Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan da Umar Shehu Elleman

time_stated_uk

 1. Sai an jima

  A nan ne dai muka kawo karshen labarai da sharhin da muke kawowa a wannan shafin. Ku ci gaba da kasancewa da bbchausa.com domin samun labarai da rahotanni game jihar Ekiti da ma duniya baki daya.

 2. An fara kammala kirga kuri'u

  zaben
  Image caption: Irin wadannan hotunan ne hukumar ta INEC take wallafawa a shafinta na Twitter

  A wasu rumfunan zaben jihar Ekiti an fara kammala kirga kuri'u. Kuma mutane suna yayata sakamakon kirgne nan a shafukan sada zumunta.

  Sai dai kuma hukumar zabe ta INEC, wadda ta ke da hurumin, sanar da sakamakon zaben ba ta fara bayyana sakamakon ba kawo yanzu.

 3. An fara kirga kuri'u a wasu mazabu a Ekiti

  Kuri'a

  An fara kirga kuri'u a wasu mazabu a jihar Ekiti.

 4. INEC za ta fara kirga kuri'u a karfe biyu

  Akwatin zabe

  Wasu rumfunan zabe sun kammala kada kuri'a a halin yanzu yayin da wasu ci gaba da kada kuri'a.

  Hukumar INEC ta yi shelar cewar za a daina kada kuri'u da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriya.

 5. Fayose na zargin jami'an tsaro da kwace lamuran zabe

  Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi zargin cewar jami'an tsaro sun kwace zaben gwamnan jihar daga jami'an hukumar zabe ta INEC.

  Ya kuma yi ikirarin cewar shi ne kawai mai yakinin kan samun kashi 80 cikin 100 na kuri'un jihar.

  Fayose
 6. Fayose ya kada kuri'a

  Fayose ya kada kuri'arsa a Afao Ekiti
  Image caption: Fayose ya kada kuri'arsa a Afao Ekiti

  Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya kada kuri'arsa a garin Afao Ekiti.

 7. 'Yan sanda sun kama 'yan bangar siyasa

  Rahotanni na cewa 'yan sandan kwantar da tarzoma sun kama 'yan bangar siyasa wadanda suka saci akwatin zabe a Emure da Ado Ekiti.

  'Yan sandan sun tafi da wadanda ake zargin zuwa Ado Ekiti.

  Sai dai kuma 'yan sandan sun goge hotunan wannan lamarin da wakilin BBC ya dauka.

 8. Segun Oni ya yi magana kan masu karbar kudi

  Segun Oni

  Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam'iyyar APC, Olusegun Oni, ya ce duk wanda ya bayar da katinsa domin kudi ba zai iya kalubalantar yadda ake tafiyar da mulkin jihar ba.

  Olusegun Oni ya yi wannan maganar ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kada kuri'arsa a runfar zaben da ke mazabarsa.

  Ya kara da cewar ana ci gaba da zaben yadda ya kamata duk da tangardar da ake samu da na'urar tantance katin zabe.

 9. 'Yan daba sun ture akwatin zabe

  'Yan daba sun ture akwatin zabe a Emure Ekiti.

  'Yan sanda sun ce suna neman 'yan daban da suka ture akwatin zabe a runfar zabe ta shida a Emure Ekiti.

  Ekiti
  Ekiti
 10. An ba da kudi a gaban wakilinmu

  Ekiti

  A daya daga cikin rumfunan zaben da wakilinmu ya ziyarta, ya ga an raba kudi yayin da ake zabe lamarin da ya saba wa dokar zaben Najeriya.

  Sai dai kuma ba zai iya tantance ko jami'in wace jam'iyya ne ya bayar da kudin ba.

 11. Mun sami rahotannin wasu matsaloli — Fayemi

  Fayemi

  Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Kayode Fayemi, ya ce shi ya samu rahotanni wasu matsolli na rashin aikin na'urar tantance katin zabe daga wasu wakilan jam'iyyarsa.

  Da yake magana da manema labarai bayan ya kada kuri'arsa, Fayemi ya ce bayan zaben ne dai zai iya fitar da cikakken bayani game da matsalolin da jam'iyyarsa ta gani game da zaben.

 12. Sojoji suna yawo a babban birnin jihar Ekiti

  sojoji
  sojoji

  Wakilin BBC ya ga wucewar sama da motoci 20 dauke da sojoji a fadar jihar Ekiti, Ado Ekiti.

  Wakilin na BBC ya ga wadannan sojojin ne a hanyar da ake ce wa Oja Oba.

 13. Dan takarar PDP ya kada kuri'a

  Eleka
  Image caption: Dan takaran jam'iyyar PDP Tunde Eleka ya kada kuri'arsa

  Dan takarar jam'iyyar PDP mai mulki, Tunde Eleka, ya kada kuri'arsa kuma ya yi ikirarin cewar 'yan sanda na kallo a lokacin da 'yan jam'iyyar adawa ta APC ke bayar da kudi ga masu zabe.

  Tun jiya Juma'a ne dai rahotanni ke cewa duka jam'iyyun na bayar da kudi ga amsu zabe a zaben da ake yi ranar Asabar.

 14. Fayemi ya yi zabe

  Fayemi

  Dan takarar jam'iyyar APC a zaben, Kayode Fayemi, ya yi zabe.

 15. Ra'ayin mai zabe

  Daya daga cikin masu zaben, Abdulazeez, ya shaida wa Umar Shehu Elleman cewar koma na tafiya daidai ba tare da wata matsala ba.

  Video content

  Video caption: Kalli ra'ayin wani mai zabe a jihar ta Ekiti
 16. Tsaffi na cikin masu zabe

  Har da tsaffi

  A zaben dai da ake yi, ba a bar tsaffi a baya ba. Sun fito domin kada kuri'unsu.

 17. Na'urar tantancewa ta ba gane dan takarar PDP ba

  Oluṣọla Eleka kó tó dìbò
  Image caption: Oluṣọla Eleka kafin ya yi zabe

  Rahotannin sun ce na'urar tantancewa ba ta gane yatsar dan takarar PDP, Oluṣọla Eleka, ba.

  Sai dai kuma matarsa ta yi zabe ba tare da wata matsala ba.

 18. Barka da shigowa

  Tuni dai aka fara zabe

  Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku labarai da sharhi game da yadda jam'iyyu talatin da biyar ciki har da PDP da kuma APC ke fafatawa wajen zaben gwamnan jihar ta Ekiti.