Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Ya rasu ranar Talata a Landan yana da shekara 93
 2. Yana da mata hudu da 'ya'ya 63 da jikoki da dama
 3. Bayan sallar Juma'a aka binne shi a makabartar gidansa
 4. Jami'an gwamnati, 'yan siyasa da 'yan kasuwa suka halartar jana'izar
 5. Ya yi karatun Kur'ani da na addini a birnin Kano da Maiduguri
 6. Ya yi fice a fagen kasuwanci da yi wa Kur'ani hidima

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

Allah Ya jikan Malam

A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai-tsaye, kan jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u.

Wasu Hotunan Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu

Isyaka Rabiu
BBC
Isyaka Rabiu
Bashir Ahmed
Isyaka Rabiu
BBC

Kasuwancin Marigayi Isyaka Rabiu

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.

Marigayi Isyaku Rabi'u ya rasu ya bar mata da 'ya'ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin 'ya'yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.

Akwai kuma Rabi'u Rabi'u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines, da Naziru Rabi'u, da Quraish I Rabi'u, da Makiu Rabi'u, sai Abdullahi Rabi'u, da Muhammad Rabi'u, da Daha Rabi'u.

Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.

View more on twitter

Sakon ta'aziyyar rasuwar Malam a shafukan sada zumunta

Jana'izar Isyaka Rabiu
mustapha Ibrahim Facebook

Sakwannin ta'aziyar Isyaka Rabiu a shafukan sada zumunta

Daukakar Khalifa Isyaka Rabiu

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Kur'an".

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Sai dai har ya rasu ana ja-in-ja tsakanin jama'arsa da na Sheikh Dahiru Usman Bauchi kan wane ne ya fi cancantar wannan mukami.

Ya kuma yi suna wurin tallafawa marayu da marasa galihu.

Marigayin, wanda amini ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, da Alhaji Aminu Dantata, yana daga cikin fitattun dattawan da suka rage a jihar.

Isyaka Rabiu
Other

An toshe titin Goron Dutse

An tsoshe titin Goron Dutse saboda cinkoson mutane a wajen jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu

Jana'izar Isyaka Dahiru
BBC

Wasu manyan mutane ba su samu shiga wajen jana'izar ba

Yawan cunkoson da aka smau a wajen binne marigayin ya sa wasu manyan masu fada a ji na Najeriya ba su samu shiga wajen da aka binne shi ba, ciki har da shahararren mai kudin nan, Aminu Dantata, da wasu manyan mutane.

Gwamnonin jihohin Neja da Jigawa da Kano ne kawai suka samu shiga, sai kuma 'ya'yansa da wasu daga cikin jikokinsa.

Manyan 'ya'yansa hudu ne suka saka shi a kabarinsa, wato Nafi'u da Abdussamad da Rabi'u (Alhaji Karami) da kuma Naziru.

Isyaka Rabiu
BBC

Hotunan Hajiya Aisha Buhari a wajen ta'aziya

Hotunan uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari a yayin da ta je Kano don yi wa iyalan Khalifa Isyaka Rabi'u ta'aziyyar mutuwarsa a ranar Juma'a.

Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari
Jana'izar Khalifa Isyaka Rabiu a Kano
Aisha Buhari

Da kyar aka shigar da Ganduje wajen binne mamacin

Saboda cincirindon mutane da kyar aka samu shigar da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wajen binne gawar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu.

Jana'izar Isyaka Rabiu
BBC

An binne gawar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu

An binne marigayin a makabartar gidansa da ke Kano.

Sakon da Aisha Buhari ta wallafa a Instagram

"Yanzun nan na ziyarci iyalan Marigayi Khalifa Sheikh Isyaku Rabi'u a jihar Kano, babban malamin addinin musuluncin nan, don mika ta'aziyyata kan wannan rashi da ba za a mayar da kamarsa ba.

Ina yi wa daukacin al'ummar Kano da iyalan marigayin ta'aziyyar wannan rashi, da fatan Allah ya ji kansa," a cewar Hajiya Aisha Buhari.

View more on instagram

Aisha Buhari ta je ta'aziyya Kano

Uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta isa Kano don yin ta'aziyyar rasuwar marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u.

Aisha Buhari
Aisha Buhari Instagram

Sakonnin ta'aziyya daga manyan Najeriya

Ana ci gaba da aike da sakonnin ta'aziyya ga iyalan marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u daga ciki da wajen Najeriya.

Shugaba Buhari wanda ba ya kasar a yanzu, ya nuna matukar alhininsa tare da yin addu'ar Allah ya ji kan mamacin.

Shi ma tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ya kadu da jin rasuwar Khalifa saboda irin shakuwar da ke tsakaninsu tsawon shekaru.

Ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin wannan babban rashi.

IBB
IBB twitter

Cincirindon mutane a wajen Jana'izar Isyaka Rabiu

Jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu

Cincinrindo mutane ya hana a isar da gawar Khalifa Isyaka Rabiu inda za a binne ta a gidansa.

Jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu
BBC

Za a binne shi a cikin Makabartar da ke gidansa

Jana'izar Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu

A yanzu an kammala Sallar Jana'izarsa, za a binne shi a cikin makabartar da ke cikin gidansa a Kano

Janaiza
BBC

An fara sallar gawar Malam Isyaka

A yanzu dai an tayar da sahu don gabatar da sallar gawar marigayin.

jana'iza
BBC

Kalli bidiyon yadda jama'a ke halartar jana'izar

Jana'izar Khalifa Isyaku Rabi'u

Manyan baki sun hallara a masallacin

Manyan bakin da suka hallara a masallacin dai sun hada da gwamnonin Kano da Sokoto da Jidgawa.

Da Sarkin Musulmin Najeriya da shugabannin hukumomin kwastam da na shige da ficen kasar.

jana'iza
BBC
jana'iza
BBC
jana'iza
BBC

Bidiyon yadda mutane ke shiga masallacin Isyaka

Yadda ake halartar jana'izar Shaikh Isyaku Rabiu

Ana shirin sallar Juma'a a masallacin Khalifa Isyaka

Sallar Juma'a
BBC
sallar Juma'a
bb
Masallacin Sheikh Muhamma Rabiu
BBC

Ana shirin ngabatar da sallar juma'a a masallacin Sheikh Muhammad Rabiu inda za a yi wa Khalifa Isyaka Rabiku sallar jana'iza

Cincirundon mutane a masallacin Khalifa

Tuni gidan marigayin ya cika ya batse, ana jira a yi sallar Juma'a sannan a sada Khalifa Isyaka da makwancinsa.

Jana'izar Isyaka Rabi'u
Family IRS
Jana'izar Isyaka Rabi'u
IRS Family

Ganduje na cikin wadanda suka tarbi gawarsa

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na cikin wadanda suka tarbi gawar Khalifa Isyaka Rabiku a lokacin da ta isa Kano da safiyar yau.

Gawar Khalifa
Twitter/@Salimbabajo
Gawar Khalifa Isyaka Rabiu
Twitter/@Salimbabajo

Bayani kan darikar Tijjaniya

Isyaka Rabi'u ne shugaban darikar Tijjaniya na Afirka

 • An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784
 • Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta
 • Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka
 • Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya
 • Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma
 • Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:
 • Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah
 • Sai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta wa
 • Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama
 • An haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa
 • Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai
Darikar Tijjaniya
Getty Images

Manyan baki

Sarakuna da sauran manyan mutane

Sarakunan Hadeja da Gumel da Ringim da Kazaure da Dutse na jihar Jigawa duk sun halarci wajen jana'izar.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo ma yana wajen, da mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Kazalika Alhaji Aminu Dantata, wanda amini ne ga marigayin. shi ma ya je wajen.

Babban hafsan sojin sama Sadiq Abubakar tare da Gwamna Ganduje
Salim Babajo Twitter
Babban hafsan sojin sama Sadiq Abubakar tare da Gwamna Ganduje

Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya isa Kano

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya isa Kano inda ya mika sakon ta'aziyyar Shugaba Muhammadu Buhari ga iyalan marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu.

View more on twitter

Tarihin Kahlifa Isyaka Rabi'u

Yau za a yi jana'izarsa a Kano

Isyaka Rabi'u
Other
 • An haifi marigayin ne a 1925
 • Ya yi karatun AlKur'ani da na adidni a birnin Kano
 • Kafin daga bisani a tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu
 • Ya koma Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Kur'ani da na addini
 • Daga baya ne kuma ya fara harkokin kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons
 • Ya bar 'ya'ya 63 da matan aure uku
 • Ainihin uwargidansa ta rasu shekaru kadan da suka gabata
 • Ya yi fifce matuka a fagen kasuwanci da na karatun Alkur'ani
 • Daga bisa ni an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya
 • Harkokin kasuwancin da 'ya'yansa suka gada kuma suka ci gaba da samun daukaka a kai

Gidan marigayin ya fara cikar kwari

Mataimakin shugaban kasa da ministoci sun je

Tuni dai shirye-shirye suka yi nisa na jana'izar marigayin, wadda za a yi a masallacin gidan marigayin da ke unguwar Goron Dutse a birnin Kano.

An tsaurara matakan tsaro a unguwar ta Goron Dutse.

Manyan mutane daga ko ina a fadin Najeriya sun hallara a Kano don halartar jana'izar.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ma zai halarta tare da wasu ministoci bakwai, da shugabannin tsaron kasar.

Rayuwar Khalifa ya Isyaka Rabiu a takaice

Isiyaka Rabiu dai ya fara karatun Kur'ani da addini ne a Kano kafin a tura shi Maiduguri karo ilimi.

Bayan ya dawo Kano ya ci gaba da koyar da karatun Kur'ani da addini.

Daga baya ne kuma ya shiga harkar kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons.

Isyaka
Family

Bidiyon isowar gawar Khalifa Isyaka

Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda suka tarbi gawar Khalifa Isyaka Rabi'u a filin jirgin saman Malam Aminu da ke Kano, a ranar Juma'a da safe.

View more on twitter

Barkanku da shigowa wannan shafin

Jama'a barkanku da shigowa wannan shafi, inda muke kawo muku labarai da sharhi kai tsaye game da jana'izar marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u, shugaban darikar Tijjaniya na Afirka.