Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahya da UmmulKhairi Ibrahim

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

  1. Karshen bayani

    A nan muka kawo karshen bayanan da muke kawo muku kan rikicin majalisar wakilan Najeriya.

  2. Jibrin ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa

    Wakilin BBC ya ce:

  3. 'Na hannun daman Dogara'

    A baya dai, Abdulmumin Jibril wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, yana daya daga cikin na hannun damar shugaban majalisar.  

  4. Ana bincike kan batun

    Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC da rundunar 'yan sanda da ta farin-kaya sun fara gudanar da bincike kan lamarin bayan Abdulmumini Jibrin ya kai musu koke.

  5. 'Zafin kaye ke damunsa'

    Sai dai Abdulrazak Namdas, mai magana da yawun majalisar wakilan, ya musanta zarge-zargen da Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mumakin shugaban kwamitin kasafin kudi ane ke damunsa.  

    'Yan majalisa sun sha alwashin ganin karshen lamarin
    Image caption: Dogara ya ce zafin rasa mukami ne ke damun Jibrin
  6. Post update

    Jibrin ya ce  yana da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Najeriya.

  7. Asalin rigimar

    Rikicin ya barke ne bayan an sauke Abdulmumini Jibrin daga shugabancin kwamitin kasafin kudin majalisar, inda shi kuma ya yi zargin cewa shugaban majalisar Yakubu Dogara da wasu manyan 'yan majalisar uku sun yi cushen kimanin N30bn a kasafin kudin 2016.

    Rikicin ya raba kan 'yan majalisar
    Image caption: Jibrin ya ce dole Dogara ya sauka
  8. Barkanmu da warhaka

    Za mu kawo muku bayanai kan rikicin da yake ci gaba da faruwa a majalisar wakilan Najeriya saboda zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2016.