Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

 1. Rufewa!

  Nan muka kawo karshen rahotannin. Gaisuwa gare ku abokan harkarmu.

  Mu hade gobe a manyan wasanni tsakanin Liverpool da Man City da kuma Man United da Brighton, sai Wolves da za ta karbi bakuncin Aston Villa.

  Kafin nan Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne ke maku fatan mu kwana lafiya.

  'Yan Leicester City
  Image caption: 'Yan wasan tawagar Leicester City
 2. Wasannin yau

  Premier

  Chelsea 2-0 Crystal Palace.

  Burnley 3-0 West Ham United.

  Newcastle United 2-1 AFC Bournemouth.

  Southampton 1-2 Evertonl.

  Tottenham Hotspur 1-1 Sheffield United.

  Leicester City 2-0 Arsenal.

 3. Leicester City ta casa Arsenal, ta koma ta biyu

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester City ta doke Arsenal da ci 0-2 ta kuma koma matsayi na biyu a teburin Premier Ingila.

  Wannan ne wasa na biyar a jere da kungiyar ta yi kuma take samun nasara ba tare da la'akari da a gida take ba ko a waje.

  Dan wasan gaban kungiyar Jamie Vardy ne ya fara jefa kwallo ta farko a minti na 68 - jimillar kwallo 11 da ya ci kenan a gasar ta bana - kafin daga bisani James Maddison ya kara ta biyu a minti na 75.

  Yanzu dai Leicester City ta koma matsayi na biyu a teburin Premier, wanda hakan ke nufin tana saman Manchester City da maki daya kafin ta buga wasanta da Liverpool a gobe Lahadi.

  Irin wannan nasarar kungiyar ta rika samu a kakar wasanni ta 2014/2015, wadda ta kai ga ba ta damar lashe gasar a shekarar.

  Yanzu dai Leicester za ta je bakunci ne Brighton kafin daga bisani kuma Everton ta ziyarce ta.

  Jemie Vardy da James Maddison
  Image caption: Jamie Vardy da James Maddison
 4. Bayern Munich ta yi ragaraga da Dortmund

  Bayern Munich 4-0 Dortmund

  Bayern Munich ta yi fatafata da babbar abokiyar hamayyarta Brussia Dortmund a wasan mako na 11 na gasar Bundesliga ta kasar Jamus a filin wasa na Allianz Arena.

  Wasan dai ya tashi 4-0 ne, inda sarkin cin kwallaye Robert Lewandowski ya zura guda biyu a minti na 17 da kuma 76 - kwallonsa 15 kenan a Bundesliga.

  Gnabry ne ya jefa kwallo ta biyu a ragar Dortmund a minti na 47, inda shi kuma Mats Hummles ya ci gida ana saura minti 10 a tashi daga wasa.

  Sakamakon ya sa Bayern ta koma ta uku da maki 21, yayin da Dortmund take a mataki na biyar.

  Wannan nasara ta biyo bayan kashin da Bayern ta sha a karshen makon da ya gabata a hannun Frankfurt da ci 5-1, abin da ya sa ta kori kocinta Niko Kovak -wasu rahotanni na alakanta Arsene Wenger da kulab din.

  Robert Lewandowski
  Image caption: Robert Lewandowski
 5. An tashi

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Jamie Vardy da James Maddison ne suka cinye Arsenal. Babban lokacin farin ciki ne ga Leicester la'akari da yadda Arsenal ke wahalar da ita a baya.

  Hakan na nufin Leicester City ta zama ta biyu a samna teburi da makinta 26 - daidai da Chelsea kenan.

  Maddison da Vardy
 6. Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester ta buda filin tana ci gaba da taba Arsenal. karsashi ya karu daga magoya bayan Leicester yayin da lokaci ke kara kurewa Arsenal.

 7. Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Babu shakka zai zama mummunan dare ga Arsenal tare da magoya bayanta.... kyakkywan lokaci ga Leicester City.

 8. katin gargadi

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Bellerín ya karbi katin gargadi saboda kayar da Vardy da ya yi,

 9. GOAL Bayern Munich

  Bayern Munich 3-0 Dortmund

  Da alama abubuwa sun kwace wa Dortmund. Lewandowski yana ta ci gaba da sarautarsa ta cin kwallaye - shi ne ya ci ta ukun a minti na 76.

 10. Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Minti 10 ne yayi saura kuma babu wata alamar Arsenal za ta iya rama kwallonta.... an koma yiwa Arsenal 'yar gala-gala

 11. Arsenal ta yi canji

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Lucas Torreira ya fita Joe Willock ya shigo.. hakan zai iya kawo sauyi a wasan?

 12. Leicester City 2-0 Arsenal

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Jamie Vardy ya ci kuma ya bai wa James Maddison shi ma ya ci.

  Ban sani ba ko akwai wata zumunta a duniyar nan da ta fi wannan!

 13. Arsenal ta yi canji

  Leicester City 2-0 Arsenal

  Nicolas Pepe ya yi canjin Rob Holding... dan wasan ya shigo babu wani farin ciki a fuskarsa... watakila ya iya farke wa Arsenal

 14. GOALLLLLLL Leicester City '75

  Leicester City 2 -0 Arsenal

  James Maddison ya kara kwallo ta biyu.....

  Jamie Vardy ne ya shiga da kwallon cikin yadi na 18 na Arsenal amma sai Ballerinb ya hana shi bugawa. Sai ya bai wa Maddison kwallon, wanda bai yi wata-wata ba ya dadata cikin ragar Leno, wanda bai iya yin komai ba illa kallonta tana shiga ragarsa.

  View more on twitter
 15. Leicester City ta yi canji '73

  Leicester City 1-0 Arsenal

  An sa Dennis Prae ya yi canjin Harvey Barnes....

 16. Leicester City 1-0 Arsenal

  Leicester City 1-0 Arsenal

  Da zarar an tashi a haka Leicester City ta koma ta biyu a teburi, kafin Manchester City ta buga nata wasan gobe da Liverpool.....

 17. Leicester City 0-0 Arsenal

  Leicester City 0-0 Arsenal

  Aubameyang ya dan buya in aka kwatanta da yadda yake buga kwallo

 18. Leicester City 0-0 Arsenal

  Leicester City 0-0 Arsenal

  Gray ya buga kwallo daga wajen yadi na 18