Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Liverpool za ta sake wa Barcelona Countinho kuwa?
  2. Wane ne Chelsea ke son ya maye gurbin Antonio Conte?
  3. Wani dan wasa Manchester United ke so daga Juventus?

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe

Karshen labaran kasuwar musayar 'yan wasan kenan.

'Na gamsu da taka-ledar Morata'

Morata
Getty Images
Morata ya barar da damarmakin shan kwallaye a karawar kungiyarsa ta Chelsea da Arsenal

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya ce duk da cewar Alvaro Morata ya barar da wasu damarmakin cin kwallaye, shi ya gamsu da wasansa.

Conte ya ce: "Idan ya ci kwallayen, da mun sake doke Arsenal. Aikin dan wasan gaba shi ne ya ci kwallo, amma su ma 'yan wasan gaban suna kuskure. A wasanni biyu na baya bayan nan Morata bai yi sa'a ba, amma na gamsu da aikin da ya yi wa kungiyar kwallon kafar.

Ta yiwu Mourinho na kiran kansa mai barkwanci —Conte

Kocin Chelsea ya ce zai yiwu kocin Manchester United, Jose Mourinho, yana siffanta kansa ne a lokacin da ya ce yawancin koci-koci na gasar Firimiya masu barkwanci ne.

"Ya kamata ya ga yadda shi kansa yake a da. Ta yiwu yana magana ne game da yadda shi kansa yake a baya. A wasu lokutan wani zai manta abin da wani ya fada a baya."

Mourinho
Getty Images

Juventus na son sayen dan wasan Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus na da kwarin gwiwar iya sayen Emre Can daga Liverpool a lokacin bazara. Kungiyar kwallon kafar da ke wasa a gasar Serie A ta taya mai shekara 23 din fam 85,000 a ko wane mako, in ji Guardian.

Emre Can
Getty Images

Mourinho ya ce shirme ne labarin barinsa United

Kocin Man United, Jose Mourinho, ya bayyana ikirarin da ake yi cewar ya shirya domin barin Manchester United a karshen wannan kakar a matsayin "shirme".

Mourinho yana kan tattaunawa game da sabuwar yarjejeniya da kulob din, sai dai an yi ikirarin cewar kocin yana son tafiya domin ba ya jin dadi a Old Trafford.

Jose Mourinho
Getty Images

Chelsea na neman dan West Ham

Andu Carroll
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi tambaya game da dan wasan gaban Ingila da West Ham, Andy Carroll, mai shekara 28, in ji Mail.

Tottenham na son inganta kwantiragin Harry Kane

Harry Kane and Toby Alderweireld
Getty Images

Tottenham ta shirya domin inganta kwantiragin dan wasan gabanta, Harry Kane, mai shekara 24, tare da kwantiragin dan wasan bayanta dan kasar Belgium, Toby Alderweireld, mai shekara 28, in ji Independent.

Man United na son dan wasan Juventus

Alex Sandro
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana son sayen dan wasan bayan Juventus Sandro, amma Juventus ba ta son sayar da dan wasan mai shekara 26.

PSG na gogayya da Tottenham kan dan Fullham

Fullham
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain za ta yi gogayya da Tottenham wajen sayen Sessegnon wanda ake ganin farashinsa zai kai fam miliyan 30, in ji Mirror.

Fullham ma tana kokarin ganin dan wasan ya kara kaka daya a wajenta.

Chelsea na son Simeone ya maye gurbin Conte

Kwantiragin Conte zai kare a Chelsea ne a karshen wannan kakar
Getty Images
Kwantiragin Conte zai kare a Chelsea ne a karshen wannan kakar

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana son kocin Atletico Madrid, Diego Simeone, ya maye gurbin Antonio Conte a matsayin kocinta a karshen wannan kakar, in ji Times.

Ko Countinho zai koma Barca?

Coutinho
Getty Images

Da alamar Liverpool za ta bar Philippe Coutinho, dan shekara 25, ya koma Barcelona a lokacin kasuwar musanyar 'yan wasa na watan Janairu kan kudi fam miliyan 140, in ji Times.

George Weah ya gayyaci Arsene Wenger

Wenger yana ganin zai iya halartar taron rantsar da George Weah idan aka dakatar da shi kan kalamansa game da alkalan wasa
Getty Images
Wenger yana ganin zai iya halartar taron rantsar da George Weah idan aka dakatar da shi kan kalamansa game da alkalan wasa

Zababben shugaban Laberiya, George Weah, ya gayyaci kocin Arsenal, Arsene Wenger, bikin rantsar da shi wanda za a yi a cikin wannan shekarar .

Wenger ne kocin Weah a lokacin da yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Monaco tsakanin shekarar 1988 zuwa shekarar 1992, amma ba shi da tabbacin ko zai iya halartar taron.

"Gearge Weah ya gayyace ni in zo in halarci taron ranar da zai zama shugaban kasa," in ji Wenger.

"Na yi imanin ayyuka za su mini yawa, amma idan aka dakatar da ni (kan kalamaina game da alkalan wasa) zan sami lokacin zuwa."

Chelsea za ta gwada dan wasan Everton

Ross ya buga wa Everton wasanni 150 kuma ya ci kwallaye 21
Getty Images
Ross ya buga wa Everton wasanni 150 kuma ya ci kwallaye 21 agasar Firimiya tun da ya fara murza wa kungiyar kwallon kafar leda a shekarar 2011

Ana tsammanin dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley, zai yi gwaji a Chelsea ranar Juma'a kafin ya koma Stamford Bridge kan kudi fam miliyan 15.

Barkley ya ki amincewa ya koma Chelsea ranar da aka rufe kasuwar musayar 'yan wasa cikin watan Agusta.

Amman kungiyoyin biyu sun sun soma tattaunawa da aka bude kasuwar musayar 'yan wasa ranar daya ga watan Janairu.

Dan wasan Ingilan mai shekara 24 ya yi watsi da tsawaita zamansa a Everton, kuma kwantiraginsa zai kare a karshen wannan kakar.

Barka da safiya

Jama'a barkanku da shigo shafin da zai kawo muku labarai da sharhi kan yadda kasuwar musayar 'yan wasan ta Turai take ci.