Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahya da Naziru Mikailu

time_stated_uk

 1. Sai a tara a karo na gaba

  To jama'a da haka muka kawo karshen wannan sharhi da muke kawo muku game da zaben Amurka, inda Donald Trump ya doke Hillary Clinton domin samun nasara. 

  Sai a kasance da shafinmu na BBCHausa.com domin cigaba da samun bayanai kan zaben da kuma sauran labarai. 

  Bari mu barku da hotunan mutanen da suka yi aiki kan wannan shafi da sauran rahotannin da kuka ji:

  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
 2. Shugaban Phillippines ya yi wa Trump san-barka

  Shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte ya taya murna ga Donald Trump, a cewar wani ministan kasar. 

  Duterte "Yana sa ran yin aiki tare da sabuwar gwamnatin domin inganta dangantaka tsakanin Philippines da Amurka ta hanyar mutunta juna da cin gajiyar juna da kuma tabbatar da dimokradiyya da mulki na gari a tsakanin mu", in ji ministan.    

  Rodrigo Duterte ya ce zai yi aiki tare da Trump
 3. Tanzania ta taya Trump murna

  Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya taya shugaban Amurka mai jiran gado murnar nasarar da ya samu, yana mai ba shi tabbacin ci gaba da kawance tsakanin kasashen biyu.

  View more on twitter
 4. Zan sa Amurka a gaba - Trump

  Donald Trump

  Mista Trump ya ce yana sa ran kulla yarjejeniya mai kyau da sauran kasashen duniya:

  Quote Message: Babu wani mafarki ko hasashe da ba a iya cimma wa ba. Amurka ba za ta sake karbar wani abu da ba shi ne mafi kyau ko inganci ba. Dole ne mu sake kwato kasarmu, sannan mu cigaba da burin samun nasara da cigaba. A kodayaushe zan saka Amurka a gaba. from Donald Trump
  Donald Trump
 5. Zan zama shugaban kowa da kowa - Trump

  Donald Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa: "Na yi alkawari ga dukkan Amurkawa cewa zan zama shugaba na kowa da kowa. Kuma hakan na da muhimmanci a gare ni".

  Ga wadanda suka yi goyon bayana, duk da cewa ba su da yawa, ina mika hannu na gare su domin neman shawarwari ta yadda za mu yi aiki tare domin hada kan kasarmu". 

 6. Ku yi hakuri da jiran da kuka yi

   "Ina gode muku matuka. Ku yi hakuri saboda mun ajiye ku anan kuna ta jiranm u, lamari ne mai cike da rudani," a cewar sabon shugaban mai jiran gado.

 7. Turmp ya bayyana

  Donald Turmp ya bayyana a gaban magoya bayansa

 8. Labarai da dumi-dumiClinton ta 'amince da shan kaye' a zaben Amurka

  Wasu majiyoyi na cewa 'yar takarar shugabancin Amurka ta jam'iyyar Democrats, Hillary Clinton ta amince da shan kaye a zaben shugaban kasar, wanda Donald Trump ya lashe.

  An ce ta kira Donald Trump domin taya shi murna.

 9. Labarai da dumi-dumiTrump ya isa dandalin magoya bayansa

  Gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa Donald Trump na kan hanyar isa otal din Midtown Hilton, inda magoya bayansa suka taru domin bikin murnar lashe zabe.

 10. Le Pen ta taya Trump murna

  Shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta National Front Marine Le Pen ta taya Donald Trump murna a daidai lokacin da ya kama hanyar lashe zaben Amurka da aka yi a ranar Talata, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

  A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce "Fatan alheri da murna ga sabon shugaban Amurka Donald Trump da kuma al'ummar Amurka da aka 'yantar!".

  Kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa Le Pen za ta iya lashe zagayen farko na zaben shugabancin kasar Faransa. 

  Sai dai za ta sha kaye a zagaye na biyu.

  Marine Le Pen
 11. Labarai da dumi-dumiOfishin kamfen din Clinton ya yi raddi

  Shugaban ofishin yakin neman zaben Hillary Clinton John Podesta ya ce ba za su ce komai a kan sakamakon zaben kasar ba tukunna. 

  Ya ce, "Ana ci gaba da kidaya kuri'u ... Akwai jihohi da dama da muke yin kankankan don haka babu abin da za mu ce a yanzu." 

  Mista Podesta ya kara da cewa "ya kamata mutane su je gida su yi bacci domin za a sanar da sakamakon zaben ne gobe."

 12. Jamus ta 'kadu' da jin Trump na kan gaba

  Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta shaida wa gidan talabijin din kasar cewa ta yi "matukar kaduwa" da jin cewa dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump na kan hanyar lashe zaben Amurka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. 

  Ursula von der Leyen ta ce akwai matsala idan Trump ya ci zabe
  Image caption: Ursula von der Leyen ta ce sun sha mamaki
 13. Mexico ta kira taron manema labarai

  Ministan Kudi na kasar Mexico Jose Antonio Meade da kuma shugaban bankin kasar Agustin Carstens sun kira taron manema labarai wanda za a yi da yammacin ranar Laraba.

  Ana sa ran za su tattauna kan faduwar darajar kudin kasar peso, da kuma katangar da Mista Trump ya nace cewa zai gina tsakanin Amurka da kasar a lokacin yakin neman zabensa.

  Ana sa ran za a tattauna kan faduwar darajar kudin kasar
  Image caption: Ana sa ran za a tattauna kan faduwar darajar kudin kasar
 14. Republican ta rike rinjayen da take da shi a majalisar wakilai

  Jam'iyyar Republican ta lashe zaben majalisar wakilai, abin da ya ba ta damar ci gaba jan ragamar majalisar bayan shafe shekara shida tana kai.

  Kamfanin dillancin labarai na  Associated Press ya Democrat sun gaza samun rinjaye.

  Ana ci gaba da kirga kuri'u sai dai Republican ta lashe kujeru 218, fiye da adadin da ake bukata domin samun rinjaye.

  Majalisar dokokin Amurka
 15. Ra'ayoyinku kan zaben Amurka

  Jama'a da dama na tafka muhawara a shafinmu na BBC Hausa Facebook kan sakamakon zaben Amurka da ke fitowa inda Donald Trump yake kan gaba:

  Quote Message: To sai mu ce Allah ya ba ta (Clinton) nasara, amma fa gaskiya cikinmu ya duri ruwa ganin yadda Donald Trump yake kan gaba a sakamakon zaben kasar from Rukaiyya Usman Fari Jebuwa
  Rukaiyya Usman Fari Jebuwa
  Quote Message: Hakika ana tabka gumurzu tsakanin Trump da Hillary, amma mudai fatan shi ne Allah ya ba wa Amurkawa shugaba mai son hada kawunan al'ummar kasar ba tare da nuna bambanci ba from Muhammad Sulei Garin Rijiya
  Muhammad Sulei Garin Rijiya
  Quote Message: Ina fatan daga karshe Mrs Hillary za ta yi galaba kan abokin karawarta domin ta kasance mace ta farko a mukamin shugabancin Amurka. from Abdulkadri Hussaini Jambil
  Abdulkadri Hussaini Jambil
 16. Trump ya lashe zaben manyan jihohi

  Donald Trump ya lashe manyan jihohi irin su Florida, Ohio, Iowa da kuma North Carolina. 

  Haka kuma ya lashe Utah, Alabama, Kentucky, South Carolina, Nebraska, Indiana, West Virginia, Mississippi, Tennessee, Oklahoma da kuma Texas, kamar yadda gidan talabijin na ABC ya yi hasashe.

  Trump ya kuma ci zaben Georgia, Missouri, Montana, Louisiana, Arkansas, Kansas, North Dakota, South Dakota, Idaho da Wyoming - dukkan su jihohi ne na masu ra'ayin rikau.

  Trump ya ce zai hana Musulmi shiga Amurka
 17. George W Bush bai yi zaben shugaban kasa ba

  Tsohon shugaban Amurka, George W Bush, wanda dan jam'iyyar Republican ne, bai zabi Donald Trump da Hillary Clinton ba.

  Mai magana da yawunsa ya ce bai zabi kowa ba a bangaren shugaban kasa, amma a bangaren 'yan majalisar dokoki ya zabi jam'iyyar Republican. 

  Babu wani daga cikin iyalan Bush da ya yi wa Mr Trump yakin neman zabe ko kuma zabensa.

  George W Bush ya zama shugaban Amurka sau biyu
  Image caption: George W Bush ya ce bai ga dalilin yin zaben shugaban kasa ba
 18. Clinton ta lashe Nevada

  Hillary Clinton ta lashe kuri'un jihar Nevada, wacce jam'iyyar Republican ke lashewa a tarihi, sai dai yanzu lamarin ya sauya saboda karuwar al'ummar Latin masu amfani da harshen Spaniya.   

  Clinton