Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Jacob Zuma ya ce Mugabe na cikin koshin lafiya
 2. Sojoji na dukan 'yan sanda
 3. Ina Grace Mugabe take?
 4. Gidan rediyon kasar na sanya wake-waken juyin-juya-hali
 5. Sojojin kasar sun ce Robert Mugabe yana cikin koshin lafiya

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sojojin Zimbabwe 'sun kakkabe masu laifi'

  Jaridar Chronicle wadda ke karkashin ikon gwamnatin Zimbabwe a birnin Bulawayo, ta wallafa labarai na musamman game da rikicin kasar.

  Ta fito da kanun dake cewa: "Sojoji sun karbe iko", tana mai cewa sojoji sun karbe mulki domin su "kakkabe masu laifuka na jam'iyyar ZANUPF".

 2. Kalli yadda sojojin Zimbabwe suka karbe iko da kasar

  Video content

  Video caption: Yadda sojoji suka kwace iko a Zimbabwe
 3. Ina Grace Mugabe take?

  Wata jarida mai zaman kanta a Namibiya ta ce gwamnatin Namibiya ba ta yi tsokaci ba game da rade-radin da ake yi cewa matar Shugaba Mugabe ta isa kasar.

  Grace Mugabe
  Image caption: Har yanzu ba a san inda Grace Mugabe take ba
 4. Gidan talabijin din Zimbabwe ya koma watsa shirye-shirye

  Gidan talabijin mallakar Zimbabwe ta fara watsa shirye-shirye kamar yadda ta saba bayan ta shafe sa'o'i tana watsa wakoki na kishin kasa da kuma neman 'yanci.

  Daga bayan misalin karfe 12 na rana ne ZBC ta koma watsa shirye-shirye kamar yadda ta saba.

  .
  Image caption: .
 5. 'Munafuncin dodo ne yakan ci mai shi'

  Wani lauya a Zimbabwe ya bayyana abin da ke faruwa a kasar a matsayin munafuncin dodo ne dake cin mai shi.

  Alex Magaisa, wanda tsohon mai bai wa madugun 'yan adawar kasar, Morgan Tsvangirai, shawara ne ya shaida wa kafar Al Jazeera cewa Shugaba Mugabe ya ci gajiyar tsoma bakin soji a harkar siyasar kasar musamman tun shekarar 2002.

  Ya ce yanzu dodon da Shugaba Mugabe ya hada ne "yake cin shi:"

 6. Me ya sa sojoji ba sa son amfani da kalmar juyin mulki?

  Rashin ambatar kalmar juyin mulki shi ne abun da ya fito cikin jawabin da manjo janar Sibusiso Moyo ya gabatar a kafar yada labaran Zimbabwe ZBC, da safiyar Laraba.

  Janar Moyo jaddada cewa wannan ba juyin mulki ba ne.

  Saboda haka me ya sa wannan yake da muhimmanci?

  Kungiyar Tarayyar Afirka AU da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (Sadc), ba sa lamuntar juyin mulki.

  Mun ga hakan ya faru a Burkina Faso a shekarar 2015 a lokacin da kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Burkina Faso ta kuma kakaba takunkumi kan wadanda suka yi yunkurin juyin mulki, shekara daya bayan an tumbuke Blaise Compaore wanda ya dade yana mulkar kasar.

  Ba abun mamaki ba ne cewa rundunar sojin kasar tana ta kokarin nuna cewa farar hula ce take iko da kasar har yanzu.

  Tuni dai, Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya fitar da wata sanar a madadin SADC cewa yankin ba zai lamunci juyin mulki ba.

  .
  Image caption: .
 7. 'Sojoji na dukan 'yan sanda'

  Wata da ke zaune a Harare, Denissa Moyannah, ta shaida wa BBC cewa ta kai ziyara tsakiyar birnin, daga gidanta da ke unguwar masu hannu da shuni ta Borrowdale da safiyar Laraba:

  Ta ce motoci masu sulke sun cika ko ina a tsakiyar birnin inda suke tsayar da ababen hawa a tsakiyar hanya.

  Ta ce sojoji na dukan 'yan sanda.

  Ta kara da cewa kafar talabijin din kasar tana saka wakokin neman 'yanci.

  Ta ce kuma kura ta lafa a babban birnin Zimbabwe din.

  .
  Image caption: .
 8. Manyan masu neman iko a ricikin Zimbabwe

  Zimbabwe
  Image caption: Da alamar cewa Robert da Grace Mugabe sun ja daga da tsohon mataimakin shugaba Emmerson Mnangagwa (na biyu daga dama) da kuma hafsan soji Janar Constantino Chiwenga
 9. Yadda wani mai zanen barkwanci ke kallon lamarin

  Wani mai zanen barkwanci da ke Kenya, Victor Ndula, yana cikin wadanda suke neman lokacin da za a iya cewa juyin mulki ba juyin mulki ba ne.

  Kalli yadda yake ganin rikicin Zimbabwe a jaridar Star ta Kenya:

 10. 'Akwai rashin tabbas a Zimbabwe'

  Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson, ya ce ya kamata mutanen Zimbabwe su guji tashin hankali.

  Boris Johnson, wanda zai amsa tambayoyi game da batun a majalisar Birtaniya a yau, ya ce:

  A halin yanzu lamarin na cike da rashin tabbas kuma yana da wahala mutum ya iya fadin yadda lamarin zai kasance

  Ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne kowa yana son ya ga Zimbabwe ta kasance cikin zaman lafiya da ci gaba.

  Boris Johnson
  Image caption: .
 11. Tarayyar Turai ta nemi a sasanta rikicin cikin lumana

  Tarayyar Turai ta nemi a sasanta rikicin Zimbabwe cikin lumana bayan sojoji sun karbe iko.

  Wani mai magana da yawun tarayyar ya ce:

  Abubuwan da suka faru a fagen siyasar Zimbabwe a baya-bayan nan da abubuwan da ke tattare da su abun damuwa ne.

  Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su koma sulhu daga fito-na-fito domin a sasanta cikin lumana."

 12. 'An kama 'yan sanda a Harare'

  Wata lauya a babban birnin kasar, Harare, ta wallafa wani hoto a shafinta na Twitter da ke nuna wasu 'yan sanda suna zaune a kasa yayin da wasu sojoji ke sa ido.

  Fadzayi Mahere, wadda ke fatan za ta zama 'yar majalisa a mai wakiltar Mount Pleasant, a Harare, ta dauki hoton ne daga tagar ofishinta ranar Laraba.

  Ba a san abin da ya faru da 'yan sandan ko kuma dalilin da ya sa aka hada su a wuri daya haka.

  Fadzayi Mahere
  Image caption: .
 13. Bayanai game da Robert Mugabe

  Karanta bayanai game da rayuwar mutumin da ya mamaye siyasar Zimbabwe tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1980.

  An haife shi a shekarar 1924

  Ya karanci aikin malanta

  Ya yi aki a Ghana inda ya hadu da matarsa ta farko Sally Hafron

  1964: Gwamnatin Rhodesian ta daure shi

  1980: Ya lashe zaben bayan 'yancin kai

  1996: Ya auri Grace Marufu

  2000: Ya sha kaye a zaben raba gardama kan ikon shugaban kasa da kuma filaye mallakar fararen fata

  2008: Ya zo na biyu bayan Morgan Tsvangirai a zagaye na farko na zaben shugaban kasa, amman madugun 'yan adawar ya janye daga zaben da aka yi a zagaye na biyu yayin da ake kai hare-hare kan magoya bayansa

  2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin Firayim minista a lokacin da kasar take fuskantar tabarbarewar tattalin azriki

  2016: Ya gabatar da takardun lamuni yayin da karancin kudade ya yi kamari

  2017: Ya kori amininsa wanda suka dade tare, mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa

  Robert Mugabe
  Image caption: Shugaba Robert Mugabe ya auri matarsa ta farko Sally Hayfron a shekarar 1961 zuwa lokacin da ta rasu a 1992
 14. 'Grace Mugabe ba ta da tagomashi a jam'iyyar Zanu-PF'

  Nick Mangwana, wani wakilin jam'iyyar Zanu-PF a Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa shi ma ya samu rahotannin da ke cewa matar Shugaba Robert Mugabe ta bar kasar.

  Dazu dai wani dan siyasa na jam'iyyar hamayya ya shaida wa BBC cewa matar shugaban kasar ta tsere zuwa Namibiya.

  Amman Mista Mangwana ya ce a siyasar Zanu-PF, Misis Mugabe ba ta da wani tagomashi a halin yanzu, yana mai karawa da cewa ita karamar 'yar jam'iyya ce, kuma ikon da take da shi na kasancewa matar Shugaba Mugabe ne kawai.

  Grace Mugabe
  Image caption: A da dai ana sa ran Grace Mugabe ce za ta zama mataimakiyar shugaban kasa
 15. Shugaba Zuma na Afirka ta Kudu ya yi magana da Mugabe a gida

  Shugaba Robert Mugabe yana cikin koshin lafiya, in ji Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma.

  Mista Zuma ya yi magana da takwaransa mai shekara 93, wanda ya ce an tsare shi "a gida," amma yana "lafiya", kamar yadda wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya fitar.

  .
  Image caption: .
 16. Da gaske ne Grace Mugabe tana Namibiya?

  Dan majlisa na jam'iyyar hammaya Eddie Cross, ya shaida wa BBC cewa yana da imanin cewa matar Shugaban kasar Grace Mugabe ta tsere zuwa Namibiya.

  Dan siyasar na jam'iyyar MDC ya ce ya ji cewa rundunar sojin kasar ta ba ta damar barin kasar jiya da-daddare.

  Ya kara da cewa zabin wurin da za ta iya tserewa ya ragu, bayan ta far wa wata mai tallan kayan kawa a birnin Johannesburg a watan Agusta.

  Sai dai kuma rundunar sojin kasar ba ta tabbatar da ko wanne daga cikin wadannan ba.

  A jawabin da ya gabatar a talabijin din kasar, Manjo Janar Sibusiso Moyo, ya ce shi zai iya tabbatar wa kasar cewa " Shugaban kasa .... da iyalansa suna cikin wani hali na tsaro."

  Grace Mugabe
  Image caption: Mugabe dai ya auri Grace ne a shekarar 1996
 17. Rundunar soji ta toshe hanyar majalisar dokokin kasar

  Jeffrey Moyo, wani dan jarida mai zaman kansa a Zimbabwe, ya shaida wa BBC cewa sojin kasar ta toshe hanyar zuwa majalisar dokokin kasar – Nelson Mandela Avenue.

  Kuma ta hana zirga-zirga a wata babbar hanya - Samora Michel Avenue – wadda ke kusa da ofishin Shugaba Robert Mugabe, in ji shi.

  .
  Image caption: .
 18. Shugaba Buhari ya ce a mutunta kundin tsarin mulkin Zimbabwe

  Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi a zauna lafiya tare da mutunta dokar kasar Zimbabwe.

  A wata sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, Shugaba Buhari ya ce dole masu ruwa da tsaki na siyasa da na soji su guji dukkanin abubuwan da ka iya tsunduma kasar cikin tashin hankali.

  Buhari
  Image caption: .
 19. 'An kama shugaban matasan jam'iyyar ZANU PF'

  Rahotanni sun ce an kama shugaban matasan jam'iyyar ZANU PF, Kudzai Chipanga, a Harare, kwana daya bayan ya ce shi da magoya bayansa sun shirya domin su mutu wajen kare Shugaba Robert Mugabe.

  Bangaren matasan jam'iyyar yana mara wa matar Shugaba Mugabe baya domin ta gaje shi a mulki

  Kudzai Chipanga
  Image caption: Kudzai Chipanga ya yi wani jawabi na rashin tsoro ga manema labarai ranar Talata
 20. Jaridar gwamnatin Zimbabwe ba ta sauya shafinta na Intanet ba

  Jaridar gwamnatin Zimbabwe - The Herald - har yanzu ba ta sauya shafinta na Intanet domin nuna abubuwan da suka faru da dare ba.

  Har yanzu tana dauke da labarai da ke bai wa Shugaba Robert Mugabe goyon baya.

  Babban labarinta ya nuna shugaban matasan jam'iyyar Zanu-PF, Kudzai Chipanga, yana nuna goyon baya ga Mista Mugabe, yana mai cewa "za mu kare shugaban kasa da rayukanmu":

  .
  Image caption: .