Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Mohammed Abdu

time_stated_uk

 1. Lokacin da INEC ta diba ya cika

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ana jiran INEC ta sanar a hukumance wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan kammala tattara sakamakon daga jihohi da Abuja.

  Misalin karfe uku na dare ne INEC ta ce za ta dawo bayan kammala nazari kan sakamakon gaba daya domin sanar da wanda ya yi nasara.

 2. Ko Atiku zai amsa shan kaye?

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ana ganin amsa shan kaye daga dan takarar babbar jam'iyyar hamayya zai kara tabbatar da ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.

  Sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon.

  Shugaban mai shekara 76 ya kayar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.

  A zaben 2015 da ake ganin mafi zafi a tarihin siyasar Najeriya inda a karon farko aka kada shugaba mai ci, an kawo karshen zaben cikin ruwan sanyi.

  Tun kafin sanar da sakamakon zaben ne tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya kira Muhammadu Buhari mai ci na yanzu ya taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa.

  A zantawa da suka yi ta wayar tarho, Jonathan ya amsa shan kaye a zaben 2015 tare da taya Buhari murnar nasarar lashe zabe.

  Ana ganin yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da aka sanya wa hannu a lokacin ita ce ta yi tasiri har shugaban kasa mai ci nan take ya amsa shan kaye.

  A zaben 2019 yanzu hankali zai koma kan dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, kan ko zai amsa shan kaye kamar yadda Jonathan ya yi a zaben 2015.

  Ko da yake, Jam'iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben.

  Tun a sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa jam'iyyar ta yi zargin cewa akwai kura-kurai da aka tafka tare da zargin jam'iyya mai mulki ta APC da yin magudi.

  Amma zai zo da mamaki tare da rufe bakin jam'iyyar PDP idan har Atiku ya amsa shan kaye tare da taya abokin hamayyarsa shugaba Buhari murna.

  Atiku Abubakar
 3. Yadda magoya bayan APC ke murna a Fatakwal

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Video content

  Video caption: Yadda magoya bayan APC ke murna a Fatakwal
 4. Buhari ya lashe zabe da kashi 56 bisa 100

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Sakamakon zaben da aka tattara ya tabbatar da shugaba Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar asabar.

  Buhari ya lashe zaben ne da kashi 56 na kuri'un da aka kada, yayin babban abokin hamayyarsa na PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri'u 47.

  Sai dai jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi watsi da sakamakon zaben.

  Mutane sun fi fitowa a zaben 2015 fiye da adadin wadanda suka fito a zaben 2019.

  Shugaba buhari
 5. Buhari ya lashe zaben shugaban kasa

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ana jiran hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

  Sakamakon zaben Najeriya
 6. Ku kalli Ma'aikatan BBC da ke kan aiki

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Video content

  Video caption: Ku kalli Ma'aikatan BBC da ke kan aiki
 7. Yadda magoya bayan Buhari ke murna a Abuja

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Magoya bayan APC
  Magoya bayan APC
 8. Ma'aikatan BBC da ke kan aiki

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
  Ma'aikatan BBC
 9. Yadda magoya bayan Buhari suka fara murna

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Magoya bayan Buhari
  Magoya bayan Buhari
  Magoya bayan Buhari
  Magoya bayan Buhari
 10. Magoya bayan APC sun fara biki

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ku kalli yadda magoya bayan APC suka fara murna bayan kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa da alkalumman suka nuna shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi nasara da ratar kuri'u sama da miliyan hudu tsakaninsa da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP

  Video content

  Video caption: Yadda 'yan APC suka fara murna
 11. Jihohin da APC da PDP suka lashe

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Taswirar Najeriya
 12. INEC ta dage zaman bayyana sakamako

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya dage bayyana sakamakon zaben shugaban kasa har zuwa karfe 3:00 na dare.

  Ya ce za su yi nazari kan sakamakon da suka tattara da kuma korafin da wakilan jam'iyyu suka gabatar kafin sake bude zauren bayyana sakamakon zaben.

 13. An kammala tattara sakamako

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Ana jiran yanzu a sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan kammala tattara sakamakon zaben na da aka gudanar a ranar Asabar daga jihohi

  INEC
 14. Shehu Sani ya yi bayani kan faduwarsa zabe

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  BBC ta tambayi Shehu Sani, ko El Rufa'i ne ya yi sanadin faduwarsa zabe a jam'iyyarsa ta PRP.

  Video content

  Video caption: Shin el-Rufai ne ya yi sanadiyyar faduwar Sanata Shehu Sani?
 15. Atiku ya lashe Rivers

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya lashe zaben jihar Rivers jiha ta karshe daga cikin jihohi 36 da aka sanar.

  Atiku ya samu kuri'u 473,971, yayin da Buhari ya samu kuri'a 150,710.

  View more on twitter
 16. Buhari ya kasa ya tsare

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya kasa ya tsare a gaban akwatin talabijin dinsa a yayin da ake dab da kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi.

  Yana kallon lokacin da ake bayyana sakamakon jihar Zamfara.

  Shugaba Buhari
  Shugaba Buhari
 17. An fara bayyana sakamakon Rivers

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  Rivers ce jiha ta karshe da ta rage a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.

  An bayyana sakamakon jihohi 35 da Abuja.

 18. Buhari ya lashe Zamfara

  Sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya

  shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya lashe zabe a jijhar Zamfara da kuri'a 438,682, yayin da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu kuri'a 125,423.

  View more on twitter