Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Muhammad Annur Muhammad

time_stated_uk

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe wanna shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook, Twitter, ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. 'A Facebook na koyi tsafin da na kashe budurwata'

    .

    Matashin nan da ake zargin ya kashe budurwarsa domin tsafin kudi a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, ya ce ta Facebook ya koyi hakan.

    Soliu Majekodunmi, ya ce ya nemi bayanin yadda ake yin tsafin kudi ne a shafin, inda kuma ya samu bayanin da ya umarce shi yadda ya kai ga datse kan budurwar tasa Sofiyah, ya kuma kona kokon-kanta a tukunyar gargajiya.

    A ranar Litinin din nan ne Majekodunmi da wasu mutum uku suka bayyana haka, lokacin da aka gabatar da su a hedikwatar ‘yan-sanda ta jihar Ogun, a Abeokuta.

    Majekodunmi, mai shekara 18, wanda ya tsere da farko bayan kisan, aka kuma kama shi daga baya, ya ce ta intanet ya koyi tsafin daga nan ya hada baki da wasu suka aikata kisan.

    Bayan amsa laifin kisan kamar yadda rahotanni suka ambato, matashin da abokansa sun ce suna son samun kudi ne domin sayen motoci na alfarma da kuma rayuwa a gidaje na gani-na-fada

  3. Kamfanin Twitter ya kai karar gwamnatin Jamus kan sabuwar doka

    Twitter

    Kamfanin tuwita ya shigar da kara a kan wata doka da za ta fara aiki gobe Talata a Jamus, kan duk wani abu da aka sa a shafin intanet na mugun laifi.

    Dokar wadda hukumomin kasar suka yi za ta sa shafukan sada zumunta da muhawara gaggauta dakatar ko goge rubutu ko wani hoto da ya danganci aikata mugun laifi sannan kamfanonin intanet din su bayar da rahoton laifin ga ‘yan sanda.

    Kamfanin tuwita ya ce ya damu da wannan doka ganin cewa za ta tilasta musu keta haddin ‘yan kasa, ta hanyar mika bayanai a kan mutum ga jami’an tsaro tun ma kafin ta bayyana cewa mutumin ya aikata laifi.

    Hukumomin Jamus sun bullo da sabuwar dokar ne domin taimaka wa jami'an tsaro na kasar dakile ayyukan masu tsananin ra’ayin rikau da yada bayanan batanci da kiyayya a shafukan intanet.

  4. 'Yan bindiga sun sace sama da mutum 50 a jihar Katsina ta Najeriya

    Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari

    Barayin daji sun sace sama da mutum 50 daga kauyen Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a arewa maso gabashin Najeriya.

    Jaridar DailyTrust ta kasar ta ruwaito cewa , wani dan yankin wanda ya nemi a boye sunansa ya sheda mata cewa maharan su sama da 60 sun je ne a kan babura inda suka bude wuta, suna harbin kan mai-uwa-da-wabi.

    Ya ce ‘yan bindigar sun ci karensu ba babbaka tsawon sa’a biyu, ba tare da wasu jami’an tsaro sun kai dauki ba, duk da cewa akwai sojoji kusan 20 a kauyen, in ji jaridar.

    Mutumin ya kara bayani da cewa, tun ma kafin mutanen su je garin sun samu bayani a kan shirin zuwan, kuma sun gaya wa jami’an tsaro, amma abin takaicin maharan sun je da kusan karfe 7:30 na al’muru, inda suka shafe sa’a biyu a garin.

    ‘’Sun raunata mutum uku amma ba su kashe kowa ba, sai dai kuma sun sace sama da mutum 50 bayan kwashe wasu kayayyaki da suka hada da tufafi,’’ in ji mutumin.

    Wanei dan garin ya yi zargin cewa sojoji da suka fito daga bangaren garin Sheme na karamar hukumar sun ga maharan suna tsallaka titi da mutanen da suka sace, amma kuma ba su yi wani yunkuri na cetarsu ba.

  5. EFCC ta tsare shugaban kamfanin jirgin sama na Medview kan kudin aikin hajji

    Shugaban kamfanin Medview Airline, Alhaji Muneer Bankole
    Image caption: EFCC na tuhumarsa da karbar kudin jigilar aikin hajji, wadda bai yi ba

    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta tsare manajan darektan kamfanin sufurin jirgin sama na Medview Airline, Alhaji Muneer Bankole a kan zargin cin kudin aikin hajji.

    Hukumar ta zarge shi da karkatar da kashi 50 cikin dari na kudaden da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta biya shi da kuma wasu karin dala dubu 900 domin jigilar alhazai a 2019, aikin da bai yi ba.

    Rahotanni sun ce EFCC ta tsare shi ne Litinin din nan da rana a babban ofishin hukumar da ke unguwar Jabi a Abuja.

    Rahotannin sun kara bayani da cewa Alhaji Muneer, ya amsa gayyatar hukumar ne inda ya je hedikwatar tata da misalin karfe 11 na safe, domin amsa tambayoyi kan kin aikin jigilar bayan ya karfi wadannan kudade na soma aiki.

    Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da tsare shugaban inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

  6. EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 17 a kan Rochas Okorocha

    Sanata Rochas Okorocha
    Image caption: EFCC ta gabatar tuhumar ne bayan Rochas ya kaddamar da takarar neman shugaban kasa a 2023

    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume 17 a kan tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar mazabar Imo ta Yamma.

    A tuhumar da ta gabatar a gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja, EFCC ta ce Rochas ya hada baki da wasu, wadanda suka hada da ‘yan jam’iyyar APC, da wasu kamfanoni biyar suka saci naira biliyan 2.9 daga asusun gwamnati.

    Hukumar ta dauki wannan mataki ne sa’o’i bayan da toshon gwamnan ya kaddamar da aniyarsa ta takarar shugaban kasa a Najeriyar a 2023.

    A watan Afrilu na 2021, EFCC ta kama Okorocha, ta tsare shi har tsawonkwana biyu tana yi wa toshon gwamnan wanda ya mulki jihar Imo daga 2011 zuwa 2019 tambayoyi a kan batutuwn da suka shafi zargin cin hanci.

    Gwamnatin jihar ta yanzu tana zarginsa da aikata laifukan cin hanci da rashawa da almundahana da dama, sai dai kuma ya musanta dukkanin zarge-zargen.

  7. Ana ka-ce-na-ce tsakanin INEC da jam'iyyar PRP kan zaben Kebbi

    Video content

    Video caption: Ana ka-ce-na-ce tsakanin INEC da jam'iyyar PRP kan zaben Kebbi

    Latsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton Haruna Shehu Tangaza:

    A yayin da ake shirye-shiryen zabukan kananan hukumomi a jihar Kebbin Najeriya, ana ka-ce-na-ce tsakanin jam’iyyar adawa ta PRP da kuma hukumar zaben jihar bayan da hukumar ta ki saka jam’iyyar a cikin wadanda za su fata a zaben wanda za a yi a karshen makon nan.

    Wannan dai ya faru ne bayan jam’iyyar ta ki biyan kudaden da hukumar ta bukaci ‘yan takara su biya; bisa hujjar cewa babu tanadin biyan kudin a kundi tsarin mulki har ma ta maka ta a kotu.

  8. An gano gawar wani yaro zabiya da aka sace

    An gano gawar wani yaro zabiya dan shekara hudu kwana daya bayn an sace shi ranar Lahadi a gabashin Burundi

    An tsinci gawar Igiraneza Abdoul ne a wani daji.

    Yanzu dai an kama mutum uku, wadanda suka hada da ‘yan achaba guda uku, yayin da wani kuma da ake nema da bisa zargin alaka da lamarin ya tsere, amma ana nemansa.

    Igiraneza Abdoul na wasa ne da sauran yara abokana a gundumar

    Muramvya ta shiyyar Kinama a lokacin da wasu mutane a cikin tasi suka dauke shi.

    Mahaifiyarsa Kwizera Marie Godeberte ta gay awa BBC cewa wata motar tasi ce ta zo inda suke, sai kawai duka yaran suka shiga cikinta.

    Ta kara da cewa: "Da kusan karfe 7:30 ne na dare. Mun yi nema a ko’ina muka sanarwa a shafukan intanet amma ba labari."

    Kungiyar kare zabiya ta duniya ( Albinos Sans Frontières) ta ce kisan ya tayar mata da hankali, wanda ya a a yanzu yawan wadnda aka kashe a Burundi tun 2008 ya kai 28

  9. An dakatar da shari'ar kisan Thomas Sankara saboda juyin mulki

    Iyalan jagoran juyin-juya-halin ne suka bukaci dage shari'ar har sai an dawo da doka a kasar
    Image caption: Iyalan jagoran juyin-juya-halin ne suka bukaci dage shari'ar har sai an dawo da doka a kasar

    Wata kotu a Burkina Faso ta dakatar da shari'ar mutanen da suka kashe jagoran juyin-juya-hali na kasar, Thomas Sankara, wanda aka kashe a 1987.

    Iyalin Mista Sankara ne suka nemi a dakatar da shari'ar saboda juyin mulkin da aka yi a makon da ya wuce.Sun ce suna so a ci gaba da shari'ar da zarar an dawo da bin tsarin mulkin kasar.

    Kungiyar tarayyar Afrika ta dakatar da Burkina Faso daga cikinta ranar Litinin, kwana uku kenan bayan ita ma kungiyar Ecowas ta dakatar da kasar.

    Tawagar hadin gwiwa ta Majalisar Dinkin Duniya da Ecowas na Ouagadougou, babban birnin kasar, domin tattaunawa da sabbin shuwagabannin mulkin soji na kasar.

  10. Ambaliyar ruwa ta halaka mutum 18 a Brazil

    Jami'an lafiya a birnin Sau Paulo, mafi yawan al'umma a Brazil, sun ce ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sun hallaka mutum 18 tun daga ranar Juma'a.

    Kusan iyalai 500 ne suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwan.

    Gwamnan Sao Paulo Joao Doria ya fitar da kuɗin agaji bayan ganin irin ɓarnar da ambaliyar ta yi, inda wasu yankunan sai a jirgin helikofta ake zuwa.

    Tun bayan tsayawar damuna ake fuskantar mamakon ruwan sama, inda sama da mutum 40 suka mutu a jihohin Bahia da Minas Gerais a ɗan tsakanin nan.

  11. Mali ta bai wa jakadan Faransa wa'adi na korarsa daga ƙasar

    Mali

    Gwamnatin soja ta Mali ta bai wa jakadan Faransa wa'adin awa 72 (kwana uku) na ya fice daga ƙasar kan wasu kalamai da Faransar ta yi game da jami'an gwamnatinta.

    A ranar Juma'a ne Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yes Drian ya ce gwamnatin Mali ta rasa abin yi yayin da ake ci gaba da sa'insa tsakaninta da ƙawayenta na Turai game da harkokin tsaro da kuma zaɓe.

    "An kira jakadan Faransa kuma an sanar da shi matakin da gwamnati ta ɗauka na ya bar ƙasar cikin awa 72 sakamakon kalamai na takaici da ministan harkokin waje na Faransa ya yi a kwanan nan," a cewar gwamnatin.

    An bayyaan matakin ne cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.

  12. Mun kashe biliyan 100 wajen gyara matatun mai a Najeriya a 2021 - NNPC

    NNPC

    Kamfanin man fetur na Najeriya Nigerian National Petroleum Company (NNPC) ya ce ya kashe naira biliyan 100 kan gyaran matatun mai na ƙasar a cikin shekarar 2021.

    NNPC ya bayyana hakan ne cikin wani rahoton shekara da ya gabatar wa asusun haɗaka na gwamnatin tarayya da jihohi yayin wata ganawa, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

    Duk da cewa ba a bayyana matatun ba, NNPC ya ce ya kashe naira biliyan 8.3 a kowane wata na 2021 don gyara matatun man.

    Matatun man da ke ƙarƙashin kulawar NNPC sun haɗa da ta Fatakwal da Kaduna da Warri.

    Baki ɗayansu, suna da ƙarfin tace gangar mai 445,000 duk rana, kuma duk da cewa Najeriya na da matatu huɗu, tana kai ɗanyen mai ƙasashen waje a tace sannan ta sayo tataccen don shigowa da shi cikin ƙasar.

  13. Labarai da dumi-dumiKotu ta umarci a ci gaba da tsare Ɗan-Sarauniya a gidan yari

    Wata kotu a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta umarci jami'an tsaro da su ci gaba da tsare Mu'azu Magaji, tsohon kwamashinan ayyuka, bisa zargin ɓata sunan Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

    Mai Shari’a Aminu Gabari na kotun da ke Nomansland a Kano ya kuma umarci a aika likitoci su duba lafiyar shahararren mai sukar Gwamna Ganduje wanda aka fi sani da Ɗan-Sarauniya ko kuma Win Win.

    Kazalika, alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 3 ga watan Fabarairun 2022.

    Ya umarci lauyoyi masu shigar da ƙara da kuma masu kare wanda ake zargin da su kawo masa kundin shari’ar a ranar.

  14. Shari'ar Mu'azu Magaji: Ɗan Sarauniya ya musanta zargin ɓata sunan Ganduje

    Kano

    Tsohon Kwamashinan Ayyuka na Kano Mu'azu Magaji, wand aka fi sani da Ɗan-Sarauniya, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa a gaban kotu, ciki har da zagin Gwamnan Kano Ganduje.

    A yau Litinin ne ake ci gaba da sauraron ƙarar wadda gwamnatin Kano ta shigar tana zargin sa da ɓata sunan Ganduje da iyalansa a shafukan zumunta.

    Bayan karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa ne kuma tsohon kwamashinan ya musanta dukkaninsu. Zarge-zargen su ne: zagin gwamna, ɓata sunan gwamna, yunƙurin tunzira al'umma, yin ƙarya.

    Lauyoyin Mu'azu Magaji ƙarƙashin jagorancin Barista Ghazali Datti Ahmed sun nemi a ba su belin wanda suke karewa.

    Sai dai lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Wada Ahmad ke adawa da ƙudirin neman belin.

    Ana ci gaba da tafka muhawara a gaban alƙali yanzu haka...

    Kano
  15. Mahara sun harbe 'yan sanda biyu a Jamus

    Jamus

    Wasu mahara sun harbe 'yan sandan Jamus biyu a wurin duba ababen hawa.

    Da misalin ƙarfe 04:20 na asubahin ƙasar ne 'yan sanda suka tsayar da wata mota a gundumar Kusel da ke Rhineland-Palatinate mai iyaka da ƙasar Faransa.

    A wurin ne aka harbe ɗan sanda mai shekara 29 da kuma 'yar sanda mai shekara 24. 'Yar sandar ɗaliba ce a kwalejin 'yan sanda kafin kisan nata.

    'Yan sanda sun bazama neman maharan.

  16. Labarai da dumi-dumiBam ya kashe mutum tara a Kenya

    Mutum aƙalla tara ne suka mutu sannan wasu da yawa suka ji raunuka sakamakon harin bam a arewacin Kenya kan wata motar bas, a cewar wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar.

    Motar bas ɗin da ake kira matatu na kan hanyarta ne zuwa garin Mandera, wanda 'yan bindiga ke yawan kai wa hari.

    Hotunan da wani ɗan jarida a ƙasar ya ɗauka sun nuna ɓaraguzan motar da ta tarwatse bayan ta taka abin fashewar a kan titi.

    Ya zuwa yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin harin amma mayaƙan ƙungiyar Al-Shabab sun sha kai hari a ciki da kewayen Mandera, inda suka kashe mutane da dama a 'yan shekarun nan.

    A makon da ya gabata ofisoshin jekadancin ƙasashen waje, ciki har da na Amurka da Faransa, suka gargaɗi 'yan ƙasarsu kan hare-haren da za a iya kaiwa a ƙasar.

  17. 'Yan zanga-zanga sun hana zaman shari'ar Mu'azu Magaji a Kano

    Kano

    Masu zanga-zanga sun kawo wa zaman kotu cikas yayin da take ƙoƙarin ci gaba da sauraron ƙarar Mu'azu Magaji (Win Win) kan zargin cin zarafin Gwamna Ganduje da iyalansa.

    Wakilin BBC a Kano ya ambato jami'an kotun da ke Nomans Land, Sabon Gari a Kano na cewa ba za su fara sauraron ƙarar ba har sai 'yan zanga-zangar sun bar wurin.

    Matasa ɗauke da kwalaye da ke nuna goyon baya ga tsohon kwamashinan na ayyuka sun yi cincirundo a bakin kotun, yayin da wasu ɗalibai kuma ke kiran da a hukunta shi.

    Kano
  18. Gurfanar da Mu'azu Magaji a kotu ta jawo zanga-zanga a Kano

    Kano

    Yau Litinin ake sa ran tsohon Kwamashinan Ayyuka na Jihar Kano Mu'azu Magaji (wanda aka fi sani da Win Win) zai bayyana a gaban kotu bisa zargin cin mutuncin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

    Gabanin kawo shi harabar kotun da Nomans Land da ke Sabon Gari a Kano, wasu matasa na zanga-zangar neman a sake shi, inda suke ɗauke da kwalayen da ke nuna goyon bayansa.

    A gefe guda kuma, wasu ɗalibai na ɗaga kwalayen da ke cewa a hukunta shi.

    'Yan sandan Kano sun kama tare da gurfanar da tsohon kwamashinan ne bayan Gwamna Ganduje ya shigar da ƙorafi, yana mai zargin sa da cin mutuncinsa da iyalansa a shafukan sada zumunta.

    Kano
  19. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram a harin kwanton-ɓauna

    Najeriya

    Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi wa mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP kwanton ɓauna a yankin Mallumti na Jihar Borno ranar Lahadi.

    Wata sanarwa da ta fitar da yammacin Lahadi, rundunar ta ce Bataliya ta 109 ce da ke Magumeri ta gudanar da samamen, inda ta shiga sansanin 'yan bindigar.

    Ta ƙara da cewa dakarun nata sun kashe 'yan ƙungiyar da dama tare da ƙwato makamai da ababen hawa.

    Sauran abubuwan da ta ƙwato sun haɗa da wayoyin salula da kayayyakin haɗa abubuwan fashewa. Ta ce har ya zuwa lokacin da ta fitar da sanarwar tana ci gaba da aikin sintirin.

    Bugu da ƙari, rundunar ta kai hare-hare kan wani sansanin na Boko Haram a ranar Asabar a Douro da ke kusa da Damasak, duka a jihar ta Borno.

  20. Karatun makarantar dalla-dalla ya samo asali tun da daɗewa

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku kalli bidiyon

    Fitattun "malaman" nan da ke karatun barkwanci a kafafen sada zumunta sun bayyana dalilansu na shiga irin wannan aiki na barkwanci.

    Malam Abubakar Adamu wanda shi ne ke fassara karatun makarantar ya ce idon kana son isar da sako a mafi yawan lokuta sai ka dan haɗa da barkwanci domin ya isa inda ake so.

    Yaya Bala da ke jan ɓaki a wannan makaranta ya ce sakon da suke aikawa yana isa kuma yana tasiri.

    Mutanen biyu sun kwashe dogon lokaci suna gudanar da wannan aiki, amma a cewarsu a lokacin kullen korona ne karatun ya samu karbuwa sama da tunaninsu.