Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Sani Aliyu da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

 1. Zaɓen Najeriya: EU za ta tura masu sanya ido 100 a zaɓen 2023

  zaɓe

  Ƙungiyar tarayyar Turai ta ce za ta tura jami'anta 100 domin sanya ido a babban zaɓen Najeriya da ke tafe.

  Shugaban kwamitin sanya ido kan za buka na ƙungiyar Barry Andrews ne ya bayyana haka a lokacin ƙaddamar da kwamitin ƙungiyar kan zaɓen Najeriya na 2023 ranar Litinin a Abuja babban birnin ƙasar.

  Mista Andrews ya ce ƙungiyar EU ta kafa kwamiti kan Zaɓen Najeriya ne bayan da ta samu gayyata daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasar (INEC.

  Ya kuma ce tuni jami'an EU 11 suka fara aiki tun ranar 11 ga watan Janairu, a ɓangarori daban-daban na shirye-shiryen zaɓen.

  Ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na bakwai da ƙungiyar ke sanya ido a zaɓukan Najeriya.

  Ya ci gaba da cewa jami'an ƙungiyar sun ƙunshi ƙwararru a fannin fasahar zamani kasancewa wannan shi ne karo na farko da Najeriya za ta gudanar da zaɓuka ta hanyar amfani da na'urorin da ke aiki da fasahar zamani, musamman domin tantance masu kaɗa ƙuri'a da kuma aika sakamakon zaɓe.

 2. Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su riƙa gode wa Allah

  Buhari

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abubuwan more rayuwa da ake ginawa a faɗin ƙasar 'abin ban sha'awa' ne.

  A wata sanarwa mai mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya yi kira ga 'yan ƙasar da su riƙa yaba wa da abubuwan more rayuwa da ake gina musu, la'akari da yanayin da ƙasar ke ciki idan an kwatanta da sauran ƙasashe.

  Shugaban na jawabi ne a lokacin da yake kammala ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Kano da ke arewacin ƙasar domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar da ta tarayya da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu suka yi.

  Shugaban ya ce ‘‘muna da ƙasaitacciyar ƙasa, amma ba ma yaba mata, har sai mun ziyarci ƙasashe maƙwabta da sauran ƙasashe, inda sai mutane sun yi da gaske sannan su sami abinci sau ɗaya a rana''.

  ‘‘A lokacin da nake shawagi a cikin jirgi adadin dogayen gine-ginen da na gani da yawan ci gaban da ake da shi a doron ƙasa abin ' ban sha'awa' ne. Mun gode wa Allah, Mun gode wa Allah'', in ji Buhari.

  Shugaban ƙasar ya kuma umarci manyan 'yan ƙasar da su ƙarfafa wa matasa gwiwwa wajen rungumar ilimi, yana mai cewa dole ko ana so, ko ba a so makomar ƙasar a hannun matasan take.

  Ya ce '‘dole su rungumi ilimi, Fasaha ta saukaka abubuwa da dama, to amma babu abin da zai maye gurbin ilimi, dan Allah ku ƙarfafa wa yara gwiwwa su samu ilimi''.

  Shugaban ya kuma jinjina wa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bisa ayyukan raya jihar da ya shimfiɗa, yana mai cewa a ziyarar baya-bayan nan da ya kai jihohin Kogi da Yobe da Legas da Katsina ya nuna cewa, gwamnonin waɗannan jihohi sun yi namijin ƙoƙari, wajen yin ayyukan raya ƙasa a jihohin nasu idan aka kwatanta da kuɗaden da suke samu.

 3. Tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa a 2023 - MDD

  kudi

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi uku cikin 100 a shekarar 2023.

  A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar kan yanayin bunƙasar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023, ta ce ƙaruwar hauhawar farashi da ƙarancin wutar lantarki na yin tasiri a kan haɓakar tattalin arzikin Najeriya.

  ''To sai dai tattalin arzikin zai bunƙasa ta hanyar haɓakar kasuwanci da sauran sana'o'i, lamarin da zai sa bunƙasar ta kai kashi uku cikin 100.'', in ji rahoton.

  Rahoton ya ƙara da cewa ana sa ran samun haɓakar tattalin arziki ne a gabashi da yammacin Afirka.

  Haka kuma rahoton ya yi hasashen cewar ƙaruwar farashin kayayyaki zai taimaka wa masu safarar kayayyakin, to sai dai kuma ta yi gargaɗin cewar ruguwar ɓukatar kayayyakin a duniya ka iya haifar da kalubale.

 4. Labarai da dumi-dumiHarin masallacin Pakistan: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 59

  hoto

  Adadin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar bom a wani masallaci a birnin Peshawar na ƙasar Pakistan ya kai mutum 59.

  Rahotonni sun ce an kai harin ne kan jami'an 'yan sanda waɗanda masallacin ke tsakiyar shalkwatarsu.

  Firaministan ƙasar Shehbaz Sharif ya ce '''yan ta'adda na son sanya tsoro da fargaba a zukatan al'umma ta hanyar kai hari kan jami'an da ke kare ƙasar Pakisatan''.

  Kawo yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, to sai dai ana alƙanta shi da 'yan ƙungiyar Taliban ta Pakistan.

  A watan Nuwamba ne dai ƙungiyare ta kawo ƙarshen tsagaita buɗe wuta, daga nan ne kuma aka fara samun hare-hare a ƙasar.

  Ko a watan Disamban bara ma ta kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a arewa maso yammacin ƙasar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan bindiga 33.

 5. Ana kai wa motocin Mozambique hari a Afirka ta Kudu

  hh

  Gwamnatin ƙasar Mozambique ta bayyana damuwarta kan yawaitar hare-haren da ake kaiwa kan ababen hawa masu ɗauke da lambar ƙasar a Afirka ta Kudu.

  A hari na baya-bayan nan da wasu gungun masu aikata laifuka suka kai, sun ƙona wasu motoci shida na 'yan ƙasar Mozambique, ciki har da motar ɗaukar fasinja wadda ke ɗauke da fasinjoji 35 a kan hanyarta ta zuwa birnin Durban.

  Harin ya faru ne kilomita 90 daga garin Ponda wanda ke kan iyakar ƙasashen biyu.

  To sai da babu rahoton rasa rai ko raunata wani mutum a harin.

  Hukumomin Afirka ta Kudu sun kuɓutar da mutanen da harin ya rutsa da su tare da yi musu rakiya zuwa kan iyakar ƙasar.

  Baya ga cinna wa motocin wuta, miyagun sun kuma sace wasu kayyaki a cikin motocin.

  Ministar harkokin wajen Mozambique Veronica Macamo ta bayyana lamarin da cewa abin tsaro ne, tana mai cewa gwamnatin ƙasar ba ta san dalilin faruwar hakan ba, inda kuma ta buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu da ta fito ta yi bayani game da hakan.

 6. Likitoci sun dakatar da yajin aikin da suka shirya yi a Najeriya

  Likitoci

  Ƙungiya Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya ta soke yajin aikin da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar.

  Matakin na zuwa ne bayan ganawar da kwamitin zartarwa na ƙungiyar ya gudanar a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda ƙungiyar ta sake duba batun.

  A cikin watan Janairu ne dai ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki a fadin ƙasar saboda kasa biya mata buƙatunta da gwamnati ta yi.

  Likitocin dai na buƙatar a sake duba tare da inganta kuɗaɗen alawus ɗin horaswa da ake ba su, yayin da suke kuka da rashin biyansu wasu alawus-alawus, da rashin biyan wasu daga cikin mambobinsu da sabon tsarin albashi da ƙasar ta amince da shi.

  Rahotonni sun ce a ƙarshen ganawar majalisar zartarwar ƙungiyar, likitocin sun yaba wa gwamnatin tarayya game da sakin sabuwar sanarwar biyan kuɗaɗen alawus-alawus na horaswa ga likitocin.

  Haka kuma likitocin sun nemi gwamnatin tarayyar da ta biya wasu daga cikin mambobinta da ke bin gwamnatin bashin kuɗaden alawus-alawus.

 7. Somaliya ta tasa ƙeyar matar shugaban IS na ƙasar zuwa gidan yari

  ISIS

  Kotun soji a Somaliya ta yanke wa matar Abdiqadir Mumin - mutumin da ake zargi da shugabantar reshen ƙungiyar ISIS ta ƙasar - hukuncin ɗaurin shekara takwas a gidan yari sakamakon samunta da laifin aika wa ƙungiyar kuɗi da bayanan sirri.

  Gidan Talbijin na ƙasar ya ruwaito cewa an kama matar - wadda ke amfani da sunaye daban-daban domin ɓoye kanta - a shekarar da ta gabata a birnin Mogadishu.

  Mijinta, Abdiqadir Mumin ya taɓa riƙe babban muƙami a ƙungiyar al-Shabab kafin daga bi -sani ya ɓalle tare da wasu gwamman mayaƙa inda ya koma ƙungiyar IS a shekarar 2015.

  Rahotonni sun ce mijin nata na zaune a arewa maso gabashin yankin Putland na ƙasar.

  A makon da ya gabata ne dai dakarun Amurka suka hallaka wani babban kwamandan IS mai suna Bilal al-Sudani a arewacin Somaliya.

 8. Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da Aliero a matsayin ɗan takarar Sanata na jam'iyyar PDP

  Aliero

  Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin ɗan takarar kujerar sanata ta Kebbi ta tsakiya a ƙarkashin inuwar jam'iyyar PDP.

  A ranar Litinin ne tawagar alƙalan kotun biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari'a China Centus Nweze, suka yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da na babbar kotun tarayya suka yanke a baya, a kan zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar ta gudanar.

  Alƙalan sun yanke hukuncin cewa ƙalubalantar ayyana Saidu Haruna a matsayin ɗan takarar sanata a jam'iyyar PDP yana kan daidai.

  Haka kuma kotun ƙolin ta tabbatar da zaɓen Dakta Abubakar Yahaya Abdullahi a matsayin ɗan takarar sanatan Kebbi ta arewa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

  A yanzu Sanata Aliero - wanda tsohon gwamnan jihar Kebbi ne - zai fafata da gwamnan jihar mai ci Atiku Bagudu, wanda ke takarar kujerar sanatan a jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

 9. Everton ta nada Sean Dyche ya maye gurbin tsohon kocinta Frank Lampard

  Sean Dyche tare da Frank Lampard

  Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta firimiyar Ingila ta Sean Dyche a matsayin sabon kocinta.

  Masu kungiyar sun nada Dyche na tsawon shekara biyu da rabi, kwantiragin da za ta kawo karshe a watan Yunin 2025.

  Kungiyar wadda masoyanta ke kira da sunan "Toffees" ta sallami Frank Lampard ne a makon jiya bayan da ta sami kanta a matsayi na 19 a teburin firimiya a karkashin kulawarsa.

  Dyche mai shekara 51, kwararren koci ne wanda tun watan Afrilu ya zama ba shi da kulob din da yake horarwa tun da kungiyar Burnley ta sallame shi bayan ya shafe shekara 10 yana aiki tare da su.

  Sean Dyche zai zama koci na bakwai a karskashin mai kungiyar Farhad Moshiri - wanda ya sayi kungiyar tun 2016.

 10. Yawan masallatan da suka mutu a harin bam na masallacin Pakistan ya kai 32

  A section of the mosque was destroyed by the blast

  Masallatan da suka mutu bayan fashewar wani abu a birnin Peshawar na kasar Pakistan sun kai mutum 32, inda wasu mutum 150 kuma sun sami raunuka.

  Rahotann na cewa wani bangaren ginin masallacin ya rufta baki dayansa kuma akwai wasu mutanen da baraguzai suka danne.

  Yawancin wadanda suka mutu 'yan sanda ne, abin da yasa wasu ke ganin su aka kai wa wannan harin.

  Wasu rahotannin sun ce wani dan kunar bakin wake da ya zauna a sahun gaba na masallacin ne ya tashi abin fashewar da ke daure a jikinsa, sai dai babu wanda ya tabbatar da haka, kuma babu wanda ya dauki alhakin harin bam din.

  Shugabn 'yan sandan Peshawar Muhammad Ijaz Khan ya shaida wa manema labarai cewa tsakanin 'yan sanda 300 zuwa 400 ne ke harabar masallacin yayin da fashewar ta auku.

 11. Shugaba Buhari na ziyara a Kano

  ...

  A yau ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke gudanar da wata ziyara a jihar Kano.

  Tuni shugaban ya fara ƙaddamar da ayyuka daban-daban, waɗanda gwamnatin jihar ta aiwatar.

  Hakan na zuwa ne bayan da a baya ake raɗe-raɗin cewa za a ɗage ziyarar domin gudun tashin tarzoma.

  Wasu daga cikin ayyukan da Shugaba Buharin ke ƙaddamarwa sun haɗa da cibiyar maganin cutar kansa da ke a asibitin Giginyu, da cibiyar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10.

  Sai kuma katafariyar gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Maiduguri.

  ...
  Image caption: ...
 12. DSS ta kama gungun masu cazar jama'a kafin yi musu musayar sababbin takardun naira

  DSS Nigeria officers

  Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta sanar da kama wasu miyagu masu aikata laifukan sayar wa 'yan kasar sababbin takardun kudin da gwamnati ta fitar a sassan kasar.

  Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar tsaron ta fitar ta hannun kakakinta Dr Peter Afunanya a ranar Litinin a Abuja babban birnin kasar.

  Ya ce jami'an hukumar ne suka damke gungun masu aikata laifin yayin da suke tsakiyar hada-hada. Ya kuma ce, "Binciken mu ya nuna cewa wasu jami'an bankunan kasuwanci na taimaka wa masu aikata wannan zagon kasar da ake wa tattalin arziki."

  Hukumar ta gargadi al'umomin kasar da su taimaka wa jami'anta da bayanan dukkan wuraren da suka san ana yin wannan haramtaccen cinikin.

 13. Abin fashewa ya kashe akalla mutum 28 a masallacin Pakistan

  Pakistani soldiers

  Akalla mutum 28 sun rasu bayan fashewar wani abu a wani masallaci da ke birnin Peshawar na kasar Pakistan.

  Fashewar ta auku ne yayin da masallacin ke cike makil da masallata inda fiye da mutum 150 suka sami raunuka.

  Wani bangare na ginin masallacin ya rushe, kuma jami'ai a garin sun ce akwai mutanen da baraguzan ginin suka danne, kuma an tafi da wasu mutanen zuwa asibiti.

  Kawo yanzu ba a san abin da ya janyo fashewar ba, amma firaministan kasar Shebaz Sharif ya yi kakkausar suka kan harin.

  Fashewar ta auku ne yayin daa ake sallar Azahar a birnin da ke arewa maso yammacin kasar, kusa da kan iyakarta da Afghanistan.

 14. Damisa ta biyu ta tsere daga gidan kula da namun dawa

  Wata damisa ta tsere da safiyar Litinin daga wata gonar da ake ajiye da ita a Afrika ta Kudu, mako biyu bayan da wata damisar ta tsere.

  Al'ummar Edenvale da ke lardin Gauteng sun ga wata damisa tana yawo a yankin, kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.

  Wata hukuma mai rajin kare dabbobi daga ketar da ake musu, NSPCA ta tabbatar da ganin damisar, ta kuma bukaci hukumomi su dauki matakan kama ta baya ga gargadin jama'a su killace dabbobinsu na gida.

  Sai dai daga baya tashar yada labarai News24 ta sanar da an yi nasarar kama damisar, kuma an kai ta wani wurin da za a killace ta.

  View more on twitter

  A farkon wannan watan wata damisa ta tsere daga wata gona a yankin Walkerville na lardin Gauteng inda ta kwashe kwanaki tana kai hare-hare har ta raunata wani mutum da wani kare da kuma wani alade kafin daga baya a harbe damisar.

 15. Shugaban Sudan al-Burhan na ziyarar aiki a Chadi

  Abdel Fattah al-Burhan with Mahamat Idriss Déby
  Image caption: Abdel Fattah al-Burhan da Mahamat Idriss Déby a birnin N'Djamena

  Shugaban gwamnatin mulkin soja na Sudan Abdel Fattah al-Burhan na wata ziyarar aiki zuwa kasar Chadi mai makwabtaka domin binkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na SUNA ya ruwaito.

  Janar al-Burhan da shugaban gwamnatin rikon kwarya na gwamnatin Chadi, Mahamat Idriss Déby sun gana a N'Djamena inda suka bayyana aniyarsu ta aiwatar da wata yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a 2018.

  Sun kuma bayyana damuwarsu kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a cikin kasashen nasu, sun kuma ce za su kafa wat rundunar hadin gwuiwa da za ta yi aiki a kan iyakokinsu.

  Yankin da ke kan iyakar kasashen Sudan da Chadi ya kasance wurin da ake gudanar da wasu matakai na siyasa tsakanin dakaru masu goyon bayan mataimakin shugaban gwmantin mulkin soja na Sudan Mohamed Hamdan Dagalo, da na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da 'yan tawayen Chadi da kuma kungiyar Wagner ta Rasha mai sojojin haya.

 16. Ƴan bindiga sun kashe mutum takwas wurin bikin zagayowar ranar haihuwa

  South Africa Police

  Wasu 'yan bindiga da suka kai hari kan wani gidan da ake bikin zagoyowar ranar haihuwa sun bude wuta kan 'yan bikin, inda suka kashe mutum takwas a lardin Eastern Cape na Afirka ta Kudu da yammacin ranar Lahadi.

  'Yan sandan yankin sun ce maharan su biyu, sun kutsa cikin gidan ne da ke unguwar Gqeberha, wadda a baya ake kiranta Port Elizabeth, inda suka rika harbin mai uwa da wabi kan 'yan bikin, kamar yadda wata sanarwar da 'yan sanda suka fitar ke cewa.

  Ciki wadanda suka halakahar da mai gidan.

  Sai dai kawo yanzu babu wanda aka kama kan harin, amma 'yan sanda sun kaddamar da bincike, kamar yadda kafofin yada labarai a yankin suka ruwaito.

 17. An damke 'yan Najeriya biyu kan damfarar $500,000 a Canada

  Gbemisola Akinrinade and Adebowale Adiatu
  Image caption: Gbemisola Akinrinade (a hagu) da Adebowale Adiatu

  'Yan sanda a Canada sun kama wasu 'yan Najeriya biyu - Gbemisola Akinrinade and Adebowale Adiatu - kan tuhumar sun azurta kwunansu da kudaden damfarar wasu matafiya bayan sun sayar musu da tikitin jiragen sama wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka 500,000.

  Galibin matafiyan da suka sayi tikitin jiragen saman daga yankin Calgary suke kuma jiragen da suke son shiga sun taso dag nahiyar Afirka ne, kamar yadda 'yan sandan yankin Peel suka sanar.

  Hukumomin 'yan sandan sun ce ana tuhumar mutanen biyu da damfarar matafiya da mallakar kadarorin da ba nasu ne ba, da yaudara da kuma amfani da na'urar komfuta da niyyar cutar da jama'a.

  Sun kuma bukaci matafiya su mayar da hankali soosai kan sahihancin shafukan intanet din da suke mu'amula da su.

 18. Gwamantin Somaliya ta 'kashe mayakan al-Shabab fiye da 130'

  Soldiers in battle

  Gwamnatin kasar Somaliya ta ce sojojinta sun kashe mayaka fiye da 130 na kungiyar al-Shabab - ciki har da manyan kwamandojin kungiyar.

  Gwamnatin ta kuma ce wannan aiki ne na hadin gwuiwa tsakaninta da wasu kawayenta na kasa-da-kasa, ciki har da sojojin Amurka.

  Cikin watanni shida da suka gabata kungiyar Islamic Group, wadda ba ta da karfi sosai a cikin Somaliyar ta yi rashin wasu yankunan da ta ke karkashin ikonta a sanadin samamen da mayakan da ke biyayya ga gwmnatin kasar ke kai wa kungiyar.

  Sai dai zai yi wuya a tabbatar da sahihancin alkaluman mayakan da gwamnatin ta Somaliya ke cewa ta kashe, amma gwamnatin na ikirarin wannan babban koma baya ne ga al-Shabab.

  Ministan yada labarai na kasar ne ya sanar cewa mayaka masu ikirarin jihadi 136 aka kashe, inda a kwanaki uku da suka gabata ma Amurka ta sanar cewa sojojinta sun kashe wani kwamandan wata kungiya ta masu tayar da kayar baya a arewacin kasar.

 19. NRC ta sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja da Kaduna

  NRC train

  Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta sanar da masu mu'amulla da ita cewa tana farin cikin dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin biranen Abuja zuwa Kaduna.

  Hukumar ta dakatar da dukkan jigilar fasinjoji kan wannan hanyar ne a ranar Juma'a 27 ga watan nan na Janairu 2023 a sanadiyyar gocewan da wani jirgin kasa yayi a kusa da tashar Kubwa cikin wannan yinin.

  Cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa na NRC Niyi Alli ya sanya wa hannu, hukumar za ta koma daukan fasinjoji daga Talata 31 ga watan Janairun 2023.

  Ta kuma sanar da jadawalin jiragen da za su rika zirga-zirga kamar haka: AK1 zai tashi daga Idu da karfe 7:00 na safe KA2 zai tashi daga Rigasa da karfe 10:15 na safe AK3 zai tashi daga Idu da karfe 1:20 na rana KA4 zai tashi daga Rigasa da karfe 4:30 na yamma.

  Sai dai a ranakun Laraba, jirgi mai lamba AK1 ne kawai zai tashi daga Idu zuwa Rigasa da karfe 7:00; inda jirgi mai lamba KA4 zai tashi daga Rigasa zuwa Idu da karfe 4:30 na yammacin wannan ranar.

 20. Barkanmu da hantsi daga BBC Hausa!

  Barkanmu da wayewar garin ranar Litinin, ranar da aka ce ko bature na tsoronta!

  Sani Aliyu ne zai jagoranci wannan aiki na sanar da ku masu bibiyarmu abubuwan da ke wakana a sassan duniya.

  Sai ku kasance da ni tsawon wannan yinin daga Sashen Hausa na BBC.