Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Imam Saleh

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

  Za ku iya ziyartar mu a shafinmu na Facebook ko Twitter ko Kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan wasu labaran da muka wallafa a wannan shafin.

 2. Aljeriya ta hana jirage daga Morocco wucewa ta sararin samaniyarta

  ...

  Ƙasar Aljeriya ta rufe iyakar sararin samaniyarta da makwafciyarta Morocco, wanda hakan wani mataki ne da ke nuna taɓarɓarewar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

  Gwamnatin Aljeriya ta bayyana cewa wannan matakin ya shafi jiragen sojoji da na farar hula kuma matakin ya fara aiki nan take.

  Aljeriya dai na zargin Morocco da ci gaba da tsokanarta da muzguna mata. Tun a watan da ya gabata ne Aljeriya ta yanke hulɗar diflomasiyya da makwafciyar tata.

  An shafe shekaru ana ƴar tsama tsakanin ƙasashen biyu sakamakon goyon bayan da Aljeriya ke bai wa ƙungiyar ƴan tawaye ta Polisario Front, da ke neman ƴancin Yammacin Sahara daga Morocco.

 3. Birtaniya ta sanar da cewa ƙarin mutum 34,000 sun kamu da korona

  Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa an samu ƙarin mutum 34,460 da suka kamu da korona a ƙasar.

  Gwamnatin ƙasar ta kuma sanar da cewa an samu mutum 166 da cutar ta kashe.

  Adadin waɗanda suka mutum ɗin ya ragu daga 203 kenan a jiya

  Haka kuma adadin waɗanda suka kamu ya ƙaru idan aka kwatanta da wanda aka samu a jiya wato 31,564.

 4. Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta kama ɗan ƙasar Jordan

  ..
  Image caption: Shugaba Felix Tshisekedi

  Gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta ce ta kama wani ɗan kasar Jordan saboda tana tuhumarsa da alaka da wata kungiyar da ke ikirarin jihadi a gabashin kasar.

  Wannan matakin ya zo ne yayin da ake fargabar kungiyar I-S na kokarin kulla kawance da kungiyar 'yan tawaye ta Allied Democratic Forces - wadda kungiya ce da ta samo asali daga kasar Uganda.

  Ana dora alhakin wasu hare-hare da ake kai wa kan fararen hula kan kungiyar ta ADF.

  Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya ga wasu takardun da ke tabbatar da cewa mutumin ne ke kula da jirage marasa matuka na kungiyar ta ADF.

 5. Ƙididdiga ta nuna mata sun fi maza yawa a Ghana da mutum 400,000

  ..

  Hukumar ƙidaya da ƙididdiga ta ƙasar Ghana ta bayyana cewa alƙaluma sun nuna cewa adadin mutanen da ke ƙasar ya kai mutum miliyan 30.8

  Hukumar ta saki waɗannan alƙaluman ne a yau bayan ƙidayar jama'ar ƙasar da gidaje da aka gudanar a watan Yunin bana.

  Bisa yadda ƙididdigar ta nuna, adadin jama'ar Ghana ya ƙaru da mutum miliyan 6.1 idan aka kwatanta da ƙidayar da aka yi a shekarar 2010 da ta nuna cewa adadin mutanen ƙasar mutum miliyan 24.7 ne.

  Wannan na nuni da cewa an samu ƙaruwa da kashi 2.1 cikin 100, kuma shi ne adadi mafi ƙaranci da aka samu na ƙaruwar jama'a a ƙasar tun bayan da Ghana ta samu ƴancin kai.

  Ƙididdigar ta nuna adadin mata a kasar ya kai miliyan 15.6 sai kuma adadin maza ya kai miliyan 15.2.

  Hakan na nufin mata sun fi maza yawa a Ghana da mutum 400,000.

 6. Amurka ta sake alkawarin bayar da tallafin riga-kafin korona miliyan 500

  ..

  Shugaba Joe Biden ya sanar cewa Amurka za ta taimaka wa kasashe masu bukata alluran riga-kafin korona miliyan dari biyar.

  Shugaba Biden din ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wani taron da aka yi ta intanet da shugabannin duniya.

  Mista Biden ya ce kawo yanzu Amurka ta yi alkawarin bayar da alluran riga-kafin fiye da biliyan daya kenan kyauta

  Mista Biden din ya bayyana cewa an fara raba riga-kafin samfurin Pfizer guda miliyan dari biyar wadanda ya sanar za su bayar yayin taron G7 a watan Yuni ta hannun shirin nan na Covax.

  Ya kuma bayyana cewa za su bayar da karin wasu allurai miliyan dari biyar na riga-kafin samfurin Pfizer ga kasashe marasa galihu a sassan duniya daban-daban.

  Shugaban ya kuma yi alkawarin ci gaba da aiki tare da Tarayyar Turai domin taimaka wa kasashe mabukata da alluran riga-kafin.

 7. Janar Haftar zai ajiye aikinsa na Soji gabannin zaɓe a Libya

  Janar

  Jagoran 'yan tawayen Libya Khalifa Haftar ya ɗau hanyar da za ta iya bashi damar shiga takara a zaɓen shugaban kasa, da ke tafe a watan Disamba.

  Janar Haftar ya ce zai ajiye aikinsa na soji, alamar yana son ya yi amfani da damar da ke akwai na sabuwar doka wajen neman takara.

  Ya shaida cewa dole jami'ai su ajiye aikinsu domin samun takarar siyasa, sai dai ya jadada cewa za a iya koma wa gidan jiya idan suka yi rashin nasara.

  Dokar da abokan huldar Janar Haftar suka bijiro da ita - ta fuskanci adawa daga abokan hamayya.

  Masu sharhi na cewa rikicin da ke tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji ya dakata saboda zabukan Libya da ke tafe.

 8. APC ta ɗage ranar gudanar da taronta na jihohi

  APC

  Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da ɗage ranar gudanar da taronta na jihohi zuwa Asabar, 16 ga watan Oktobar 2021.

  A cewar jam'iyyar, nan ba da jimawa ba za ta fitar da jadawalin taron da tsare-tsare yada abubuwa za su kasance.

  Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata John Akpanudoedehe ya fitar.

 9. Boko Haram: Shin karshen kungiyar ya zo ne?

  BH

  Ana ci gaba da samun karuwar mayakan Boko Haram da ke tuba da mika wuya kuma ake karbarsu cikin al'umma a jihar Borno.

  Fadar Shehun Borno ta gudanar da wani taro a ranar Talata kan fadakar da al'ummar Borno da wayar musu da kai - su rungumi tsofaffin 'yan Boko Haram da suka ajiye makamai suka mika wuya ga gwamnati.

  An gudanar da taron ne a fadar Shehun Borno da hadin gwiwar hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP da UNICEF don wayar da kan jama'ar jihar su karbi tubabbun mayakan da suka baro daji.

  Taron na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce sama da ƴan Boko Haram 8,000 suka miƙa wuya zuwa yanzu.

  Babban Kwamandan runduna ta bakwai Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, ya ce sun mika wuya ne daga maɓuyarsu a dajin Sambisa, da kuma sauran inda suke ɓuya.

  A cewar Kwamandan, miƙa wuya da tubabbun ƴan Boko Haram ke yi abin farin ciki ne, yana mai cewa yawan luguden wuta da ake masu ne dalilin tubarsu.

  Shiga nan domin karanta cikaken maƙalar

 10. IPOB ta yi barazanar tilastawa mutane zaman gidan wata daya a kudu maso gabashin Najeriya

  Kanu

  Kungiyar IPOB ta kabilar ibo da ke neman ballewa daga Najeriya ta yi barazanar tilastawa mutane zaman gida na wata guda a yankin kudu maso gabashin Najeriya, idan ba a gurfanar da shugabanta, Nnamdi kanu a kotu ba a ranar 21 ga watan Oktoba.

  Jami'in yada labarai na kungiyar, Emma Powerful, ya shaida haka ne a wannan Larabar ga manema labarai a birnin Akwa na jihar Anambra.

  Ya ce majiyoyinsu na tabbatar musu da cewa ma'aikatar tsaron cikin gida ba za ta kawo Kanu kotu ba kamar yada aka tsara a ranar 21 ga watan Oktoba domin ci gaba da masa shari'a.

  Ko a farkon watan Agusta sai da aka shiga zaman zullumi da rashin tabbas a yankin sakamakon irin wannan umarnin da kungiyar 'yan a-ware ta IPOB ta bai wa mazauna yankin da kada su fito wuraren ayyuka da harkokinsu na kasuwanci.

  Hukumomin Najeriya na zargin kungiyar da kai hare-hare kan jami'an tsaro da cibiyoyinsu inda suke kashe jami'an tsaron da kona ofisoshinsu da kuma kwashe makamai. Hakan nan suna zargin kungiyar ta IPOB da kisan farar hula.

  To amma kungiyar IPOB na cewa matakan da hukumomi ke dauka kan shugabanta da kuma yankin baki daya rashin adalci ne.

  Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ma, a wani rahoto a baya-bayan nan, ta zargi jami'an tsaron Najeriya da yin amfani da karfi fiye da kima kan 'yan awaren da ma wadanda ba su ji ba su gani ba a yankin.

  A cikin watan Yuni ne aka sake kamo Nnamdi Kanu bayan da ya gudu zuwa kasar waje bayan da aka bayar da belinsa a 2017.

 11. An yanke wa jagoran 'yan tawayen Congo daurin rai da rai

  An yanke wa wani jagoran ‘yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo hukuncin daurin rai da rai saboda laifukan yaki da cin zarafin bil adama.

  Chance Mihonya, sojan da ya gudu, ya kafa ƙungiyar 'yan tawaye a shekarar 2017 a gandun daji na Kahuzi Park. An kama shi a bara.

  Kotun soji ta tafi -da -gidanka da aka kafa kusa da birnin Bukavu ta same shi da laifin yin garkuwa da azabtar da mutane daga kauyuka da dama a dajin.

  An kuma yanke masa hukunci da laifin daukar yara kanana sojoji da yin amfani da albarkatun kasar.

  Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce akwai kungiyoyi masu dauke da makamai da dama a gabashin DR Congo, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan aka tilastawa barin gidajensu a bana sakamakon rikici.

 12. Birtaniya ta ɗauki likitoci 353 ƴan Najeriya aiki cikin kwana 100

  Likitocin Najeriya akalla 353 ne suka yi rajistar fara aiki a Birtaniya cikin kwanaki 100 da suka gabata.

  Bayanai da shafin yanar gizo na hukumar General Medical Council ta Birtaniya da ke yin rajista da bayar da lasisi galikitoci a Birtaniyar sun nuna cewa an yi wa likitoci ƴan Najeriya 353 rajistar dtsakanin 24 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yunin shekarar 2021, da kuma 24 ga watan Satumbar 2021.

  Rashin inganta ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya ne abinda masu sharhi da dama ke dangantawa da yawan ficewar likitocin zuwa kasashen waje.

  Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa tana iya bakin kokarinta wajen inganta bangaren kiown lafiyar.

  Ku saurari rahoton Bilkisu Babangida:

  Video content

  Video caption: Birtaniya ta ɗauki likitoci 353 ƴan Najeriya aiki cikin kwana 100
 13. Shugaban Ukraine ya lashi takobin zakulo maharan da suka yi yunkurin kashe hadiminsa

  Zelensky

  Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi alkawarin mayar da martani bayan da aka yi yunkurin halaka daya daga cikin manyan na kusa da shi a wani hari da ya yi kama da na kisan killa.

  Yayin da yake magana a zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Shugaba Zelensky ya ce bai san wadanda su ka kai harin ba, sai dai yana ganin yan yiwuwa daga wajen kasar su ke.

  Ya ce ''Ya ku 'yan Ukraine, Cikin sa'o'i biyu da suka gabata, an yi yunkurin halaka daya daga cikin masu yi min hidima, kuma aboki na na kut-da-kut Serhiy Shefir, sai dai ba zan iya cewa ga wadanda su ka kai harin ba, amma na yi tabbatar mu ku zan dauki matakin da ya dace''

  Wasu mahara ne dai su ka yi wa motar Serhiy Shefir ruwan harsasai yayin da yake barin gidansa, wanda ya sa direbansa ya sami raunuka.

  Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce babu kanshin gaskiya a cikin rade-radin da ake yi cewa Rasha na da hannu a harin da aka kai.

 14. Babu abin da 'yan bindiga suka cancanta face mutuwa - Sarkin Katsina

  Sarkin Katsina

  Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Usman, ya ce babu abin da 'yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma suka cancanta face mutuwa.

  Sarkin na magana ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a ranar Talata a Katsina.

  Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, da wasu da dama.

  Sarkin ya ce tunda 'yan fashin sun yanke shawarar daukar rayukan mutane, su ma "ba su cancanci rayuwa ba".

  Hakazalika ya koka kan jinkirin gurfanar da masu laifi da hukunta su, yana mai cewa "wannan bai dace ba.

  A cewar sarkin, dole ne gwamnatoci a dukkan matakai su tashi tsaye su hukunta 'yan fashin yadda ya dace.

  'Yan ta'adda sun jefa jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya cikin kangi, yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, kashe mutane da kona al'ummomin karkara ya ta'azzar'' inji sarkin.

 15. Kotu ta daure 'yan majalisar jam'iyyar Islama a Tunusia

  'Yan majalisa

  Wata kotun soji a Tunisia ta daure wasu 'yan majalisar dokoki biyu daga jam'iyyar Islama ta Karama.

  An zargi Nidal Saudi da cin mutuncin ma'aikatan tsaro a filin jirgin sama, kuma an hukunta Saif Eddine Makhlouf saboda yi wa alkali barazana da kuma yin wasu kalamai a kotu.

  Mista Makhlouf yana yawan sukar shugaban Tunisia, Kais Saied.

  Kwanan nan shugaban ya dakatar da majalisar kuma ya kwace kusan dukkan iko a hannunsa, lamarin da ya haifar da karuwar damuwa game da tabarbarewar hakkin dan adam a kasar.

 16. Masanan da suka kutsa kogon da 'ake daure aljanun duniya' sun ce ba su ga komai a ciki ba

  Bahout

  Wata tawagar masana da ta shiga Kogon nan da ake kira 'Jahannama' da ke Oman sun aiko da sakamakon farko tun bayan shiga kogon.

  Kogon na a ƙarƙashin hamada ne a gabashin Yemen.

  Ramin - wanda aka yi imanin yana da zurfin fiye da mita ɗari, ya kasance wani dadadden wuri da jama'a suka shafe tsawon lokaci suna guje masa.

  Tsawon ƙarnuka ana ta samun labarain cewa nan ne ake 'daure manyan rauhanan duniya''.

  Masanan sun aiko da samfuran ƙasa, da wani nau'in ruwa wanda za a fara bincike a kansa.

  Kazalika sun ci karo da macizai, da kwaɗi, da tumujin ƙwari da matattun dabbobi.

  Wani abu da basu yi tozali da shi ba dai shine rauhanan da ake cewa an daure a ciki.

 17. Yadda rikici ya tarwatsa mutanen wani gari a Myanmar

  Thantlang

  Kusan dukkan mutane dubu takwas mazauna wani gari a Myanmar sun tsere sakamakon fada tsakanin sojoji da mayakan da ke adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a farkon wannan shekarar.

  Wasu mutane daga Thantlang, a jihar Chin, an ba da rahoton cewa sun tsere ta kan iyakar da ke kusa da Indiya.

  Hotunan garin sun nuna gine -ginen da aka kone da tituna babu kowa tare da dabbobin gida suna yawo.

  Tom Andrews, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kare hakkin dan adam a Myanmar, ya ce harin bama -bamai da aka kai kan gidaje a Thantlang ya nuna irin kuncin da sojin kasar suka jefa mutane.

 18. An bindige mayakan Taliban a shingen binciken ababen hawa

  Taliban

  Rahotanni daga gabashin Afganistan na cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe mayakan Taliban biyu da wani farar hula.

  Shaidun sun ce mutanen da ke dauke da makamai sun kai hari kan shingen binciken jami'an tsaro a Jalalabad a Lardin Nangarhar.

  Kungiyar Taliban ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce duk wadanda suka mutu fararen hula ne.

  A ranar Asabar, akalla mutane biyu sun mutu a wani harin bam da aka dasa a gefen hanya a Jalalabad sannan biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a Kabul babban birnin kasar.

  Lardin Nangarhar tushe ne ga kungiyar masu da'awar kafa daular Islama wato IS wacce ta yi tir da sabuwar gwamnatin ta Taliban.

 19. Gwamnatin Sudan ta jinjina wa sojojin da suka dakile yunkurin juyin mulki a kasar

  Firaiministan Sudan

  Ministan harkokin wajen Sudan ya yaba wa sojojin kasar kan yadda suka dakile yunkurin juyin mulki ranar Talata.

  Yayin da take zantawa da BBC, Mariam El Sadig Al Mahdi ta ce hakan ya nuna jajircewar sojojin son ganin dimokradiyya ta tabbata.

  El Sadig Al Mahdi ta ce wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin magoya bayan tsohon shugaban kasar Omar Albashir ne.

  Ta ce an gano yunkurin juyin mulkin ne lokacin da suka yi yunkurin kwace gidan rediyon Omdurman.

  Ta kara da cewa zuwa yanzu babu wata alamar kutse daga waje.

 20. Girgizar kasa ta afka wa Australia

  Girgizar kasa

  Girgizar kasa ta afka wa jihar Victoria na Australiainda ta daidaita gine-gine a Melbourne tare da haddasa wata girgiza a daruruwan kilomita.

  Masana sun ce girgizar mai karfin maki 5 da digo 9, ita ce mafi karfi da kudu maso gabashin Australia ya fuskanta tun shekarun 1980.

  Can a yankin karkarar Mansfield ma an samu rushewar gine-gine, sai dai kawo yanzu babu rahoton rasa rai ko wadanda suka ji rauni.