
Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019
Labarai da rahotanni har ma da sharhi kan yadda aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Najeriya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.
Labarai da rahotanni har ma da sharhi kan yadda aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Najeriya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.
Rahoto kai-tsaye
Daga Awwal Ahmad Janyau da Mohammed Abdu
time_stated_uk
Bankwana
Masu bibiyarmu a wannan shafi duka-duka a nan muka kawo karshen bayanai na kafin zabe da ranar zabe da kuma na bayan fadar sakamako da muka yi ta kawo muku.
A madadin daukacin ma'aikatan BBC Hausa, musamman wakilanmu da suka yi ta aiko da rahotanni daga sassan Najeriya da editan BBC Hausa Jimeh Saleh da Yusuf Yakasai da Naziru Mika'il da suka yi ta sa ido kan yadda abubuwa ke gudana.
Sai kuma wadanda suka yi ta kula da wannan shafi kamar Nasidi Adamu Yahaya da Muhammad Abdu Mamman Skipper da Umar Rayyan da Halima Umar Saleh da Mustapha Kaita da Awwal Janyau da Sani Aliyu da Abdulbaki Jari da Fatima Othman da Umar Mika'il da Sadiya Umar Tahir da Abdullahi Bello da Muhammad Auwal Mu'az da kuma Abubakar Abdullahi, muke muku fatan alkahiri.
Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu, kuma ku biyo mu tun ranar jajibirin zaben gwamnoni don samun irin wadannan bayanai kai tsaye.
Allah ya ba mu alkhairi, Ameen summa ameen.
Shaidar lashe zaben 2019 da aka ba Buhari da Osinbajo
Hukumar zaben Najeriya INEC ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo shaidar lashe zaben 2019 a ranar Laraba.
Najeriya ta gudanar da sahihin zabe – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kamar yadda masu sanya ido na kasashen ketare suka bayyana,"kasar ta shirya zabe sahihi."
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi takardar shaidar lashe zaben 2019 daga hukumar INEC a Abuja ranar Laraba.
Video content
Atiku ya yi fatali da sakamakon zaben 2019
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi watsi da sakamakon zaben 2019.
A ranar Larabe ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Atikun ya ce wannan ne "zabe mafi muni da aka taba gudanarwa a tarihin Najeriya."
"Hatta zaben gwamnatocin soja suka gudanar bai kai wannan muni ba," in ji shi.
Taron ya samu halartar manyan mambobin jam'iyyar PDP, kamar su Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da Sanata Rabi'u Kwankwaso da Shugaban Jam'iyyar Uche Secondus da sauransu.
Atiku ya yi wa manema labarai jawabi
Atiku yana yi wa manema labarai jawabi a cibiyar tuna wa da Shehu Musa 'Yar Adua a Abuja ranar Laraba.
Kuma za ku iya garzaya wa shafinmu na Facebook don kallon bidiyon jawabinsa kai-tsaye.
BBC ta yi hira da dan Atiku Abubakar, Mohammed
Dan Atiku Abubakar, Mohammed ya bayyana wa BBC ra'ayinsa game da zaben 2019.
Mohammed ya bayyana hakan ne a cibiyar tuna wa da Shehu Musa 'Yar Adua a Abuja, inda Atiku Abubakar zai yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba.
Video content
Ganduje ya taya Buhari murnar nasarar zaben 2019
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Shugaba Buhari ziyarar ta ya shi munar lashe zaben 2019.
Ya kai masa ziyarar ne a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, bayan da shugaban ya karbi shaidar lashe zabensa daga hukumar INEC.
Buba Galadima ya bayyana a Abuja
Buba Galadima ya bayyana a cibiyar tuna wa da Shehu Musa 'Yar Adua a Abuja, inda Atiku Abubakar zai yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba.
A karshen makon jiya ne dan siyasar ya yi batan-dabo.
A ranar Lahadi ne iyalan Buba Galadima suka tabbatar wa da BBC cewa suna zargin jami'an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama dan siyasar da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.
Video content
Buhari da iyalansa suna murnar lashe zaben 2019
Shugaba Buhari tare da iyalansa suna murnar lashe zaben 2019 a fadarsa ranar Laraba!
Atiku zai yi jawabi kan zaben Nigeria
Jigogin jam'iyyar PDP suna hallara a babban darin taro da ake kira 'Musa Yar'Adua Centre da ke Abuja, Nigeria.
Ana sa ran Atiku zai bayyana yadda zai kalubalanci zaben da Muhammadu Buhari ya kayar da shi.
Atiku zai yi jawabi kan zaben Najeriya
Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakr zai yi jawabi kan zaben Naheriya.
Atiku wanda ya sha kaye a hannun shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai amince da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar a fadin Najeria ba.
Tsohon mataimakin shugaban Najeria ya ce zai kalubalanci zaben a kotu.
Atikun zai yi jawabin ne da misalin karfe 4:00 agogon Najeria da Miger.
Mufti Menk ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben
Shahararren malamin addinin Musuluncin nan Mufti Menk ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben 2019.
Malamin wanda dan asalin kasar Zimbabwe ne ya yi fatan Allah "ya kare shugaban, ya kuma ci gaba da yi masa jagora a dukkan al'amuransa."
latsa nan domin ci gaba da karanta labarin
Ci gaba da taya Buhari murnar lashe zabe
Wasu matasan katarko dake,kusa da Damaturu sun yi tattaki bisa kekuna zuwa Damaturu domin ,murna amma sun koka bisa takura,daga sojoji .dake garin.
Buhari zai ci gaba jan ragamar Najetr
Me ya sa aka samu karancin masu zabe?
Bayan da aka zabi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeria karo na biyu, masana harkar siyasa na tambayar dalilin da ya sa aka samu karancin masu zabe.
Wadan da suka fita zabe kaso 35.6 cikin 100 ne.
Ko da a jihar Legas an samu karancin wadan da suka karbi katin yin zabe zuwa kaso 18.3 cikin 100.
Tun kan a fara zabe, wasu matasa 'yan shekara 18 zuwa 20 a jihar Legas da garin Abeokuta sun shaidawa BBC cewar ba za su yi zaben ba.
An bai wa Buhari shaidar lashe zabe
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi shaidar lashe zaben Najeriya da aka yi a ranar Asabar a fadin kasar.
A taron da aka gudanar a ranar Laraba, an fara bai wa mataimakin shugaba, Yemi Osinbajo takardar shaida daga baya aka mika wa Buhari.
A jawabin da Buhari ya gabatar ya ce yadda masu sa ido a fadin duniya suka bibiyi zaben suka kuma sanar da ingancinsa ya nuna yadda dimukradiyyar Nageria ta kankama.
Buhari ya ce zai ci gaba da aikin farfado da tattalin Najeriya da samar da tsaro da manyan aiyukan da za su kawo wa kasar daukaka.
Wani ya sanya wa dansa sunan Buhari
Wani Bakano ya sanya wa jaririn da aka haifa masa a safiyar yau suna Buhari, domin nuna farin cikinsa ga nasarar da zababben Shugaban Najeriya Muhammadu Biuhari ya yi a zaben 2019
Yadda kuke tafka muhawara a BBC tuwita
Fatan 'yan Najeriya ga Muhammadu Buhari
Video content
Post update