Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Donald Trump ya zama sabon shugaban Amurka
  2. Ya maye gurbin Barack Obama da karfe 5.00 agogon GMT
  3. Trump yi jawabin karbar mulki
  4. Obama ya shiga jirgi zuwa California

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Abdu da Mukhtar Adamu Bawa

time_stated_uk

Karshen sharhi da bayanai

Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na BBCHausa.com.

Trump da matarsa bayan rantsar da shi
AP

To, sai wata rana, Obama

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama da uwargidansa Michelle sun tashi cikin jirgin shalkwaftan soja wanda zai kai su zuwa sansanin sojan sama na Andrews.

Daga nan za su hau wani jirgi wanda zai kai California inda za su je hutu.

Yayin da yake bankwana, ya yi musabaha da Donald Trump da mai dakinsa kuma ya yaba wa jami'an tsaron da ya yi aiki da sul. 

Joe Biden da matarsa za su hau jirgin kasa, wanda zai kai su Delaware.

Kun san sau nawa Trump ya jawo ce-ce-ku-ce?

 BBC ta yi nazari ta kuma zakulo wasu daga cikin irin kalaman da Donald Trump ya yi a lokutan yakin neman zabe wadanda suka jawo a ka yi ta sharhi a kai, da kuma irin tasirin da watakila za su iya yi bayan ya dare kujerar mulkin.  Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

http://www.bbc.com/hausa/labarai-38666866Link

Trump inaguration
Getty Images

'Jawabin kama-aikin shugaba mafi fushi' - malamin jami'a

Wani masanin siyasa, Dr Mike Cornfield, a jami'ar George Washington ya fada wa BBC cewa yana tunanin jawabin shugaba Trump shi ne jawabin kama-aikin wani shugaba mafi fushi da ya taba ji

Dr Cornfield ya ce yana tunanin hanyar da sabon shugaban ke amfani da ita ta "fito-na-fito ce".  

Kalmomin da Trump ya yi ta amfani da su a lokacin jawabi

Wadan nan sune kalmomin da sabon shugaban Amurka Trump ya yi amfani da su a lokacin da ya gudanar da jawabi, bayan da aka rantsar da shi.

Kuma kalmar "America" da "Americans" sune ya fi maimatawa. 

Trump inaguration
BBC

'Ruwan sama alama ce ta albarka'

Yayin addu'ar rufe taro, Rabaran Franklin Graham ya fada wa sabon shugaban Amurka, Donald Trump cewa ruwan da ake yi, wata albarka ce daga Allah. 

Hoton Trump a lokacin da yake yin rantsuwa

Trump Inaguration
Reuters

Obama: 'ya yi kyau, ka kyauta'

"Ku ji abin da zan fada. Ba za a kara yin biris da ku ba," a cewar Trump lokacin da ya kai kololuwar kammala jawabinsa da wannan alkawari.

"Da hadin kanku za mu sake mayar da Amurka mawadaciya.

"Za mu maida Amurka kasar alfahari.

"Tabbas, da ku za mu sake mayar da Amurka kasaitacciyar kasa."

"Allah ya albarkaci Amurka", ya fada sau biyu kafin ya bar inda ya yi jawabi. 

An ji Obama yana cewa "Ya yi kyau, ka kyauta."

A yayin da yake jawabi an sauya sunan shafinsa na Twitter zuwa @POTUS

An sabunta shafin sada zumunta na Donald Trump na Twitter zuwa @POTUS. Sai dai kuma har yanzu ba a rubuta komai ba a kan sabon shafin.

Trump Inaguration
BBC

Lokacin fada ba cikawa ya wuce

Donald Trump ya ce "Sai mun yi tunani mai zurfi kuma yi buri babba. Ba zan kara amincewa da 'yan siyasa masu fada ba cikawa ba, kullum sai korafi amma ba za su iya yin komai ba." 

"Lokacin fada ba cikawa ya wuce, yanzu lokaci ya zo na aiki gadan-gadana. Kada ku yarda kowa ya ce muku wani abu ba zai yiwu ba."

Trump ya yaba wa Obama

Donald Trump
BBC
Trump yana jawabi

'Amurka kasarku ce'

Trump ya ce: "Wannan ranarku ce, bikinku ne, kuma wannan, Amurka, kasarku ce."

"Za a daina mantawa da Amurkawa maza da mata da aka manta da su. Kowa yana saurarenku a yanzu."  

An canja lambar motar da Trump zai yi aiki da ita

Yadda aka rantsar da Donald Trump haka aka sauya lambar motar da sabon shugaban Amurka zai yi amfani da ita.

Trump inaguration
@jeffmason1

Trump yana jawabi

"Bikin yau muhimmi ne al'amari ne don ba kawai mika mulki daga wannan gwamnati zuwa wata aka yi ba, musayar gwamnati aka yi daga Washington inda aka damka wa mutane".

Rantsuwar da Trump ya yi

Bayan ya daga hannunsa sama ya ce "Na rantse zan gudanar da aikin ofishin shugaban Amurka da zuciya guda zan kuma yi bakin iayawata don alkintawa da karewa da tsare kundin mulkin Amurka"

Labarai da dumi-dumiAn rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka

Babban jojin Amurka, John Roberts, shi ne ya rantsar da shi.

An rantsar da mataimakin shugaban kasa Mike Pence

Alkalin kotun Kolin Amurka, Clarence Thomas ya rantsar da Mike Pence a matsayin mataimakin shugaban Amurka

mIKE pENCE
BBC
An rantsar da Mike Pence

An bude taro da addu'a

Babban limamin kirista Timothy Dolan ya yi addu'ar neman taimakon Ubangiji ga al'ummar Amurka da kuma shugaban da za a rantsar.

Shugaban babbar cocin New York ya karanta addu'ar sarki Sulaiman kuma ya alamta gicciyen addinin kirista don neman tubarraki. 

Donald Trump ya rintse hannuwansa kuma ya sunkuyar da kai.

Magoya bayan Trump sun ce ko ana ruwa ana iska sai sun shaida rantsuwa

Akwai dumbin magoya bayan Trump da suka fita don ganin bikin rantsar da sabon shugaban Amurka, duk da zanga-zangar da ake yi a wasu wurare

Trump supporters
@cNorthcott
Magoya bayan Trump sun ce ko ana ruwa ana iska

Jirgi mai saukar ungulu na Obama

Jirgi mai saukar ungulu da yake jiran Barack Obama domin ya kai shi barikin sojojin sama na Andrews.

Trump Inaguration
@jakesherman

Trump na daf da yin jawabi

Babu wanda ya san abin da jababin Trump ya kunsa, amma wasu jami'ai sun ce jawabin na sa zai kai tsawon minti 20.

Trump I8naguration
AP

Bill Clinton da Mai dakinsa, Hillary sun hallara

Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton da mai dakinsa Hillary wadda Trump ya kayar a zabe sun zo don shaida bikin rantsar da shugaban Amurka na 45 

Hillary da Bill Clinton
BBC
Hillary da Bill Clinton sun zo shaida rantsar da Trump

Trump ya shiga wurin da za a rantsar da shi

Donald Trump ya isa wurin da za a rantsar da shi domin kama aiki a nutse.

Trump Inaguration
Pool

Melania ta hawo kan dandamali

Mai dakin Trump, Melania, ta hau kan dandamalin da aka kebe, inda wani sojan Amurka yake take mata baya.

Sai daga baya ne Ita da danta, Barron za su tare a Washington DC. Za su jira har zuwa karshen shekarar karatun yaron mai shekara 10.

Su wane ne ke zanga-zanga?

Wakilin BBC James Cook ya ci karo da wasu zazzafar zanga-zanga a daren jiya.

Akwai kungiyoyin 'yan fafutuka daban-daban da suka je birnin Washington, wasu ga alama da muguwar niyya.

Wata kungiya da ake kira, Disrupt J20, tana ta kokari ta kange shingen binciken tsaro don hana magoya bayan Trump samun damar shiga wani wurin kallo da aka kebe. 

Yadda Trump zai yi rantsuwa

Kamar yadda tsoffin shugabannin Amurka suka yi rantsuwar kama aiki, haka shi ma Trump zai yi.

Yadda tsoffin Shugabannin Amurka suka yi rantsuwar kama aiki

An gargadi Amurkawa game da zanga-zanga

Ofishin jakadancin Amurka a Canada ya gargadi Amurkawa a kan su farga da zanga-zangar da aka shirya a birnin Montreal.

Anti- Trump protest
Getty Images
An shirya gudanar da zanga-zanga a fadin kasar Canada tsakanin ranar Juma'a da Asabar

Mike Pence da Joe Biden za su shiga mota zuwa wajen ranstuwa

Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden da takwaransa Mike Pence wanda za a rantsar a yau sun fita zuwa Capitol Hill

Vice Presidents
BBC
Mataimakan shugabannin Amurka sun kama hanya

Kun san manyan na hannun-daman Trump?

 A matsayinsa na sabon shugaban Amurka, Donald Trump zai karɓi iko da fadar White House, mun yi nazari kan iyali da abokan hulɗar da za su kasance cikin jami'ansa da kuma ka iya samun muhimman muƙamai a shugabancinsa. Latsa nan http://www.bbc.com/hausa/labarai-38663169

Trump inaguration
Getty Images

Obama da Trump sun fito daga White House

Shugaba Obama da Donald Trump sun fita daga fadar White House don zuwa Capitol Hill inda za a rantsar da sabon shugaban Amurka na 45

US Presidential Inauguration
BBC
Obama da Trump suna fitowa daga White House

Trump ya bar gida zuwa wajen rantsuwa

Donald da Melania Trump sun bar gida domin zuwa wajen da za a rantsar da shi, sun kuma shiga manyan motoci bakake.

Trump inaguration
AFP

Taron da aka fara rantsar da shugaban Amurka aka dauki hoto

 James Buchanan a shekarar 1857 aka rantsar aka kuma fara daukar hoton taron a kamara. 

Trump Inaguration
Smithsonian

Ko mai Trump zai cewa Amurkawa da duniya?

Mr Trump ya rubuta a shafinsa na tweeter a makon nan cewa ya rubuta jawaban da zai yi da hannunsa a fadar White House a Florida.  

Trump inaguration
Donald Trumpf Tweeter

Za a rantsar da Donald Trump a yammacin Juma'a

Za a rantasar da sabon shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya lashe zaben kasar. 

Trump attajirin dan kasuwa zai gabatar da jawabai da karfe 17:00 na yammaci agogon GMT a Washington. 

Za ku iya bibiyar shirin kai tsaye sannan za ku iya bayar da gudunmawarku a BBC Hausa Facebook

Trump sworn in
Reuters