Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

 1. PDP ta ce fashin aka yi mata a zaɓen Adamawa

  o

  Jam'iyyar PDP da ke mulki a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ayyana zaɓen da aka yi a matsayin wanda bai cika ba, kwace aka yi mata domin kuwa ta ci zaɓe.

  A wani yanayi na hayaniya wakilan jam'iyyu da dama sun rika bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaɓen baki daya, bayan bayyana zaɓen karamar hukumar Fufore.

  Cikin bayanin da baturen zaɓen ya yi ya ce, an soke wasu zaɓuka da aka yi a wasu kananan hukumomi masu yawa, wanda adadinsu za su iya maye tazarar da ke tsakanin 'yan takarar APC da PDP da ke kan gaba a fafatawar.

  Baturen zaɓen ya bayyana rashin cikar zaɓen lokacin da ake tsaka da hayaniya kuma ya fice daga zauren tattara bayanan.

 2. INEC ta bayyana Mutfwang na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Plateau

  .

  Hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Caleb Mutfwang, na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Plateau.

  Baturen zaben Musa Yusuf ya ce Mutfwanhg ne wanda ya samu kuri'u mafi yawa - 525,299 inda ya doke babban abokin karawarsa na Jam'iyyar APC, Nantawe Yilwatda da ya samu kuri'u 481,370.

  Dan takarar na PDP ya bai wa abokin hamayyarsa na APC tazarar kuri'u 43,929

  PDP ta lashe zabe a kananan hukumomi 10 yayin da APC ta yi nasara a kananan hukumomi bakwai.

 3. Labarai da dumi-dumiAn bayyana zaɓen Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba

  BBC

  Babban jami'in tattarawa da sanar da sakamakon zabe a jihar Adamawa ya bayyana zaben gwamna na jihar da aka yi ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba.

  Jami'in ya bayyana haka ne dazun nan a cibiyar tattara sakamakon zaben bayan da aka sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Fufore da ake ta dako.

  Bayan sanar da sakamakon kananan hukumomi 21 na jihar, Ahmad Umar Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 421,524.

  Yayin da babbar abokiyar hamayyarsa ta Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani ta samu kuri'u 390,275.

  Sai dai baturen zaben ya ki amincewa da sakamakon zaben da aka kawo daga karamar hukumar Fufore inda ya ce an samu banbanci a alkaluman da aka sanar da kuma wanda aka dora a shafin hukumar zabe.

  Zaben da aka yi a jihar na daya daga cikin wadanda hankula ya karkata a kai la'akari da cewa wannan ne karon farko da aka samu mace daga arewacin Najeriya da ta tsaya takarar gwamna a jihar Adamawa.

 4. Buhari ya koma Abuja bayan zaɓen gwamna

  Buhari Sallau

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja daga Katsina bayan kammala zaɓen gwamna.

  Buhari ya yi zaɓensa ne a Daura mahaifarsa, tare da iyalansa.

  Umar Dikko Radda dan jam'iyyar APC ne ya lashe zaɓen jihar, wadda dama APC ce ke mulkinta tun a baya.

  Buhari Sallau
 5. Labarai da dumi-dumiZulum ya samu nasarar komawa wa'adi na biyu

  Zulum

  Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sake samun nasarar komawa wa'adi na biyu na mulkin jihar, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamna da aka gudanar a ransar Asabar ɗin da ta gabata.

  INEC ce ta bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen a Maiduguri babban birnin jihar a ranar Litinin.

  Zulum ya lashe zaɓen ne da ƙuri'a 545,542 sai kuma jam'iyyar PDP ta ke da ƙuri'u 82,147.

  Jam'iyyar LP wadda ta taka rawar gani a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabirairu ta zo ta uku da kuri'a 1,517.

 6. Labarai da dumi-dumiPrince Bassey Edet Otu ya lashe zaɓen Cross River

  Ben Ayade

  Prince Bassey Edet Otu ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar Cross River tare da sauran jihohi a ranar Asabar 18 ga watan Maris

  Hukumar Zaɓe INEC ce ta bayyana ɗan takarar na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ya kayar da abokin burminsa na jam'iyyar PDP Sunday Onor.

  Dan takarar ya samu nasarar da kuri'u 258,619 kan abokin hamayyarsa da kuri'a 179,636.

 7. INEC ta bayyana Francis Nwifuru na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Ebonyi

  Leo Ekene Oketa (SA Media to Governor Elect)

  Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayyana ɗan takarar APC na jihar Ebonyi Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.

  Shugaban da ke tattara sakamakon Farfesa Charles Igwe, Nsukka shi ne ya bayyana Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan cika duka sharuɗan da ake tsammani ya cika.

  Francis Nwifuru ya lashe kananan hukumomi 10 cikin 13 da ake da su a jihar, yayinda dan takarar APGA ya lashe biyu na PDP ya lashe 1.

  Shi ne zai zama gwamna na hudu ga jihar ta Ebonyi da ba ta fi shekara 27 da ƙirƙira ba.

 8. Binani ta cinye sakamakon ƙaramar hukumar ƙarshe da ake jira a Adamawa

  bbc

  Bayan dogon jira da aka shafe awanni ana yi na kawo sakamakon ƙaramar hukumar Fufore wadda aka ce rikici ya hana a bayyana ta, yanzu dai an bayyana sakamakon, kuma Binani ce ke kan gaba.

  Yanzu abin da ake jira a gani shi ne sakamakon ƙarshe na zaɓen gwamnan, wanda hanakali ya karkata kansa.

  Karamar hukumar Fufore

  APC 26329

  PDP 21721

  SDP 226

 9. Sai gobe za a yi zaɓe a ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benue

  zabe

  Hukumar zaɓen Najeriya ta ce sai a gobe ne za ta gudanar da zaɓen gwamna da na 'yan majalisun jiha a ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.

  A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce a baya ta ɗage zaɓen da aka tsara gudanarwar ranar Asabar 18 ga wata, bayan da aka samu cuɗanyar muhimman takardun zaɓe tsakanin gundumomin majalisar dokokin jiha biyu da ke ƙaramar hukumar.

  Kan haka ne hukumar ta ce ta tuntuɓi wakilan jam'iyyu da sauran masu ruwa da tsaki domin sake sanya sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen.

  Sanarwar ta ƙara da cewa bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a yanzu hukumar ta saka gobe Talata 21 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar.

  Daga ƙarshe hukumar ta yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a yankin da su fito domin zaɓar mutanen da suke so a zaɓen da za a gudanar goben.

  View more on twitter
 10. Labarai da dumi-dumiUmar Mohammed Bago na APC ya lashe zaɓen gwamna a jihar Neja

  Umar Mohammed Bago

  Hukumar zaɓe ta Najeriya INEC ta ayyana Umar Muhammed Bago na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Neja.

  Bago ya samu ƙuri'u 469,896 inda ya doke abokin hamayyarsa na PDP, Isah Liman Kantigi wanda ya samu ƙuri'u 387,476.

 11. Atiku ya yi zargin murɗe sakamakon zaɓen Adamawa

  Hoton Atiku Abubakar

  Tsohon shugaban Najeriya wanda kuma ya yi wa jam'iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar ya roƙi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC a jihar Adamawa ta ayyana Jam'iyyarsa da ɗan takararta Ahmad Umar Fintiri a matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.

  Atiku ya shaida wa BBC cewa bisa alƙaluman da aka wallafa a shafin INEC, PDP ce kan gaba da APC wadda Aishatu Dahiru Ahmed Binani ke yi wa takara.

  A cewarsa, an gudanar da zaɓe lafiya ba tare da wata matsala ba, inda ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin yin murɗiya saboda jan ƙafar da ake yi wajen sanar da sakamakon zaɓen ƙaramar hukuma ɗaya da ake taƙaddama kan sakamakonta.

  Tuni dai hukumar INEC ta sanar da sakamakon ƙananan hukumomi 20 na jihar.

  Atiku Abubakar ya ce rashin sanar da sakamakon ƙaramar hukumar Fufore a kan lokaci na iya haifar da illa ga zaman lafiyar jihar Adamawa.

  A halin da ake ciki dai manyan jam'iyyun da ke fafatawa a zaɓen na iƙirarin samun nasara a zaɓen.

 12. PDP na kan gaba a jihar Plateau

  Hukumar zaɓe a jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya ta karɓi sakamakon zaɓen gwamnan jihar daga ƙananan hukumomin jihar 17.

  'Yan takara 18 ne suka fafata domin samun ɗarewa kujerar gwamnan jihar, to sai dai fafatawar ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar da jam'iyyar PDP mai hamayya.

  Yanzu dai ana dakon babban jami'in tattara sakamakon zaɓen ya gama haɗa alƙaluma domin sanar da wanda ya yi nasara a hukumace.

  Ga dai yadda sakamakon ƙananan hukumomin jihar 17 ya kasance.

  1. Karamar hukumar Jos ta gabas

  APC - 11852

  PDP - 9290

  2. Karamar hukumar Barikin Ladi

  APC - 18,568

  PDP - 32,119

  3. Karamar hukumar Bassa

  APC - 25,788

  PDP - 29,135

  4. Karamar hukumar Langtang ta Kudu

  APC - 12,437

  PDP - 16,104

  5.Karamar hukumar Kanke

  APC - 35,436

  PDP - 6,870

  6. Karamar hukumar Langtang Arewa

  APC - 20,756

  PDP - 27,826

  7. Karamar hukumar Mikang

  APC - 10,691

  PDP - 12,027

  8. Karamar hukumar Pankshin

  APC - 28,827

  PDP - 15,957

  9.Karamar hukumar Shendam

  APC - 30,815

  PDP - 17,733

  10. Karamar hukumar Riyom

  APC - 12,657

  PDP - 18,647

  11. Karamar hukumar Wase

  APC - 35,011

  PDP - 26,557

  12. Karamar hukumar Kanam

  APC - 48,710

  PDP - 28,706

  13.Karamar hukumar Mangu

  APC - 25,570

  PDP - 77,279

  14.Karamar hukumar Bokkos

  APC - 20,779

  PDP - 26,529

  15. Karamar hukumar Jos ta Kudu

  APC - 35,403

  PDP - 84,103

  16.Karamar hukumar Jos ta Arewa

  APC - 83,170

  PDP - 64,690

  17. Karamar hukumar Qua'an Pan

  APC - 24,900

  PDP - 31,727

 13. INEC ta dakatar da karɓar sakamakon zaɓen gwamna a jihohin Abia da Enugu

  'Yan takara

  Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta dakatar da karɓar sakamakon zaɓe gwamna a jihohin Abia da Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

  A wata sanarwa da INEC ɗin ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami'inta mai wayar da kan jama'a da ilimantar da su Festus Okoye ya ce an ɗauki matakin ne bayan wata ganawa da jami'an hukumar suka yi ranar Litinin.

  Sanarwar ta ce wasu 'yan daba sun kai wa ofishin INEC da ke ƙaramar hukumar Obingwa a jihar Abia hari ranar Lahadi tare da kama jami'an hukumar kan batun tattara sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙaramar hukumar.

  ''Haka kuma mun samu kiraye-kirayen sake duba sakamakon ƙananan hukumomin Nsukka da Nkanu ta gabas a jihar Enugu'', kamar yadda sanarwar ta nuna.

  View more on twitter

  Kan hakan ne INEC ɗin ta ce ta dakarar da tattara sakamakon daga ƙaramar hukumar Obnigwa a jihar Abia, da kuma ƙananan hukumomin Nsukka da Nkanu ta gabas a jihar Enugu da kawo yanzu ba a karɓa ba.

  Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta sake nazari a kan batun kafin a kammala tattara sakamon zaɓen.

  Daga ƙarshe sanarwar ta yi kira da masu kaɗa ƙuri'a da wakilan jam'iyyu da 'yan takara da su kwantar da hankalinsu tare da yin haƙuri kan matakin.

 14. Zaɓen gwamnan Kebbi bai Kammala ba - INEC

  'Yan takarar gwaman Kebbi

  Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.

  Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Yusuf Sa’idu na jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto ne ya bayyana haka a cibiyar karɓar sakamakon zaɓen da ke Birnin Kebbi.

  Ya ce an samu yawan ƙuri'u da aka soke a rumfunan zaɓe da dama a faɗin ƙananan hukumomi 20, daga cikin 21 na jihar.

  Fafatawar dai ta fi zafi ne tsakanin manyan jam'iyyun APC mai mulkin jihar da kuma jam'iyyar PDP mai hamayya.

  Farfesa Sa'idu ya ce adadin katin zaɓen da aka karɓa a wuraren da aka soke zaɓen ya kai 91,829.

  “Sakamakon da muka tattara yanzu ya nuna cewa jam'iyyar APC na da yawan ƙuri'u 388,258, yayin da PDP ke da ƙuri'a 342,980. Dan haka idan muka duba bambancin da ke tsakaninsu shi ne ƙuri'a 45,278,” in ji Farfesa Sa'idu.

  Dan haka a cewarsa ba abin da ya kamata a yi sai komawa sashe 51 ƙaramin sashen biyu da na uku, na dokar zaɓe ta 2022.

  Wanda ya tanadi cewa idan adadin ƙuri'un da aka soke ya zarta adadin tazarar ƙuri'un da ke tsakanin 'yan takara to dole sai an sake zaɓe a wuraren da aka soke zaɓukan.

 15. An ɗage karbar sakamakon zaɓen jihar Kaduna zuwa ƙarfe shida na yamma

  zabe

  Hukumar zaɓe a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana tafiya hutu daga karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar zuwa ƙarfe shida na yamma, bayan karɓar sakamakon ƙarin ƙananan hukumomi uku.

  Ya zuwa yanzu an karɓi sakamakon daga ƙananan hukumomi 22 daga cikin 23 da jihar ke da su, yanzu saura ƙaramar hukuma ɗaya wadda ita ce Kudan.

  Ga yadda sakamakon ƙananan hukumomin ukun ya kasance:

  Karamar hukumar Kachia

  APC: 23,849

  LP: 1,726

  NNPP: 470

  PDP: 27,491

  Karamar hukumar Lere

  APC: 45,823

  LP: 4,321

  PDP: 46,36

  Karamar hukumar B/Gwari

  APC: 20,627

  LP: 37

  NNPP: 726

  PDP: 19,954

 16. An kashe ɗan sanda ɗaya a hatsaniya tsakanin 'yan sanda da sojoji a Taraba

  ggg

  Rundunar 'yan sanda a jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar jami'inta ɗaya da kuma jikkatar wasu uku sakamakon hatsaniyar da ta kaure tsakanin sojoji da 'yan sanda a Jalingo babban birnin jihar.

  Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi Jada ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan jim kaɗan bayan ganawar da manyan jami'an tsaro a jihar suka yi a yau da safe.

  Haɗin gwiwar jami'an tsaron jihar waɗanda suka kira taron manema labarai sun nuna takaici kan afkuwar lamarin inda suka ce za su gudanar da bincike a kai.

  Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman ɗar-ɗar a jihar sakamakon jinkirin da aka samu wajen bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ƙarshe mako.

 17. An ɗage karɓar sakamakon zaɓen jihar Zamfara zuwa karfe biyu

  s

  Hukumar zaɓe a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana tafiya hutu daga karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar zuwa ƙarfe biyu na rana, bayan karɓar sakamakon ƙarin ƙananan hukumomi uku.

  A jiya ne dai hukumar zaɓen ta ɗage karɓar sakamakon zuwa yau, bayan da ta karɓi sakamakon daga ƙananan hukumomi biyar na jihar.

  Ya zuwa yanzu an karɓi sakamakon daga ƙananan hukumomi takwas cikin 14 da jihar ke da su.

  Takarar dai ta fi zafi ne tsakaninsa gwamnan jihar mai ci Muhammad Bello Matawalle na jam'iyyar APC, da Dauda Lawan Dare na PDP.

  Ga yadda sakamakon ƙananan hukumomin ukun ya kasance

  Karamar hukumar Talata-Mafara

  APC 41,280

  PDP 22,236

  NRM 50

  LP 42

  APGA 35

  Karamar hukumar Bakura

  APC: 41,063

  PDP: 19,455

  NRM: 40

  LP: 14

  APGA: 12

  Karamar hukumar Tsafe

  APC: 25,805

  PDP: 42,188

  NRM: 90

  LP: 23

  APGA: 43

 18. Ƴan daba sun cinna wa gidan Rarara wuta

  Kano

  Wasu mutane da ake zargin 'yan daba sun cinna wuta a gidan mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara.

  Haka na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ɗan takarar jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi nasara.

  Wani ganau ya ce 'yan dabar sun afka cikin gidan, inda ba su yi wata-wata ba suka rika lalata kayayyaki kafin cinna masa wuta.

  Sai dai ƴan mintoci bayan nan, 'yan sanda suka isa wurin tare da tarwasa ƴan dabar, amma wutar na karaɗe sassa gidan mawakin.

  Rarara ya kasance a sahun gaba lokacin yakin neman zaɓen jam'iyyar APC, inda ya yi wa ɗan takarar jam'iyyar Nasiru Gawuna waka.