Nijar: Ana korafi kan hana fitar da jakai

Hakkin mallakar hoto AFP

A jamhuriyar Nijar hadin gwiwar kungiyoyin mazauna karkara ya nuna rashin gamsuwa kan dokar da gwamnatin kasar ta hana fitar da jakai daga kasar zuwa kasashen waje.

Gwamnatin na da fargaban cewa, fitar da jakan masu yawa da ake yi na kawo raguwar jakai a cikin kasar kuma ya na barazana haddasa bacewarsu.

Kungiyoyin mazauna karkara ta bakin daya daga cikin shugabanninsu Malam Abdu Nino, ya ce dokar ba ta dace ba.

Ya ce, fitar da jakan wata dama ce ga talaka ya sayar da jaki ko jakunansa da tsada ta yadda zai ci albarkarcinsu kamar yadda ake cin albarkarcin sauran dabbobi.

Koda wasu kasashen Afirka ta yamma, kamar Burkina Faso da Mali sun kafa dokar fitar da jakai daga kasashen na su.

Kasar China ce ta fi sayen fatar jakai, inda take amfani da sinadarin gelatin wajen hada magunguna na kara karfin mazakuta da kuma man shafawa mai-da-tsohuwa-yarinya. Miliyoyin 'yan Nijar ne dai ke amfani da jakai musamman domin yin sufuri.

Labarai masu alaka