Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Da fatan za ku tara a shirinmu na gobe domin jin wasu labarin wasanni

 2. Kwantan wasan Firimiyar Nigeria

  Kai tsaye
 3. Burnley ta dauki Bardsley

  Burnley ta kammala daukar mai tsaron bayan Stoke City, Phil Bardsley. Dan wasan mai shekara 32 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a Turf Moor.

  Kai tsaya
 4. Dembele zai ci gaba da zama a Celtic

  Brendan Rodgers ya ce Moussa Dembele yana jin dadin zama a Celtic, kuma kungiyar ba ta shirya sayar da shi ba.

  Dembele ya ci kwallo 32 a wasa 39 da ya yi wa Celtic a kakar da ta kare tun lokacin da ya koma kungiyar daga Fulham kan fan 500,000.

  Celtic za ta kara da Rosenborg a wasan cike gurbin gasar cin kofin Zakarun Tuari a Celtic Park a ranar Laraba.

  Quote Message: Babu kulob din da ya taya dan kwallon mai shekara 21, duk da rade-radin cewar kungiyoyi 10 na son zawarcin Dembele. from Brendan Rodgers
  Brendan Rodgers
 5. An ci kwallo 308 a Firimiyar Nigeria

  Bayan da aka yi wasa 308 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria, an ci kwallo 611 bayan da aka kammala wasannin mako na 31 a ranar Lahadi.

  Kuma kwallo 472 aka ci a gida yayin da aka zazzaga 139 a waje, kuma saura wasa 72 a kare gasar da ake yi.

  Kai tsaye
 6. Robert Kubica zai yi tseren gwaji

  Robert Kubica zai yi wa kamfanin Renault tseren mota a matsayin gwaji a karon farko a Hungary a ranar 2 ga watan Agusta.

  Rabon da dan wasan mai shekara 32 ya tuka mota a Formula 1 tun hatsarin da ya yi a 2011, inda jikinsa ya shanye in banda hannunsa na hagu da ya dunga aiki.

  Kai tsaye
 7. Greg Rutherford ba zai yi Burtaniya wasa ba

  Zakaran tsallen badaken duniya Greg Rutherford ya janye daga shiga gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da za a yi a Landan, sakamakon raunin da ya yi.

  Dan wasan Burtaniya wanda ya ci lambar zinare a gasar Olympic da aka yi a Landan a 2015 da kambun duniya da ya lashe a 2015 ya ce ya yi bakinciki da ba zai shiga wasannin ba.

  Haka shima Richard Kilty wanda aka zaba ya yi wa Burtaniya tseren mita 400 ta 'yan wasa hudu ba zai shiga gumurzun ba, sakamakon karya tsaya da ya yi a lokacin atisaye.

  Burtaniya ta kara Shara Proctor da Jazmin Sawyers da Lennie Waite da Marc Scott da kuma Jess Turner cikin tawagarta.

  Kai tsaye
 8. Conte ya yi wa Fabregas alkawari

  Kocin Chelsea, Antonio Conte ya yi wa Cesc Fabregas alkalin zai dinga saka shi a wasa akai-akai don haka ya bukaci dan kwallon ya ci gaba da zama a Stamford Bridge in ji Everning Standard.

  Kai tsaye
 9. Wasu damben da aka yi a gidan Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria

  Video content

  Video caption: Wasu damben gargajiya da aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria
 10. Maradona ya goyi a samar da na'ura da za ta taimakawa Alkalan wasa

  Diego Maradona ya goyi da bayan a kirkiro kimiyar da za ta taimakawa alkalan wasa wajen tantance idan kwallo ya shiga raga ko akasin hakan. Maradona ya ci Ingila da hannu a gasar cin kofin duniya wasan daf da na kusa da na karshe inda Argentina ta lashe karawar da ci 2-1. Haka kuma a fafatawar ce Maradona ya yi wata bajinta inda ya yanke masu tsaron bayan Ingila biyar a karawar da Ingila.

  Kai tsaye
 11. Leicester City ta dauki Eldin Jakupovic

  Leicester City ta dauki mai tsaron raga Eldin Jakupovic daga Hull City kan yarjejeniyar shekara uku in ji Marca.

  Dan kwallon shi ne na uku da Leicester ta dauka a bana bayan Harry Maguire da kuma Vicente Iborra.

 12. Jota ya koma Wolves da taka-leda

  Wolves ta dauki aron matashin dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Diogo Jota daga Atletico Madrid.

  Dan wasan mai shekara 20 ya buga wa Porto wasanni aro a bara, inda ya yi wasa karkashin kocin Wolves Nuno Espirito Santo. Jota ya fara buga kwallo a Pacos Ferraira daga nan ya koma Atletico kan yarjejeniyar shekara biyar a bara.

  Kai tsaye
 13. Palace ta dauki Riedewald

  Crystal Palace ta dauki dan kwallon Netherlands mai tsaron baya Jairo Riedewald daga Ayax kan yarjejeniyarshekara biyar.

  Riedewald, mai shekara 20, a baya ya buga kwallo karkashin sabon kocin Palace Frank de Boer, wanda ya fara saka shi a wasa a 2013.

  Dan kwallon ya yi wasa 93 kuma yana daga 'yan wasan da suka ci kofin gasar Netherland a 2014.

  Kai tsaye
 14. Liverpool ta ce Palace ta biya kudin Sakho

  Daily Mirror ta wallafa cewar Liverpool ta shaidawa Crystal Palace cewar ko dai ta biya kudin Mamadou Sakho fan miliyan 30, idan ba haka ba, ba za ta amince ta sake bata shi aro ba.

  Kai tsaye
 15. United za ta iya daukar Reanato

  Independent ta wallafa cewar Manchester United za ta iya daukar Renato Sanchez na Bayern Munich in ji koci Carlo Ancelotti, wanda ya bayar da hasken cewar ba zai bar Arturo Vidal ya bar buga gasar Bundesliga ba.

 16. Leicester ta yi wa Mahrez farashi

  Roma ta tanadi fan miliyan 30 da wasu karin kudin tsarabe-tsarabe daukar Riyad Mahrez dan kwallon tawagar Algeria, sai dai Leicester City ta ce sai dai a biyata fan miliyan 50 in ji Daily Mail.

  Tun a cikin watan Mayu Mahrez ke son barin Leicester City

  Kai tsaye
 17. Takaitattun Labarin Wasanni na safiyar Talata

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labarin Wasanni
 18. Madrid za ta dauki Mbappe a bana

  Real Madrid za ta sayi Kylian Mbappe kan kudi Yuro miliyan 180 daga Monaco domin ya buga mata tamaula a Santiago Bernabeu a bana in ji jaridar Marca.

  A labarin da ta wallafa ta ce wannan kudin da Madrid za ta biya Monaco zai haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a 2016.

  Kai tsaye
 19. Swansea ta yi watsi da tayin Everton na sayen Sigurdsson

  Swansea ta yi watsi da tayin fan miliyan 50 da Everton ta yi domin sayen dan wasan Iceland Gylfi Sigurdsson.

  Swansea na bukatar fan miliyan 50 ne kan dan kwallon mai shekara 27.

  Sigurdsson bai bi kulob din zuwa Amurka ba, kuma yana ci gaba da atisayi ne da tawagar 'yan kasa da shekara 23 ta kulob din.

  Tayin na ranar Litinin shi ne na farko da Everton ta yi kan dan wasan na tsakiya, sai dai ita ma Leicester City ta yi yunkurin sayensa tun farko.

  Gylfi Sigurdsson