Me matasa ke yi don raya yankunansu?

A wani bangare na shirye-shiryen da BBC Media Action ke yi domin fadakar da mutane, musamman matasa, su shiga a dama da su wajen ci gaban al'umma, an kirkiro wani maudu'in don tattaunawa a shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter, wato #NoSidonLook.

Maudu'i ne dai da ke tattaunawa a kan gudunmawar da matasan za su iya bayarwa wajen kawo ci-gaba a yankunansu, kuma ma'anar maudu'in #NoSidonLook ita ce kada ka zauna kawai kana kallo.

A ranar Laraba ne dai ake kaddamar da yekuwar, don zaburar da matasa su tashi tsaye su kawo sauye-sauyen da za su haifar da ci-gaba a yankunansu.

Za ku iya shiga wannan muhawara a shafinmu na Twitter, kuma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafinmu na Facebook.

Hakanan kuma za ku iya aiko mana da hoto ko bidiyo na abubuwan da suka lalace a yankunanku ko ayyukan da kuka aiwatar na taimakon kai-da-kai. Idan kuka aiko hotunan abubuwan da suka lalace, ku hado da bayani a takaice a kan abin da kuke yi, ko kuke tunanin yi don ganin an kawo gyara.

Labarai masu alaka