Nigeria: Fada tsakanin Hausawa da Fulani

Jihar Lagos a arewacin Nigeria an gwabza mummunan fada tsakanin Fulani da Hausawa a babbar mayankar dabobbi dake Agege.

Wadanda suka ganewa idanunsu lamari sun ce, an samu asarar rayuka da kuma dukiya mai yawa.

Amma rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta musanta batun asarar rayuka.

'Yan sanda sun ce, fadan ya samo asali ne bayan wani Bafulatani ya bugi wata budurwa Bahausa, lamarin da Hausawa ba su ji dadinsa ba.

Wannan ta sa an gwabza fada tsakanin Hausawan da Fulani.

Labarai masu alaka