Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe!

  Jama'a, abun da ya samu kenan a jerin rahotannin wasannin da muke kawo muku kai-tsaye a wannan shafin a yau. Ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa.

 2. Birminghan ta dauki aron dan Chelsea

  Kungiyar kwallon kafa ta Birmingham City ta dauki aron dan wasan tsakiyar Chelsea, Jeremie Boga, na kaka daya.

  Dan wasan dan asalin kasar Ivory Coast, ya shafe shekara biyu da ya wuce a Rennes da Granada a zaman aro.

  Birmingham
 3. Siem de Jong ya sake komawa Ajax daga Newcastle

  Ajax ta sake sayan dan wasan tsakiyar kasar Netherlands, Siem de Jong, daga Newcastle kan kudin da rahotanni suka ce ya kaifam miliyan 4.

  Dan wasan mai shekara 28 ya koma Magpies ne daga Ajax a shekarar 2014 kan kudin da ba a bayyana yawanshi ba a wata yarjejeniyar shekara shida, amman ya yi ta fama da raunuka, ciki har da ciwon huhu. Ya buga wasanni 26, yawancinsu a matsayin wanda ya canji wani dan wasa, amman ya buga wasa sau 23 a lokacin ya je wasan aro a PSV Eindhoven a kakar bara.

  Ajax
 4. An yi wa shugaban Barcelona ihu

  Bikin gabatar da sabon dan kwallon da Barcelona ta saya, Ousmane Dembele ya ci karo da cikas, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta rera wakokin neman shugabanta ya yi ritaya.

  Dembele mai shekara 20, ya zama na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin tamaula a duniya kan fam miliyan 135.5, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain da murza-leda kan fam miliyan 200.

  Bikin ya ci karo da cikas bayan da aka yi jinkirin sa'a biyu, sakamakon rashin samun takardun rijistar dan kwallon daga Dortmund.

  A lokacin ne magoya bayan Barcelona 18,000 suka rinka busa usur da rera wakokin cewar Bartomeu ya yi ritaya.

  Karanta cikakken labarin a nan

  Shugaban kulob din Barcelona
  Image caption: A bana ne Real Madrid ta doke Barcelona 5-1 gida da waje a Spanish Super Cup
 5. Messi ya ci kwallo sama da 350 a La Liga

  Dan wasan Barcelona da tawagar kwallon kafa ta Argentina Lionel Messi ya ci kwallo sama da 350 a gasar La Liga.

  Dan wasan ya ci 349 kafin ya kara biyu a karawar da Barcelona ta ci Deportivo Alaves 2-0 a ranar Asabar a wasan mako na biyu a gasar ta La Liga a ranar Asabar.

  Messi ya zama na biyu da ya fi cin kwallaye da yawa a kungiya daya tsakanin manyan gasar kwallon kafa ta Turai, bayan Gerd Muller da ya ci wa Bayern Munich kwallo 365.

  Cikin kwallo 351 da ya ci a La Liga, guda 274 da kafar hagu ya ci sannan ya zura 63 a raga da kafar dama, kuma 14 da kai ya ci su.

  Messi ya ci Espanyol a kakar wasan 2007 da hannu, an kuma karbi kwallon a cikin wadanda ya ci da kai.

  Messi
 6. Las Palmas na neman dan wasan Chelsea

  Kungiyar kwallon kafa ta Las Palmas da kungiyar Cagliari suna neman dan wasan gaban Chelsea, Loic Remy, mai shekara 30, in ji jaridar Daily Mail.

  Loic Remy
 7. Chelsea za ta sake taya Llorente

  Chelsea za ta sabunta sha'awarta ta dan wasan gaban Swansea, Fernando Llorente, mai shekara 32, ta hanyar taya shi dai-dai lokacin da kungiyar take neman sayan akalla 'yan wasa uku kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji jaridar Independent.

  Fernando Llorente
 8. Conte na son Chelsea ta kara karfi

  Kociyan Chelsea, Antonio Conte, ya ce Blues na bukatar kara 'yan wasa domin kara wa kulob din karfi.

  Ya ce kungiyar na iya kokarinta na kara 'yan wasa.

  Conte
 9. Nawa kudin Mayweather a yanzu?

  Bayan Floyd Mayweather ya doke Conor McGregor a damben boksin da suka yi karshen mako, kudin dan bamben ya kai akalla fam miliyan 450, in ji jaridar Mirror.

  Mayweather
 10. Borussia Dortmund ta sayi Yarmolenko

  Borussia Dortmund ta sayi dan wasan gaban Dynamo Kiev dan asalin Ukraine, Andriy Yarmolenko kan kudin da ba a bayyana ba a wata yarjejeniyar shekara hudu.

  An bayyana zuwan dan shekara 27 din ne wasu mintuna kafin Barcelona ta bayyana cewar tsayi dan wasan gaban Dortmund, Ousmane Dembele, a wata yarjejeniyar fam miliyan 135.5.

  Yarmolenko
 11. Liverpool ta sayi Naby Keita

  Liverpool ta sayi dan wasan tsakiyar Leipzig, Naby Keita, kuma dan wasan zai fara taka wa Reds leda ne ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2018.

  Keita na cikin 'yan wasan da kociya Jurgen Klopp yake nema.

  Kudin yarjejeniyar sayan dan wasan ya fi fam miliyan 35 da Liverpool ta biya wajen sayan Andy Carroll daga Newcastle .

  Naby Keita
 12. PSG ta cimma yarjejeniyar aron Kylian Mabappe

  Paris St-Germain ta cimma yarjejeniyar aron dan wasan gaban Monaco mai shekara 18, Kylian Mbappe, da zabin sayanshi kan kudi fam miliyan 166, in ji L'Equipe .

  Nbappe
 13. Barca ta sayi Dembele

  Barcelona ta kammala sayan dan wasan gaban Borussia Dortmund, Ousmane Dembele, kan kudi fam miliyan 96.8, kuma za a iya kara kudin zuwa fam miliyan 135.5.

  San wasan dan Faransa mai shekara 20 ya rattaba hannu kan yarjejejniyar shekara biyar a Nou Camp tare da jagoran kungiyar, Josep Maria Bartomeu ranar Litinin.

  Yarjejeniyar ita ce ta biyu a tsada a fagen tamaula bayan wadda Neymar ya rattaba wa hannu kan kudi fam miliyan 200.

  Dembele
 14. 'Mene ne amfanin zaman Sanchez a Arsenal?'

  Tsohon dan wasan gaban Arsenal, Thierry Henry, ya nuna tababa game da daililin da ya sa dan wasan gaban Chile, Alexis Sanchez, zai ci gaba da zama a Gunners bayan Liverpool ta lallasa Arsenal din 4-0 . Dan wasan mai shekara 28 yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa kuma an alakanta shi da komawa Manchester City, in ji Sky Sports.

  Sanchez
 15. Napoli na son mai tsaron gidan Liverpool

  Kungiyar kwallon kafa ta Napoli na hakon mai tsaron gidan Liverpool,Simon Mignolet, mai shekara 29, in ji Gianluca Di Marzio.

  Simon Mignolet,
 16. West Brom ta taya dan wasan Fenerbache

  West Brom ta yi wa Fenerbache tayin fam miliyan 10 kan dan wasanta mai shekara 28, Josef de Souza, da aka fi sani da Souza, tare da tambaya game da dan wasan bayan Bournemouth, yrone Mings, mai shekara 24, jaridar Daily Mail.

  Josef de Souza
 17. Mustafi na shirin barin Arsenal

  Dan wasan bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, yana shirin barin Gunners domin komawa Inter Milan shekara daya kacal bayan dan wasan na Jamus, mai shekara 25, ya koma Arsenal daga Valencia kan kudi fam miliyan 35, in ji ESPN.

  Shkodran Mustafi
 18. Zamalek ta yi sabon kociya

  Kungiyar kwallon kafa ta Zamalek da ke Masar ta fitar da sanarwar cewar Montenegrin Nebojsa Jovovic ya rattaba ahannu kan yarjejeniyar shekara biyu a matsayin kociya.

  Kociyana ya maye gurbin dan kasar Portugal, Augusto Inacio wanda ya bar kulob din a watan Ylulin bayan ya shafe kasa da wata hudu yana jagorancin kungiyar .

  Nebojsa Jovovic
  Image caption: Nebojsa Jovovic ne ya jagoranci kungiuyar Al Faisaly ta Jordan zuwa wasan karshe na cin kofin larabawa a farkon watannan
 19. 'Liverpool za ta sayi Chamberlain'

  Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tashi tsaye kan batun neman Oxlade-Chamberlain, wanda ake ganin ya fi son ya koma Chelsea, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta ruwaito.

  Arsenal tana shirin sayen dan kwallon Real Madrid, Marco Asensio, a kan fam miliyan 75 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai ranar Alhamis, in ji jaridar Sunday Express.

  Chamberlain
 20. Kociyan West Ham na tsaka-mai-wuya

  Kociyan West Ham United, Slaven Bilic, yana kokarin kare aikinshi bayan ya kasa samun maki ko daya a wasanni uku na farko da ya yi a gasar Firimiya, in ji jaridar Sun.

  Slaven Bilic