasar Sa'udiyya, ya yi kakkausar suka a kan kasar Iran, yana cewa 'yan kasar ba Musulmi ba ne.

Babban Muftin, Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana Iraniyawan a matsayin wadanda ke da alaƙa da addinin Zorosta, wanda ke da karfi a kasar gabanin Musulunci.

Labarai masu alaka