Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Za a yi zaben shugaban kasa
  2. Takarar ta fi zafi tsakanin Shugaba Mahama da Nana Akuffo-Addo
  3. Da misalin karfe 0700 agogon GMT a aka fara kada kuri'a
  4. Za a rufe runfunan zabe da misalin karfe 1700 na GMT
  5. Za kuma a zabi 'yan takarar kujerun majalisun dokoki

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin sai an jiman ku.

An rufe rumfunan zaben kasar Ghana

An rufe kada kuri'a a zaben kasar Ghana, wanda aka yi na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa na shekarar 2016.

Ana yin zabe cikin kwanciyar hankali a Tamale

Thomas Naadi

BBC Africa, Accra

Ana gudanar da zabe a Tamale da ke Arewacin Ghana cikin kwanciyar hankali.

Ba a dai samu labarin barkewar rikicin siyasa ba.

Watakila saboda jami'an tsaro da ke yin sintiri a ciki da wajen birnin ne.

Zaben Ghana
BBC

Yadda ake yin zabe a birnin Kumasi

Birnin Kumasi shi ne birnin na biyu mafi girma a kasar ta Ghana bayan Accra,

'Yan takarar shugaban kasa masu amsa Nana sun yi zabe

'Yan takarar shugabancin kasar Ghana masu amsa sunan Nana sun kada kuri'arsu a zaben da ake gudanarwa. 

Daya namiji ne mai amsa sunan Nana Akufo-Addo, shugaban jam'iyar New Patriotic Party, wanda ya yi zabe a birnin Accra. 

Dayar kuwa mace ce mai suna Nana Konadu Agyeman-Rawlings mai takara a jam'iyar National Democratic Party.    

Zaben Ghana
EPA
Zaben kasar Ghana
Nana Konadu Rawlings

Ana karfafa tsaro a lokacin da ake yin zabe

Jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da yan sanda na ci gaba da sintiri a birnin Kumasi domin tabbatar da tsaro

Zaben Ghana
Getty Images
Zaben Ghana
Getty Images

Babu mutane da yawa a mazabar Malaga

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

A wasu mazabun ba mutane kamar mazabar Malaga.

To amma a wasu wuraren akwai masu zabe da yawa, kamar mazabar Malam Dudu akwai mutane da dama a kan layi. 

Kuma babban Jami'in mazabar ya shedawa BBC cewa yana fargabar da wuya za su kammala da masu zabe kafin lokacin da za a kammala kada kuri'a.

Zaben Ghana
BBC
Zaben Ghana
BBC
Zaben Ghana
BBC

Yadda ake zabe da harkar kasuwanci a mazabar Sawaba

Ibrahim Isa BBC Hausa Accra, Ghana

Tun da sanyin safiyar Laraba aka fara kada kuri'a a zaben kasar Ghana

Fursunoni a Ghana na yin zabe a kasar

Fursunoni suna daga cikin masu kada kuri'a a zaben sugaban kasar Ghana da na 'yan majalissu.

 Wannan shi ne karo na biyu da fursunonin ke yin zabe, bayan wanda suka yi a shekarar 2012. 

 A cewar wata kafar yada labarai da ke Ghana City FM a labarin da ta wallafa a shafinta na Intanet ta ce kimanin fursunoni 2,276 ne aka yi wa rijistar yin zabe a kasar ta Ghana.  

Zaben Ghana
Seth Kwame Boateng

Bin layi domin kada kuri'a

Jami'an zabe na taimakawa masu kada kuri'a hawa kan layi da bin ka'ida a wata mazaba da wakilin BBC Akweasi Sarpong ya ziyarta a birnin Accra:

View more on twitter

Yawan mutanen da za su yi zabe

Ana kada kuri'a ne a mazabu dubu ashirin da takwas da dari tara da casa'in da biyu.

Haka kuma mutum miliyan goma sha biyar da dubu dari bakwai da uku, da dari tara da casain ne za su kada kuria a zaben shugaban kasar Ghana da na 'yan majalissu.

Zaben Ghana
BBC

Zaben shugaban kasar Ghana da 'yan majalissu

Zaben Ghana
BBC
Zaben Ghana
BBC

Abubuwan da aka yi yakin neman zabe

Batun tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa su ne suka mamaye yakin neman zaben.  

Tattalin arzikin kasar dai ya samu koma baya a 'yan shekarun nan.   

Halin da tattalin arzikin Ghana ke ciki

Abubuwa biyar kan zaben Ghana da ya kamata ku sani

1. Masu suna John sune ke yawan shugabantar kasar

Tun shekarar 1992 masu suna John ne ke shugabantar kasar.

2. Tun shekarar 1992, jam'iyyu biyu ne kawai suka mamaye siyasar Ghana. Jam'iyyar National Democratic Congress ce ta shugaba mai mulki. Sai jam'iyyar New Patriotic Party ta hamayya.

3. A Duk lokacin da jam'iyyar Democrats ta lashe zaben shugaban kasar Amurka..... To sai ka ga Jam'iyyar NDC ma ta ci zabe a Ghana. Kuma idan Republican suka ci a Amurkan, haka ma jam'iyyar NPP ce ke lashe zaben Ghana.

4. A karon farko a tarihin, an samu mace ta farko Charlotte Osei, wadda ke shugabantar hukumar zaben kasar Ghana. 

5. Ba a taba samun sauyin gwamnati a Ghana, ba tare da an yi zabe zagaye na biyu ba. 

Hoton charlotte Osei
BBC
Charlotte Osei ce ke shugabantar hukumar da ke kula da zabe a Ghana

Mata masu ciki ba sa bin layin zabe

Mata masu ciki ba sa bin layi, ana basu dama su kada kuria da zarar sun je rumfar zabe.

zaben Ghana
BBC

An tantance mutane 99 a mazabar Zango B

Kawo yanzu mutane 99 sun kada kuria a mazabar Zango B, daga cikin mutane 639 kamar yadda wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai daga Kumasi a Ghana ya aiko mana da yadda ake tantance masu zabe.

Tun da sanyin safiyar Laraba aka fara kada kuri'a

An tsaurara matakan tsaro a Tamale

Wakilin BBC Thomas Naadi ya wallafa hoto a Twitter da ke nuna jami'an tsaro suna sa-ido kan yadda al'amura ke tafiya a yankin Tamale.

View more on twitter

Wasu sun kada kuri'a sun koma gida

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

Tuni wasu yan kasar ta Ghana suka kada kuri'un su kuma suka koma wajen sana'o'in su

zaben Ghana
BBC

Yadda ake tantace mutane a mazabar Zango B

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

Tun da safiyar Laraba aka fara yin zabe a Ghana

Wakilin BBC ya kada tasa kuri'ar

Daya daga cikin ma'aikatan BBC, Akwasi Sarpong, wanda dan kasar ta Ghana ne, kuma a yanzu yana can domin aiko da rahotanni kan zaben, shi ma ya kada tasa kur'ar:

View more on twitter

An takaita zirga-zirga a baburan hawa

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

Mutane suna da damar ci gaba da harkokin su a Ghana a lokacin da ake ci gaba da zaben. To sai dai an hana yawo da babura a yau har zuwa gobe da safe

Ghana Election
Getty Images

Wasu sun sanya alama a kan layin zabe

Tun kafin a fara zabe wasu mutanen suka saka alamar suna kan layi, domin da zarar an fara kada kuri'a su samu damar jefa ta su da wuri.

Ghana Election
BBC

Wasu Tun a daren Talata suka fara bin layi

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

Tun tsakar daren Talata wasu mutane suka fara hawa kan layi domin su samu kada kuri'un su da wuri 

A mafi yawan wurare dai an fara zaben a kan kari. Sai dai an samu jinkiri a wasu wurare a birnin Accra. Sai dai duk da haka an fara zaben kafin 7:30 na safe.

Ghana Election
BBC

Tun da sanyin safiya aka fara kada kuri'a

Yusuf Ibrahim Yakasai

BBC Hausa, Kumasi, Ghana

Tun da karfe 7:30 na safe agogon Ghana aka fara kada kuri'u a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Ghana. 

Za a kada kuri'n ne a mazabu dubu ashirin da takwas da dari tara da casa'in da biyu. 

Haka kuma mutum miliyan goma sha biyar da dubu dari bakwai da uku, da dari tara da casain ne za su kada kuria a zaben na yau.

Ghana Election
BBC

An fara gudanar da zagen kasar Ghana

An bude rumfunan zabe a Ghana, bayan da 'yan takarar shugaban kasar su bakwai suka yi kira da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. 

Jami'an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum daya dan adawa, bayan da rikici ya barke a lokacin da ake yin kamfen a ranar Talata. 

Manyan 'yan takarar shugaban kasa sun hada da shugaba John Mahama da tsohon Firai minista Nana Akufo-Ado. 

Ghana Election
ap
Tun da karfe 7:00 na safe agogon GMT aka fara kada kuri'a a wasu wuraren

Barkanmu da saduwa kan yadda za mu kawo muku zaben kasar Ghana kai tsaye